2027: NDC Ta Daura Damara, Za a Yi wa Gwamnan Kano Abin da Accord Ta Yi a Osun
- Dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya ce nasarar Ademola Adeleke a zaben Osun ta nuna cewa jama'a su ne siyasa
- Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo ya ce al’ummar Osun sun kare kuri’unsu tare da tabbatar da aniyarsu ta kare tsarin dimokuradiyya
- Ya bayyana cewa nasarar Adeleke alama ce da ke nuna nasarar da jam'iyyar NDC za ta iya cimmawa a zaben gwamnan Kano na 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC, Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo, ya ce sake lashe zaben gwamnan Osun da Ademola Adeleke ya yi ya nuna cewa nasarar siyasa na tattare da jama'a.
Kwamred Aminu Gwarzo ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 16 ga watan Agusta, 2026 yayin da yake mayar da martani kan nasarar Ademola Adeleke a zaben gwamnan Osun da aka gudanar ranar Asabar 15 ga watan Agusta, 2026.

Source: Twitter
A labarin da ya kebanta ga jaridar Punch, an ruwaito cewa 'dan takarar ya taya Adeleke da al’ummar jihar Osun murnar nasarar, yana mai cewa zaben ya nuna karfin dimokuradiyya da kuma kudurin al’umma na kare zabin da suka yi.
Osun: 'Dan takara a Kano ya magantu
A hirar da ya yi da jaridar, Aminu Abdussalam Gwarzo ya kara da cewa zaben ya nuna dimokuradiyya na hannun jama’a, kuma dole ne a mutunta zabin da suka yi.
A kalamansa:
“Al’ummar sun kare zabinsu tare da nuna kudurinsu na kare tsarin dimokuradiyya."
“Sun yi amfani da hakkinsu na dimokuradiyya tare da sake tabbatar da cewa dimokuradiyya tana aiki yadda ya kamata. Shigarsu zaben ya nuna cewa a karshe iko yana hannun jama’a, wadanda dole ne a mutunta muryoyinsu tare da tabbatar da zabinsu."
Gwarzo ya hango nasarar NDC a Kano
Gwarzo ya ce nasarar Adeleke a Osun na iya zama wata alama ta abin da jam’iyyar NDC za ta iya cimmawa a Kano a zaben gwamna na 2027.

Source: Facebook
Ya ce:
“Nasarar da aka samu a Osun alama ce karara da ke nuna cewa al’umma a shirye suke su kare zabinsu, kuma muna ganin irin wannan yanayi zai faru a Kano a 2027.”
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben bayan ya samu kuri’u 511,067 a karkashin jam’iyyar Accord.
Ya doke dan takarar jam’iyyar APC, Bola Oyebamiji, wanda ya samu kuri’u 444,811. Dan takarar jam’iyyar ADC ne ya zo na uku da kuri’u 17,180.
Kwankwaso ya yi magana kan zaben Osun
A wani labarin kun ji yadda Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi martani ga Gwamna Ademola Adeleke bayan ya sake lashe zaɓen gwamnan Osun da aka gudanar a karshen makn jiya.
Sanata Kwankwaso ya yaba wa al’ummar Osun saboda amfani da haƙƙinsu na zaɓe, yana mai cewa sakamakon ya nuna ƙarfin ikon jama’a wajen tabbatar da zabinsu a siyasar Najeriya.
Dan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC ya kuma yaba wa INEC, tare da kira ga masu ruwa da tsaki su tabbatar da zaɓe mai gaskiya musamman yayin da babban zaben 2027 ke karatowa.
Asali: Legit.ng

