"Na Bar Su da Allah"; Mataimakin Gwamnan Kebbi Ya Yi Maganar Cire Shi Takara a 2027
- Mataimakin Gwamnan Kebbi, Umar Abubakar-Tafida, ya karyata cewa hukuncin Kotun Koli kan zaben 2023 ne ya jawo sauya shi a matsayin abokin takarar Gwamna Nasir Idris
- Abubakar-Tafida ya ce sauya shi wani bangare ne na sauye-sauyen siyasa, amma ya yi watsi da ikirarin cewa hukuncin kotun ne ya haddasa hakan
- Mataimakin gwamnan ya sake tabbatar da biyayyarsa ga APC tare da alkawarin goyon bayan Tinubu da Gwamna Idris a zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kebbi - Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi, Umar Abubakar-Tafida, ya karyata ikirarin cewa sauya shi a matsayin abokin takarar Gwamna Nasir Idris a zaben gwamna na 2027 yana da alaka da hukuncin Kotun Koli kan zaben 2023.
Abubakar-Tafida ya bayyana haka ne ranar Laraba a Argungu, lokacin da dubban magoya bayansa, abokan siyasa da masu fatan alheri suka ziyarci gidansa domin jajanta masa bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sauya shi.

Source: Twitter
Ya bayyana ikirarin da ke alakanta sauya shi da hukuncin Kotun Koli a matsayin wani yunkuri da abokan hamayyarsa na siyasa ke son amfani da shari’ar zaben gwamnan jihar ta 2023 wajen bata masa suna, cewar rahoton Channels tv.
Ya ce sauyin wani bangare ne na siyasa
Mataimakin gwamnan ya ce ya amince da shawarar sauya shi a matsayin abokin takarar gwamnan, yana mai cewa hakan na daga cikin sauye-sauyen da ake samu a siyasa.
Sai dai ya yi watsi da yunkurin alakanta lamarin da hukuncin Kotun Koli, yana mai bayyana wannan labari a matsayin “abin kunya kuma kirkirarre”, jaridar Daily Trust ta kawo labarin.
“Duk abin da ya faru, ba mu da wata matsala da shi saboda duk abin da aka yi, an yi shi ne da izinin Allah da kuma yardarsa."
“Duk abin da mutum ya yi ba zai taba yin tasiri ba sai da izinin Allah. Babu wani abu na dindindin a rayuwa. Ko da kana siyasa ko ba ka siyasa, mutum zai iya samun ci gaba a rayuwa idan Allah ya so."
“Amma amfani da batun shari’ar da jam’iyyar adawa ta gabatar a gaban Kotun Zabe, wanda daga baya Kotun Koli ta yanke hukunci a kai, sannan a ce yanzu saboda haka ya kamata a sauya ni, wannan abin kunya ne kuma kirkirarre ne,” in ji shi.
Ya zargi abokan hamayya
Abubakar-Tafida ya zargi abokan hamayyarsa da siyasa da kitsa yunkurin bata masa suna da kuma rage martabarsa a fagen siyasa.
Ya ce manufar wadanda ke yada abin da ya kira karya ita ce bata masa suna na siyasa har abada.
“Manufar wadanda ke yada wadannan karairayi ita ce su bata min suna a siyasa har abada. Ba za mu taba amincewa da hakan ba."
“Za mu ci gaba da fadin gaskiyar abin da ya faru. Duk wanda ya yi wani abu domin bata min suna, na bar shi da Allah. Shi ne zai yi musu hukunci kan manufarsu,” in ji shi.

Source: Twitter
Gwamnan Kebbi ya yi alkawari
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kebbi ta yi nuna damuwa game da harin yan bindiga da suka yi ajalin jami'an yan sanda har guda 10.
Gwamnatin ta yi alkawarin tallafa wa iyalan ’yan sanda 10 da wasu mutanen da ’yan ta’adda suka kashe a yankin Rafin Makuku, ƙaramar hukumar Sakaba.
Asali: Legit.ng

