Sanata Barau Ya Kori Hadimarsa 'Yar Kannywood daga Mukaminta
- Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya cire Rashida Adamu, wadda aka fi sani da Rashida Mai Sa’a, daga mukaminta.
- Ofishin Barau ya ce matakin ya biyo bayan zargin cewa Rashida ta yi kalaman da za su iya tunzura magoya baya tare da raunana APC
- An kuma zarge ta da yin kalaman batanci kan Barau, yayin da ofishin ya ce wasu daga cikin waɗanda ake zargi sun sauya masa baya bayan sun amfana da tallafinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya cire Rashida Adamu, wadda aka fi sani da Rashida Mai Sa’a, daga mukaminta na Mataimakiya ta Musamman a ofishinsa.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Shitu Madaki Kunchi, mai taimaka wa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, ya fitar ranar Litinin, 28 ga Satumba, 2026.

Source: Facebook
An zarge ta da yin kalaman tunzura magoya baya
A cewar sanarwar, matakin ya biyo bayan wasu zarge-zarge da aka yi wa Rashida, ciki har da yin kalaman da ka iya tunzura magoya baya, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Ofishin ya kuma zarge ta da shiga wasu ayyuka da ake ganin suna da nufin raunana jam’iyyar All Progressives Congress (APC), tare da yin kalaman da suka ci mutuncin Sanata Barau.
Sanarwar ta ce korar ta ta biyo bayan wani saƙo da ofishin ya fitar ranar Lahadi, 27 ga Satumba.
A cikin saƙon, ofishin ya yi zargin cewa wasu mutane na ƙoƙarin lalata muradun siyasar Sanata Barau a jihar Kano da kuma cikin jam’iyyar APC.
Ofishin Barau ya yi wasu zarge-zarge
Ofishin ya ƙara da cewa wasu daga cikin mutanen da ake magana a kai sun taɓa cin moriyar muƙaman da Barau ya ba su da kuma wasu nau’o’in tallafi.

Kara karanta wannan
Matar aure ta kashe kishiyarta a yanayi mara daɗin ji, an gano cutar da ke damunta
Sai dai, a cewar sanarwar, daga bisani waɗannan mutane sun juya masa baya tare da yin aiki da abubuwan da ake ganin suna nuna adawa da shi da jam’iyyar APC.
Ofishin ya bayyana ayyukan da ake zargin mutanen da aikatawa a matsayin ƙoƙarin raunana Sanata Barau da kuma rage ƙarfin APC.
An kuma kori wani mataimaki a baya
Matakin na baya-bayan nan ya zo ne bayan Sanata Barau ya kori ɗaya daga cikin mataimakansa, Umar Alhassan, wanda aka fi sani da King Indara.
An ce an cire Alhassan daga mukaminsa ne bayan wata magana da ya wallafa a kafar sada zumunta wadda ta janyo cece-kuce saboda yadda ta shafi Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
Sanarwar ta ce matakin da aka ɗauka kan Rashida Mai Sa’a ya shafi aikin ofishin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ne, bayan zarge-zargen da aka gabatar kan ayyukanta da kalamanta.

Source: Facebook
Sanata Barau ya yaba wa Sheikh Jingir
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata Barau Jibrin, ya yaba wa shugaban malaman Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Sani Yahaya Jingir, kan aikin da yake yi wa addini da al'umma.
Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya yi godiya ta musamman ga Sheikh Jingir kan gudunmawar da yake bayarwa wajen addini da kuma ci gaban al'umma.
Asali: Legit.ng
