Siyasar 2027: Shugabannin APC Sun Hada kai Sun Yi wa Wike Rubdugu

Siyasar 2027: Shugabannin APC Sun Hada kai Sun Yi wa Wike Rubdugu

  • Wasu shugabannin APC na jihohi sun yi watsi da kungiyar Rainbow Coalition da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ke jagoranta
  • Shugabannin jam’iyyar sun bukaci Wike ya koma APC a hukumance idan da gaske yake goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027
  • Sai dai wasu sassan APC sun ce za su marabci Wike idan ya koma jam’iyyar, yayin da wasu suka ce ba za su amince da tsarin da zai raba kai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Wasu shugabannin jam’iyyar APC na jihohi sun yi watsi da kawancen Rainbow Coalition da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ke jagoranta gabanin zaɓen 2027.

Shugabannin jam’iyyar sun bukaci tsohon Gwamnan Rivers ya koma APC a hukumance idan da gaske yake son taimaka wa Shugaba Bola Tinubu wajen sake lashe zaɓen shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

APC ta fito da sabon gargadi game da zaben Atiku a 2027

Nyesom Wike da Bola Tinubu
Nyesom Wike da Bola Tinubu a fadar shugaban kasa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa rikicin ya ƙara bayyana rashin jituwar da ke tsakanin Wike da wasu gwamnonin APC kan tsarin siyasar da za a yi amfani da shi wajen neman goyon bayan Tinubu a 2027.

APC ta yi watsi da hadakar Wike

A Jihar Imo, Sakataren Yaɗa Labarai na APC, Jones Onwuasoanya, ya bukaci Wike ya bayyana kansa a matsayin cikakken ɗan jam’iyyar APC idan yana goyon bayan Tinubu.

Ya ce bai kamata mutum ya riƙa nuna goyon baya ga jam’iyya a wani mataki sannan ya tallafa wa wasu jam’iyyu a sauran zaɓuka ba.

A Gombe kuma, Sakataren Yaɗa Labarai na APC, Murtala Usman, ya ce Wike ya kamata ya koma APC gaba ɗaya, yana mai cewa kungiyar Rainbow Coalition na iya haifar da ruɗani a cikin jam’iyyar.

Ya ce masu ruwa da tsaki a APC a wasu jihohi na iya samun matsala wajen tafiyar da irin wannan tsari idan aka bar shi ya ci gaba.

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya fadi wanda zai iya nasara a 2027, ya cire Tinubu a lissafi

Jigawa za ta marabci Wike

A Jihar Jigawa, APC ta ce za ta marabci Nyesom Wike idan ya yanke shawarar komawa jam’iyyar kafin zaben 2027.

Sakataren Yaɗa Labarai na APC a jihar, Bashir Kundu, ya ce jam’iyyar ta yaba da irin gudunmawar da Wike ke bayarwa wajen tallata Tinubu da APC a zaɓen 2027.

Kundu ya ce APC ita ma ta samo asali ne daga haɗuwar jam’iyyu daban-daban, don haka za ta iya karɓar ’yan siyasa daga wasu ɓangarori idan suka yanke shawarar shiga cikinta.

Matsayar APC a wasu jihohi

A Ondo, APC ta ce ba za ta amince da tsarin da zai sa a goyi bayan Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa amma a tallafa wa ’yan wasu jam’iyyu a zaɓen majalisu da gwamnoni ba.

Sakataren APC na jihar, Alex Kalejaiye, ya ce jam’iyyar na son samun goyon bayan ’yan Najeriya ga dukkan ’yan takararta a matakai daban-daban.

Gwamnonin APC a Aso Rock Villa
Shugaba Bola Tinubu da gwamnonin APC a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

A Plateau kuwa, Shugaban APC na jihar, Rufus Bature, ya ce ba su san da wata Rainbow Coalition a jihar ba, amma ya ce Wike yana da damar shiga APC idan yana so.

Kara karanta wannan

An fara: Wasu gwamnonin APC na shirin haduwa da Atiku ta bayan fage

A Nasarawa, Sakataren Yaɗa Labarai na APC, Augustine Ogaba, ya ce za su fi farin ciki idan Wike ya shiga APC a hukumance maimakon ya ci gaba da tafiyar tasa.

Wike zai yi wa Tinubu kamfen

A wani labarin, mun ruwaito cewa Wike ya ce zai jagoranci gangamin neman sake zaɓen Tinubu a Abuja da jiharsa ta Rivers.

Wike ya bayyana hakan ne a Abuja bayan ya duba aikin faɗaɗa hanyar Kuje zuwa Gwagwalada, inda ya ce magoya bayan Shugaban Ƙasa suna shirin fara gangamin neman ƙuri’u.

Ya ce APC tana shirya kanta domin gangamin zaɓe mai ƙarfi, yayin da wasu jam’iyyu su ma ke tattara magoya bayansu gabanin zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng