'Da Bello Turji ne da Tuni Sun Sake Shi': Malami kan Tsare Nnamdi Kanu a Sokoto

'Da Bello Turji ne da Tuni Sun Sake Shi': Malami kan Tsare Nnamdi Kanu a Sokoto

  • Fasto Ezekiel Dachomo ya nuna damuwa kan ci gaba da tsare Nnamdi Kanu a gidan yarin Sokoto, yana mai danganta lamarin da addini
  • Dachomo ya yi addu’ar samun nasarar Kanu, tare da zargin cewa wasu Musulmi na shirin mamaye Kiristoci da Musulunci, yana mai cewa shirin zai tarwatse
  • Faston ya yi ikirarin cewa Kanu zai fito daga gidan yari, yana cewa karfin Yesu Almasihu zai rusa duk wata makarkashiya da ake yi masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau - Babban fasto a Plateau, Ezekiel Dachomo ya yi magana game da ci gaba da rike Nnamdi Kanu a Sokoto.

Faston ya nuna damuwa kan rashin adalci da ake yi wa Kanu saboda kawai shi Kirista ne inda ya yi addu'o'i domin samun nasara.

Fasto Dachomo ya zargi Musulmai kan tsare Nnamdi Kanu
Fasto daga jihar Plateau, Ezekiel Dachomo. Hoto: Ezekiel Dachomo.
Source: Facebook

Hakan na cikin wani faifan bidiyo da wakilin Legit Hausa ya gano wanda faston ya wallafa a shafinsa na X a jiya Alhamis 1 ga watan Oktobar 2026 da ke muke ciki.

Kara karanta wannan

Yana hanyar zuwa jana'izar mahaifinsa, ƴan bindiga sun harbe matashi a Sokoto

Fasto Dachomo ya zargi Musulmai a Najeriya

Dachomo ya ce abin takaici ne yadda Musulmi ke kulla masu makirci inda ya tabbatar da cewa babu abin da zai faru kuma shirin zai tarwatse.

Fastom ya yi zargin cewa Musulmi na shirin mamaye su gaba daya, ya tabbatar da cewa da karfin Yesu Almasihu babu abin da zai faru da su.

A cikin bidiyon, Dachomo ya ce:

"Duk wanda ya tsare Kanu a gidan yarin Sokoto, duk wani kullin da ake kullawa, Kanu zai fito.
"Duk wanda ya hana wannan mutumin fitowa saboda shi Kirista ne, da Shekau ne ko Bello Turji saboda Musulmai ne da an sake su.
"Saboda yana Kirista ko, suna tunanin za su mamaye mu da Musulunci ko, ina addu'ar ƙarfin Yesu Almasihu ya tarwatsa duk shirin Musulmi a kan mu."
Fasto Dachomo ya magantu kan tsare Nnamdi Kanu
Taswirar jihar Plateau da fasto Ezekiel Dachomo ya fito. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda Dachomo ke jawo ce-ce-ku-ce a Arewa

Ezekiel Dachomo na ɗaya daga cikin fastoci da suka fi jawo maganganu musamman a Arewacin Najeriya duba da yadda yake duka Musulmai da suka fi ya a yankin.

Kara karanta wannan

Atiku ya buƙaci Tinubu ya saki El Rufai, Sheikh Zaria, ya taɓo batun Nnamdi Kanu

Yana daya daga cikin wadanda ke yawan korafi ga Amurka kan zargin kisan Kiristoci a Arewa wanda gwamnatin Donald Trump ta nuna damuwa kan haka.

Yawan korafin Dachomo ya ja hankalin ƙasar inda ya ke ba su bayanai cewa tabbas ana yi masu kisan kiyashi a jihar Plateau da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya.

Amurka ta yi magana kan iyalan Dachomo

A baya, mun ba ku labarin cewa gwamnatin Amurka ta yi Allah-wadai da mummunan kisan da aka yi wa wasu daga cikin iyalan Fasto Ezekiel Dachomo a jihar Filato.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce dole ne a hukunta masu hannu a kisan tare da ƙara tsaurara matakan tsaro ga Kiristoci da sauran al'ummomin da ke cikin haɗari.

Lamarin ya haifar da martani daga masu amfani da kafafen sada zumunta, inda wasu suka nuna shakku kan matsayar gwamnatin Amurka kan matsalar tsaro a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.