Sojoji Sun Yi Babbar Nasara, Sun Kashe Shugaban 'Yan Ta'addan ISWAP
- Sojojin Najeriya, DSS da jami'an Amotekun sun hallaka wani babban shugaban ISWAP, Abdussamad Ohida, a wani samame da aka kai maboyar 'yan ta'adda a Ondo
- Majiyoyin tsaro sun ce Ohida, wanda aka fi sani da Anwar, yana shirin kai hare-hare kan fararen hula a wasu jihohin Kudancin Najeriya a lokacin bukukuwan Kirsimeti
- An ce bayan kisan Ohida, jami'an tsaron sun samu gagarumar nasara wajen tarwatsa shugabanci da shirin fadada ayyukan ISWAP zuwa yankunan Arewa ta Tsakiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ondo – Wani hadin gwiwar jami'an tsaron Najeriya ya hallaka Abdussamad Ohida, wani babban shugaban kungiyar ISWAP, a wani samame da aka kai maboyar kungiyar da ke dajin Owo a karshen mako.
Sojojin Najeriya, jami'an Hukumar Leken Asiri ta DSS da jami'an Amotekun, ne suka gudanar da aikin wanda aka shirya bisa bayanan sirri.

Kara karanta wannan
Ba ɓoye ɓoye, Gwamna Sule ya faɗi jihohi 3 da APC ke fuskantar babban ƙalubale gabanin 2027

Source: Facebook
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa an hallaka shi tare da wasu mambobin kungiyar yayin da jami'an tsaron suka kai farmaki ba zato ba tsammani kan maboyarsu.
Ohida ya jagoranci ISWAP
Majiyoyin tsaro sun ce Ohida ya taba zama mataimakin shugaban ISWAP a wasu yankunan Najeriya bayan kama Abu Ikrimah, wanda aka fi sani da Abu Uwais.
DSS ta kama Abu Uwais a shekarar 2023, bayan haka Ohida ya karbi jagorancin ayyukan ISWAP a wasu sassan Arewa ta Tsakiya da Kudancin Najeriya, inda ake zargin ya taka muhimmiyar rawa wajen tsarawa da aiwatar da hare-haren kungiyar.
Majiyoyin sun ce bayan da DSS ta yi wa Abu Uwais tambayoyi, ta samu bayanan sirri kan shirin Ohida na kai hare-hare kan fararen hula a lokacin bukukuwan karshen shekara.
Vanguard ta wallafa cewa wata majiya ta ce manufar shirin ita ce kai wa fararen hula hari a lokacin bukukuwan, sannan a kawo cikas ga babban zaben 2027.

Kara karanta wannan
Ta faru ta kare: INEC ta shirya sanar da makomar takarar Sheikh Pantami a zaben 2027
An ce bayanan sirrin sun samu karin tabbaci daga abokan hulda da Najeriya ke da su a Birtaniya, wadanda suka taimaka wajen gudanar da aikin da ya kai ga hallaka Ohida.
An alakanta Ohida da hare-hare
Majiyoyin sun zargi Ohida da shiryawa tare da aiwatar da mamayar ofishin 'yan sanda na Ipele da ke Owo a ranar 31 ga Disamba 2025, inda aka kwace bindigogi kirar AK-47 guda takwas kafin a tarwatsa ofishin da wani abu mai fashewa.
Haka kuma, an alakanta shi da harin da aka kai wata cibiyar sojoji da ke hanyar Suleja zuwa Zuba a jihar Neja a ranar 28 ga Yulin 2022, wanda ya yi sanadin mutuwar wasu sojoji, jami'ai da fararen hula.
Majiyoyin sun kuma danganta shi da harin da aka kai gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja a ranar 11 ga Yulin 2022, da harin Ogaminana a Adavi ta jihar Kogi a ranar 23 ga Afrilu 2022.

Source: Facebook
An kuma ce Ohida ne ya shirya harin ranar 24 ga Disamba 2020 kan wani shingen tsaron sojojin ruwa a Okene, jihar Kogi, wanda ya yi sanadin mutuwar jami'an ruwa biyu.
An kashe Abu-Bilal al-Minuki
A wani labarin, kun ji cewa a watan Mayun 2026, Najeriya da Amurka sun gudanar da wani samame na hadin gwiwa da ya kai ga hallaka Abu-Bilal al-Minuki.
Rahotanni sun nuna cewa Abu-Bilal al-Minuki babban jagoran ISIS ne da aka bayyana a matsayin na biyu a jerin shugabannin kungiyar a duniya.
Hukumomin Najeriya sun ce an tabbatar da ainihin wanda aka hallaka bayan samun bayanan sirri da na fasaha, duk da cewa an taba samun rahoton kisan wani mai irin wannan suna a 2024.
Asali: Legit.ng
