Kasa Ta Ci Wuta: Ƙungiyar Kiristoci ta CAN Ta Tura Buƙata ga Bola Tinubu
- Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da farfadowar tattalin arziki ya sauya rayuwar talakawa
- CAN ta ce ya kamata a rage farashin abinci, sufuri da makamashi, tare da inganta ilimi, kiwon lafiya, tallafin jama’a da samun rance mai sauki
- Kungiyar ta kuma bukaci gwamnati ta kara tsaro, tare da gargadin ’yan siyasa kada su yi amfani da addinin Kirista wajen yakin neman zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta nuna damuwa game da halin da ake ciki a fadin kasar.
CAN ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa farfadowar tattalin arzikin kasa ya haifar da sauyi mai ma’ana a rayuwar talakawan Najeriya.

Source: Twitter
CAN ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da shugabanta, Daniel Okoh, ya fitar domin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai, cewar Punch.
Shawarar kungiyar CAN ga Tinubu
Kungiyar ta ce nasarar sauye-sauyen tattalin arziki ya kamata a auna ta ne da yadda iyalai ke iya samun muhimman bukatun rayuwa, matasa ke samun ayyukan yi masu kyau, sannan al’umma ke rayuwa cikin aminci.
CAN ta marabci abin da ta bayyana a matsayin sauyawa daga zamanin gyare-gyaren tattalin arziki zuwa zamanin wadata, amma ta yi gargadin cewa kididdigar tattalin arziki kadai bai kamata ta zama ma’aunin ci gaba ba.
Kungiyar ta bukaci gwamnati ta mayar da rage farashin abinci, sufuri da makamashi cikin abubuwan da za a iya auna nasararsu, tana mai cewa ’yan Najeriya da suka sha wahalar tattalin arziki na tsawon shekaru sun cancanci samun saukin rayuwa.
CAN ta kuma bukaci a karfafa tsarin tallafawa masu rauni a cikin al’umma, musamman ta hanyar inganta damar samun ilimi, kiwon lafiya da rance mai sauki.
Ta bukaci gwamnati ta tabbatar da cewa ana gudanar da irin wadannan shirye-shirye cikin gaskiya da rikon amana, tare da kare su daga karkatar da kudade, tana mai cewa wadata da ba ta kai ga gidajen talakawa ba ba cikakkiyar wadata ba ce.
Dangane da tsaro, kungiyar ta ce ba za a samu wadata ta hakika ba a yanayin da ’yan kasa ba sa iya noma, kasuwanci, tafiya ko barci cikin kwanciyar hankali saboda tsoro.
Saboda haka, ta bukaci a ci gaba da daukar matakan kare rayukan jama’a, tabbatar da tsaron al’umma da kuma dawo da amincewar jama’a a sassa daban-daban na kasar.
Kungiyar ta kuma gargadi ’yan siyasa gabanin zaben 2027 kan kada su gabatar da kansu a matsayin masu ceto, tare da kira ga Kiristoci su yi amfani da ’yancinsu wajen goyon baya ko sukar ’yan takara ba tare da janyo sunan Yesu Almasihu cikin rikicin siyasa ba.
CAN ta ce:
“Babu wani dan siyasa da yake kamar Almasihu, a guji amfani da sunasa.”
Kungiyar ta sake tabbatar da kudurinta na ci gaba da kasancewa murya mai zaman kanta daga jam’iyyun siyasa, tana mai cewa za ta ci gaba da yaba abin da ya dace, yin magana idan jama’a na shan wahala da kuma rike shugabanni da ka’idojin adalci, rikon amana da tausayi.
CAN ta taya ’yan Najeriya murnar cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai, tare da kira da a fara wani sabon zamani da alkawarin wadata ya bayyana a rayuwar yau da kullum ta ’yan kasa.
Fastoci na yaki da tikitin Muslim Muslim
Mun ba ku labarin cewa Kungiyar Fastoci ta Najeriya (PFN) ta bayyana cewa ba ta goyon bayan tsarin tikitin takarar shugaban kasa na Musulmi da Musulmi a zabukan shekarar 2027.
PFN ta bayyana cewa Najeriya kasa ce mai mabambanta addinai da kabilu, saboda haka ya kamata shugabancin kasar ya nuna wannan adalci da daidaito.
Matakin na zuwa ne biyo bayan matakin jam'iyyar APC na sake tsayar da Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima a zaben 2027.
Asali: Legit.ng


