Babachir Ya Kawo Shawarar da Za Ta Ba Peter Obi da Kwankwaso Nasara a Zaben 2027
- Injiniya Babachir David Lawal yana ganin Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ba su amfana da farin jininsu sosai
- Tsohon sakataren Gwamnatin tarayyan yana so ‘yan takaran na NDC su rika tallata kansu da kyau ga jam’a
- Idan sun shiga cikin jama’a, Babachir yana ganin da bukatar Obi da Kwankwaso su fadi manufofinsu da kyau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - An hira Babachir David Lawal bayan sauya-shekarsa ta tabbata, wannan karo ya yi magana a matsayin ‘dan jam’iyyar adawa ta NDC.
Tsohon sakataren na Gwamnatin tarayya ya yi magana game da alakarsa da Peter Obi da Rabiu Kwankwaso da ke neman mulki a 2027.

Source: Facebook
Babachir Lawal ya ci gyaran 'yan takaran NDC
Tattaunawar Babachir David Lawal da tashar Arise ta tabo zancen siyasa da yadda za a tallata jam’iyyar NDC domin ta shiga Aso Rock.

Kara karanta wannan
Daga zuwa NDC, Babachir ya shiga tono abubuwa har da bayyana masu munafuntar jam'iyya
‘Dan siyasar ya koka cewa Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ba su ci moriyar farin jininsu yadda ya kamata har su iya hambarar da APC.
Babachir David Lawal wanda ya yi yawo daga APC zuwa ADC kafin shiga jam'iyyar NDC ya ce:
“Na zauna da Obi da Kwankwaso, na fada masu cewa idan suka je haduwa da zugar jama’arsu, ba su tallata kansu da kyau.
"Kwankwaso sai ya tara miliyoyin masu jajayen huluna. Su yi rawa, su yi waka, sai ya daga hannunsa. Ban jin komai."
Shawarar Babachir ga Rabiu Kwankwaso
Injiniya Babachir Lawal ya ce Sanata Kwankwaso ya saba tara dubunnan mutane masu jar hula, amma sai taron ya watse babu tasiri sosai.
Ya ce a matsayin Kwankwaso na kwararren injiniyan ruwa, ya kamata ya yi wa magoya baya maganar yadda zai kawo gyara a bangaren.
Ganin yadda ake da madatsun ruwa wato dam dabam-dabam a Arewacin Najeriya, ya ce kyau Kwankwaso ya maida hankali a kansu.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: An ɗauko batun da zai tsoratar da 'yan Arewa kan shirin dawo da tallafin fetur
Babachir yana so Madugun na Kwankwasiyya ya yi bayanin yadda za a gyara madatsun domin a samu ruwa kuma a inganta noman rani.
Yadda Peter Obi zai gyara tafiyarsa
Haka lamarin yake wajen Peter Obi, ya ce ‘dan takaran shugaban kasar na 2027 ya saba shiga coci, iyaka a yi ta ihun kiran sunansa.
Ya bada misali da yadda yake shiga coci sai kowa har da limamai sun dauka, amma ba tare da ya yi maganar yadda zai gyara kasa ba.
“Haka shi ma Obi. Zai je jana’iza a coci sai ya jira sai cocin ya cika makil sannan ya shigo, ya tarwatsa komai, har fasto ya rika kiran ‘Obi, Obi’, hawar ce kurum ba ta cewa komai.”
- Babachir David Lawal
Idan an bi ta Babachir, ‘yan takaran za suna da abin fada a kan aikin hako mai a Kolmani da kuma na samar da lantarki daga Mambilla.
Za a samu bangaren tattaunawar a shafin Nig Affairs a X.
2027: Babachir ya shigo NDC da rikicin gida
A labarin da ya zo a baya, an ji cewa Babachir David Lawal ya yi watsi da zargin adawa da shigarsa NDC da wasu ‘yan takarar gwamnoni suke yi
Daga zuwan shi jam’iyyar NDC ya zama jagora a Arewa maso gabas da Arewa maso tsakiya, wasu sun nuna ba su yarda da wannan matsayi ba.
Sannan Injiniya Babachir Lawal ya ce akwai wadanda suke yaudarar su Peter Obi, suna yi wa 'dan takaran ADC wato Atiku Abubakar aiki a asirce.
Asali: Legit.ng
