Malamar Addini Ta Fito Ta Gayawa Tinubu Gaskiya kan Halin da Ake ciki a Najeriya

Malamar Addini Ta Fito Ta Gayawa Tinubu Gaskiya kan Halin da Ake ciki a Najeriya

  • Apostle Glory Helen Ikeleji ta ce tsadar fetur na ƙara jefa talakawa cikin matsanancin hali, inda wasu ke fuskantar wahalar samun abinci
  • Ta roƙi Shugaba Bola Tinubu da ministocinsa su gaggauta duba matsalolin tattalin arziki da tsadar kayan masarufi da ke addabar ’yan Najeriya
  • Malamar ta kuma yabawa gwamnatin Tinubu kan ƙoƙarin yaƙi da satar mutane da ’yan bindiga, musamman a yankunan Arewacin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Malamar ta koka kan tsadar fetur Yayin da ’yan Najeriya a jihohi 36 da Abuja ke bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kai, wata fitacciyar malamar addini a Kaduna ta yi kira ga gwamnati ta magance matsin tattalin arziki.

Apostle Glory Helen Ikeleji, daga Christ Goshen City Assembly Worldwide, ta ce hauhawar farashin man fetur na jefa al’umma cikin mawuyacin hali.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi maganar hana hawa a Kano bayan kalaman bangaren Aminu Ado

Malamar addini ta ba Tinubu shawara
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Malamar ta bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da jaridar The Punch ta waya ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoban 2026.

Ta bayyana yawan tashin farashin fetur ba tare da daidaito ba a matsayin abin takaici, tana mai cewa talakawa da dama ba sa iya samun abinci sau uku a rana.

A cewarta, cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi ya ƙara wa wasu ’yan Najeriya wahalhalun rayuwa.

“Ina jin zafin wahalar da ’ya’yana ke ciki”

Apostle Glory Helen ta ce kasancewarta uwa ga mabiya da dama da kuma bayin Allah ya sa ta ga wajibi ta faɗi gaskiya ga waɗanda ke da ikon yanke hukunci a ƙasar.

Ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da mambobin majalisar ministocinsa da su gaggauta duba matsalar tare da nemo hanyoyin rage wahalhalun da ’yan ƙasa ke fuskanta.

Ta ce ba za ta iya kallon ’ya’yanta suna fama da yunwa ba tare da ta yi magana ba.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da Tinubu ya tabo a jawabin ranar bikin murnar samun ‘yancin kai

“Ni uwa ce. Zuciyata na ciwo kuma ina matuƙar damuwa idan na ga ’ya’yana mata da maza ba sa iya samun abinci sau uku a rana."
“Babu uwa ta gari da za ta kalli ’ya’yanta suna jin yunwa. Wannan lamari yana ɓata mini rai. Kamar sauran mata da iyaye mata a ƙasar nan, muna kallon ’ya’yanmu suna fama da yunwa saboda rashin abin da za su ci, kuma ba mu farin ciki,” in ji ta.

Tsadar fetur na ƙara tsadar kayan masarufi

Malamar ta ce mutane da dama na fuskantar matsalolin kuɗi saboda yadda farashin fetur ke ci gaba da tashi.

Ta bayyana cewa duk lokacin da farashin fetur ya ƙaru, farashin kayan abinci da sauran muhimman abubuwan da ake buƙata a kullum su ma na ƙaruwa.

A cewarta, hakan na sanya kayan masarufi yin tsada fiye da ƙarfin wasu ’yan Najeriya, musamman masu ƙaramin ƙarfi.

"Mutane suna cikin wahala sosai saboda rashin daidaito da yawan tashin farashin fetur da sauran kayayyakin man fetur."

“Wannan ƙarin farashin ya kuma shafi harkar sufuri sosai, inda zuwa daga wuri ɗaya zuwa wani ya zama tamkar abin alfarma saboda tsadar kuɗin mota. Mutane suna fuskantar wahalhalu da yawa.” In ji ta.

Kara karanta wannan

Zance ya kare: Tinubu ya sanar da 'yan Najeriya halin da ya tsinci kasar a 2023

Ta yabawa Tinubu kan yaƙi da ’yan bindiga

Duk da sukar da ta yi kan matsin tattalin arziki, Apostle Glory Helen ta yabawa gwamnatin Shugaba Tinubu kan ƙoƙarin da take yi wajen yaƙi da masu garkuwa da mutane da ’yan bindiga.

Musamman ta yaba da matakan da gwamnatin ke ɗauka wajen magance matsalar rashin tsaro a Arewacin Najeriya.

Ta ce kafin zuwan gwamnatin Tinubu a shekarar 2023, rashin tsaro ya zama babban abin damuwa ga al’ummar Arewa.

A cewarta, a wancan lokacin, mutane da dama a yankin sun shiga halin tsoro, har suka daina iya kwanciya barci cikin kwanciyar hankali saboda yawaitar hare-hare, garkuwa da mutane da ayyukan ’yan bindiga.

Shugaba Tinubu ya samu shawara
Bola Ahmed Tinubu, shugaban kasar Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Ma'aikata sun fara yajin aiki

A wani labarin kuma, kun ji cewa ma’aikatan gwamnati a matakin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi sun fara yajin aikin gargadi na kwana uku a faɗin Najeriya.

Ƙungiyar JNPSNC ta umarci dukkan ma’aikatan ma’aikatu, hukumomi da sassan gwamnati su bi umarnin yajin aikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng