Buba Galadima Ya Fadi Wanda zai Iya Nasara a 2027, Ya Cire Tinubu a Lissafi
- Jigon jam’iyyar NDC, Buba Galadima, ya ce Allah da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ne kawai suka san abin da zai faru a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
- Galadima ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan damar Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso a zaɓen 2027
- Dan siyasar ya ce yana da yakinin Peter Obi da Rabiu Kwankwaso za su iya samun nasara idan aka gudanar da zaɓen cikin gaskiya, adalci da sahihanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Jigon jam’iyyar NDC, Buba Galadima, ya ce Allah da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ne kawai suka san abin da zai faru a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da shirye-shiryen zaben shugaban kasa da sauransu a Najeriya gabanin 2027.

Kara karanta wannan
2027: Tsohon sakataren gwamnatin Najeriya ya sauya sheka, ya bi tafiyar su Kwankwaso a NDC

Source: Facebook
Buba Galadima ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wata tattaunawa a shirin Politics Today na Channels Television, inda ya yi magana kan tikitin Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar NDC.
Magana kan zaɓen 2027
Buba Galadima ya ce yana da yakinin Obi da Kwankwaso za su iya samun nasara idan aka gudanar da zaɓen cikin gaskiya, adalci da sahihanci.
Ya kuma yi zargin cewa ana kai hare-hare cikin tsari kan ‘yan adawa, yana mai cewa Allah da Tinubu ne kawai suka san abin da zai faru a zaɓen.
Akwai rabuwar kai a NDC?
Vanguard ta rahoto cewa jigon NDC ya yi watsi da damuwar da ake nunawa kan yiwuwar samun rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar.
A bayanin da ya yi, Buba Galadima ya ce manyan jiga-jigan jam’iyyar suna tare kuma suna aiki kafada da kafada wajen shirye-shiryen zaɓen 2027.
Dangane da tasirin tikitin Obi da Kwankwaso a Arewacin Najeriya, Galadima ya ce jam’iyyar ta gabatar da tikitin da ta yi imanin zai iya samun karɓuwa a sassan ƙasar.
Bayani kan Obi da Kwankwaso
Buba Galadima ya bayyana haɗin Obi da Kwankwaso a matsayin “tikitin kawo waraka”, yana mai cewa ‘yan siyasar biyu suna taimakon juna wajen cika gibin da ke tsakaninsu.
Ya ce jam’iyyar na gabatar da tikitin mutane masu kwarewa da gogewa, yana mai jaddada cewa wannan ne tsarin da ta dogara da shi.

Source: Facebook
Kwankwaso ya soki Alia
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce Gwamnan Benue, Hyacinth Alia, na bukatar ƙara fahimtar harkokin shugabanci.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata hira, inda ya yi magana kan lamarin da ya faru yayin ziyarar Peter Obi zuwa jihar Benue.
Ya bayyana yadda wasu mutane suka tare ayarin motocin Obi a matsayin lamari mara daɗi kuma wanda ba shi da muhimmanci, yana mai cewa wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar APC sun nuna fushi kan abin da ya faru.
Asali: Legit.ng
