Wata Miyar Sai a Makwabta: Gwamna Ya Nada Hadimai Fiye da 1,000 a Gwamnatinsa
- Gwamnan Ondo ya nada kwamishina guda daya, masu ba shi shawara uku, manyan mataimaka da mataimaka na musamman da dama
- Aiyedatiwa ya tura sunan Erelu Taibat Oloruntoba daga Akoko Arewa ta Yamma zuwa Majalisar Dokokin Ondo domin tantancewa
- Sababbin masu ba gwamna shawara sun hada da Abimbola Fajolu kan muhalli, Ade Adeniyi kan ci gaban karkara da Muyiwa Ogunyemi kan sufuri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Akure, Ondo - Gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya amince da wani sabon zagaye na nade-nade domin karfafa tsarin mulki da inganta ayyukan gwamnati a fadin jihar.
Nade-naden sun kunshi kwamishina guda daya, masu ba gwamna shawara uku, manyan mataimaka 90 da mataimaka na musamman 910, kamar yadda fadar gwamnan ta sanar.

Source: Twitter
Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan, Prince Ebenezer Adeniyan ya wallafa haka a Facebook in da ya ce Erelu Taibat Oloruntoba daga Karamar Hukumar Akoko North-West ce aka zaba a matsayin Kwamishiniyar Ayyuka na Musamman.
An mika sunanta ga Majalisar Dokokin Ondo domin tantancewa da tabbatar da nadinta. Hakan na nufin ba ta fara aiki a matsayin kwamishina ba har sai majalisar ta tabbatar da ita.
Gwamnan ya kuma nada sababbin masu ba shi shawara uku. Su ne Hon. Abimbola Fajolu mai ba da shawara kan muhalli, Chief Ade Adeniyi kan ci gaban karkara da al’umma.
Sauran shi ne Mista Muyiwa Ogunyemi, wanda aka nada mai ba gwamna shawara kan harkokin sufuri. Gwamnatin ta kuma fitar da sunayen wasu daga cikin manyan mataimakan da aka nada.
Daga cikin wadanda aka nada akwai Erelu Toyin Ogungbure mai kula da hada kan mata a yankin Kudu, Bidemi Obayangbon kan gandun daji da Gboluge Olufunmi Alex kan hulda da al’umma a Kudu.
Haka kuma, Hon. Akin Adeniyi zai kula da hulda da al’umma a yankin Tsakiya, yayin da Obayan Theophilus Ayodeji zai kula da wannan bangare a Arewa.
Sauran sun hada da Kelvin Solomon kan harkokin dalibai, Adeolu Iwakun kan ayyukan sa-kai, Samson Job Bazuaye kan man fetur da iskar gas.
Fade Ojamomi zai kula da karfafa matasa da samar da ayyukan yi, yayin da Sam Adepoju zai kula da hulda da jama’a. Alhaji Samad Orijeminiyi zai kula da tallafin karatu.
Victor Omodara zai kula da hada kan jama’a daga tushe, yayin da Abayomi Adefolalu zai kula da daukar hotuna.
Alhaji Abdulkadiri Adenoyi, Prince Nzuoma Egbulefu da Alhaji Garba Goni kuma an nada su masu kula da al’amuran wadanda ba ’yan asalin jihar ba.
Adeniyan ya ce za a fitar da cikakken jerin sunayen manyan mataimaka 90 da mataimaka na musamman 910 nan gaba.
Gwamna ya umarci bude tsohon masallacin Juma'a
A baya, kun ji cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya ba da umarnin sake bude babban masallacin Juma'a bayan shekaru hudu a kulle.
An rufe masallacin tun 2022 saboda rikicin shugabanci da ya dabaibaye limancin masallacin da ake faragabar barkewar rikici.
An umurci Sheikh Abubakar Muhammed Abbas da ya ci gaba da jagorantar sallar Juma’a kamar yadda yake yi a baya.
Asali: Legit.ng

