'Yan Najeriya Sun Samu Dama da Saudiyya Ta Amince da Bukatar NAHCON a Hajjin 2027
- Saudiyya ta ƙara wa Najeriya kujerun Hajji 10,000, inda jimillar adadin mahajjatan da za su je Hajjin 2027 ya kai 60,000.l
- Daga cikin ƙarin kujerun, 7,500 za a bai wa hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi, yayin da 2,500 za su tafi ga kamfanonin yawon buɗe ido
- NAHCON ta ce za a tafiyar da kujerun cikin gaskiya da bin ƙa’idojin Najeriya da Saudiyya da suka shafi aikin Hajji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta ce Saudiyya ta ƙara wa Najeriya kujerun Hajji 10,000 domin aikin Hajjin 2027.
Wannan ƙarin ya sa adadin kujerun da Najeriya za ta samu ya tashi daga 50,000 zuwa 60,000 na mahajjata.

Source: Twitter
Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da Shugaban Sashen Yaɗa Labarai na NAHCON, Shafii Mohammed, ya fitar ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoban 2026, cewar rahoton jaridar Leadership.
Yadda aka raba ƙarin kujerun
A cewar hukumar, daga cikin ƙarin kujerun 10,000, an ware 7,500 ga hukumomin jin daɗin alhazai, hukumomi da kwamitocin aikin Hajji na jihohi.
Sauran 2,500 kuma an ware su ga kamfanonin yawon buɗe ido guda bakwai da ke kan gaba wajen shirya tafiye-tafiyen aikin Hajji.
Hukumar ta ce wannan ƙarin ya faɗaɗa kujerun da Najeriya ta samu tun farko na 50,000, inda jimillar kujerun ƙasar na Hajjin 2027 yanzu suka kai 60,000.
NAHCON ta yabawa Najeriya da Saudiyya
Shugaban NAHCON, Amb. Ismail Abba Yusuf, ya nuna godiya ga gwamnatin tarayya da hukumomin Saudiyya bisa ƙarin kujerun, jaridar The Punch ta kawo labarin.
Ya ce ƙarin ya samu ne bayan ci gaba da tattaunawar diflomasiyya tsakanin gwamnatin Najeriya da Masarautar Saudiyya.
Hukumar ta ce ƙarin kujerun na nuna kyakkyawar dangantakar da ta daɗe tana tsakanin Najeriya da Saudiyya.
Za a tafiyar da kujerun cikin gaskiya

Kara karanta wannan
Amaechi ya hango barazanar da ke fuskantar 'yan adawa idan Tinubu ya zarce a 2027
Ismail Yusuf ya tabbatar da cewa NAHCON za ta tafiyar da ƙarin kujerun cikin gaskiya da bin ƙa’idojin Najeriya da Saudiyya.
Ya kuma ce hukumar za ta tabbatar da cewa an gudanar da rabon kujerun bisa dokoki da buƙatun gudanar da aikin Hajji.
A cewar NAHCON, gwamnatin tarayya ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ci gaba da bayar da goyon baya da jagoranci wajen inganta harkokin Hajji da walwalar mahajjatan Najeriya.
Najeriya ta samu kujeru 50,000 tun farko
Tun da farko, Saudiyya ta ware wa Najeriya kujerun Hajji 50,000 na shekarar 2027. Daga cikin kujerun, 35,000 an ware su ne ga mahajjatan da gwamnati ke daukar nauyinsu, yayin da 15,000 aka ware wa kamfanonin yawon buɗe ido masu lasisin shirya zuwa aikin Hajji.
Bayan ƙarin kujerun 10,000, Najeriya yanzu za ta samu damar kai mahajjata 60,000 aikin Hajjin 2027.

Source: Facebook
Sultan ya shawarci 'yan siyasa kan aikin Hajji
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya gargadi ’yan siyasa da masu rike da mukaman gwamnati.
Sarkin Musulmin ya gargade su da su guji daukar nauyin aikin Hajji ko ziyartar wurare masu tsarki a Makka da Kudus da kudaden da aka samu ta hanyar sata ko cin hanci.
Asali: Legit.ng
