Takaitaccen labarin Adams Oshiomhole yayin da ya cika shekaru 68
A Ranar 4 ga Watan Afrilu ne shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ya cika shekaru 68 a Duniya. Mun tsakuro maku takaitaccen tarihin wannan ‘Dan siyasa.
1. Haihuwa da Musulunci
An haifi Adams Aliyu Oshiomhole ne a shekarar 1952 a wani Gari mai suna Iyamho da ke kusa da Garin Auchi. Auchi Gari ne wanda ya yi fice da Musulmai da Musulunci a tarihi. A dalilin haka aka haifi Adams Oshiomhole a cikin gidan Musulunci, amma daga baya ya koma Kirista.
2. Ilmi
Mutane da-dama ba su san cewa Adams Oshiomhole ya fara aiki ba ne tun bayan lokacin da ya gama sakandare. Oshiomhole ya smau aiki da kamfanin masakar Arewa a wancan lokaci.
Daga baya Oshiomhole ya tafi Makarantar Ruskin da ke Oxford a Ingila inda ya yi Digiri a fannin tattalin arziki da huldar kasa da kasa. Oshiomhole ya kuma yi kwas a Makarantar NIPS ta Kuru.
3. Aure
Tsohuwar Mai dakin Adams Aliyu Oshiomhole watau Clara Oshiomhole ce wanda ta yi sanadiyyar komawarsa Kirista inda ya zabi Eric a matsayin sunan Mabiya Darikar Katolika.
KU KARANTA: Gwaji ya nuna Adams Oshiomhole bai dauke da COVID-19
Bayan rasuwar Clara Oshiomhole, Adams Oshiomhole ya yi shekaru ya na gwauranci. Sai daga baya ne ya hadu da Lara Fortes ‘Yar kasar Cape Verde wanda ya aure ta a shekarar 2015.
4. Gwargwamaya
Abin da jama’a ba za su manta game da Adams Oshiomhole bas hi ne tsohon ‘Dan gwagwarmaya ne. Tun ya na Matashi ya zama Sakataren kungiyar kwadago a lokacin ya na aiki a Arewa.
A 1999 aka zabi Adams Oshiomhole a matsayin shugaban Kungiyar kwadago na Kasa watau NLC. A lokacin Oshiomhole ya rika arangama da gwamnatin shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
5. Siyasa
A 2007 Adams Oshiomhole ya shiga siyasa tsindum har ya yi takarar gwamna a Edo a jam’iyyar AC. Oshiomhole ya sha kashi a hannun PDP, amma a 2008 kotu ta ce shi ya lashe zaben.
Bayan Oshiomhole ya zarce a mulki ya zo daf da karshen wa’adinsa, sai ya marawa Godwin Obaseki baya domin ya gaje shi. Haka kuwa aka yi, amma kafin ayi nisa su ka samu sabani.
A 2018 ne aka zabi Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya. Oshiomhole ya gamu da barazana a kujerarsa har ta kai an dakatar da shi a farkon 2020.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng