Tinubu Must Go: Cafke Matasa Ya Bar Baya da Ƙura, ADC Ta Tsoma Bakinta

Tinubu Must Go: Cafke Matasa Ya Bar Baya da Ƙura, ADC Ta Tsoma Bakinta

  • Reshen jam’iyyar ADC na Borno ya yi Allah-wadai da kama wasu matasa biyar da aka ce jami’an tsaro sun cafke saboda sanya rigunan “Tinubu Must Go”
  • ADC ta ce kama matasan ya saba wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, wanda ya bai wa ’yan ƙasa ’yancin faɗin ra’ayinsu
  • Jam’iyyar ta bukaci a saki matasan ba tare da wani sharadi ba, tare da neman afuwa daga jami’an tsaro da kare ’yancin dimokuraɗiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno - Reshen jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) na Jihar Borno ya yi Allah-wadai da abin da ya kira kama matasa biyar ba bisa ka’ida ba a Maiduguri.

Jam’iyyar ta ce an kama matasan ne bisa zargin sanya rigunan T-shirt da ke ɗauke da rubutun “Tinubu Must Go”, lamarin da ta ce bai dace da dimokuraɗiyya ba.

Kara karanta wannan

Matsin da ake ciki yana damun Tinubu, ya fadi hanyar tsame mutane miliyan 5 daga talauci

ADC ta fusata kan kama matasa a Borno
Kakakin jam'iyyar ADC a Najeriya, Bolaji Abdullahi. Hoto: Bolaji Abdullahi.
Source: Facebook

Sakataren yaɗa labarai na ADC na Borno, Hon. Baba Ahmed Mustapha, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a daren Talata, cewar Vanguard.

Cafke matasa: ADC ta yi Allah wadai

Mustapha ya ce jam’iyyar ta samu labarin kama da tsare matasa biyar cikin mamaki, inda ya zargi jami’an tsaro da aikata hakan bisa umarnin jam’iyya mai mulki.

Ya ce ADC ta yi Allah-wadai da abin da ta bayyana a matsayin abin da bai dace da dimokuraɗiyya, Kundin Tsarin Mulki da kuma ’yancin faɗin ra’ayi ba.

Jam’iyyar ta yi nuni da cewa Sashe na 39(1) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, kamar yadda aka yi wa kwaskwarima, ya ba kowane ɗan ƙasa ’yancin faɗin ra’ayinsa.

ADC ta ce sanya T-shirt mai ɗauke da rubutun siyasa wani nau’i ne na bayyana ra’ayi, don haka bai kamata a hukunta mutum saboda hakan ba.

An kama matasa kan kin goyon bayan Tinubu
Taswirar jihar Borno da aka cafke matasa saboda Bola Tinubu. Hoto: Legit.
Source: Original

Shawarar ADC game da bunkasar dimokuraɗiyya

Kara karanta wannan

Kaico: Abin da ya faru wanda ya kai ga kashe babban malamin jami'ar ABU, ya ba da wasiyya

Jam’iyyar ta kuma ce dimokuraɗiyya tana bunƙasa ne ta hanyar samun ra’ayoyi daban-daban, tana mai cewa ’yan ƙasa na da damar yin suka ko kira ga sauyin shugabanci ta hanyoyin da doka ta amince da su.

Ta zargi amfani da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro wajen kama matasa saboda bayyana ra’ayinsu da cewa cin zarafin ikon gwamnati ne da kuma ƙoƙarin tsoratar da al’umma.

ADC ta ce abin mamaki ne yadda jam’iyyar da ta hau mulki ta hanyar zanga-zanga, suka da ’yancin faɗin ra’ayi take ƙoƙarin hana ’yan Najeriya wannan ’yanci.

Jam’iyyar ta ce matasa na fuskantar matsalolin yunwa, rashin tsaro da rashin aikin yi, don haka bai kamata a ƙara musu wani nau’in tsoratarwa ba, cewar Daily Post.

ADC ta bukaci a saki matasan biyar nan take ba tare da wani sharadi ba, tare da neman jami’an da abin ya shafa su ba matasan da iyalansu haƙuri.

Ana neman hada kan Atiku, Obi

An ji cewa tafiyarTinubu Must Go, TMG, ta nemi Atiku Abubakar, Peter Obi, Seyi Makinde da Omoyele Sowore su haɗa kai domin kayar da Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

APC ta fito da sabon gargadi game da zaben Atiku a 2027

TMG ta buƙaci ’yan siyasar su ajiye burinsu na kashin kansu gefe tare da shiga tattaunawar da za ta samar da ɗan takarar da zai wakilci ’yan adawa.

Tafiyar ta ce haɗin kan ’yan adawa zai samar wa ’yan Najeriya damar kayar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.