An Fara: Wasu Gwamnonin APC na Shirin Haduwa da Atiku Ta Bayan Fage
- Wasu gwamnonin jam’iyyar APC da ke nuna rashin jin daɗi da wasu tsare-tsaren jam’iyyar sun fara duba yiwuwar kulla alaƙa da Atiku Abubakar gabanin zaben 2027
- Rahotanni sun ce matakin na da nasaba da damuwar da wasu gwamnonin ke nunawa kan tasirin ƙungiyar Rainbow Coalition da ke ƙarƙashin Ministan Abuja, Nyesom Wike
- Wasu majiyoyi sun ce Atiku da jam’iyyar ADC na daga cikin hanyoyin siyasar da ake dubawa domin kare muradun wasu gwamnonin APC da kuma tunkarar Rainbow Coalition
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Wasu gwamnonin jam’iyyar APC da ba sa jin daɗin wasu al’amuran cikin gida na jam’iyyar sun fara tattaunawa kan yiwuwar kulla alaƙa da Atiku Abubakar gabanin babban zaben 2027.
Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da caccaka tsinke tsakanin gwamnonin APC da ministan Abuja, Nyesom Wike.

Kara karanta wannan
Gwamnonin Arewa 7 sun shilla ƙasar Amurka, sun nemo abin da zai amfani 'yan Najeriya

Source: Getty Images
Majiyoyi sun shaida wa Business Day cewa damuwar wasu daga cikin gwamnonin ta fi karkata ne kan yiwuwar Rainbow Coalition da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ta yi tasiri a zabukan gwamnoni da na ’yan majalisu.
Gwamnonin APC na naman mafita
Wani daga cikin masu tallata Tinubu Continuity Project a Arewacin Najeriya ya ce wasu gwamnonin APC da ba su gamsu da al’amuran jam’iyyar ba sun fara tattaunawa da Atiku.
Ya ce sauya sheƙar da wasu gwamnonin jam’iyyun adawa suka yi zuwa APC a baya-bayan nan ya nuna cewa akwai sauye-sauyen siyasa da ya kamata a kula da su.
“Mun ga sauya sheƙar wasu gwamnonin adawa zuwa APC a baya-bayan nan. Don haka barazanar tana nan. Ina sane da cewa wasu gwamnoninmu da ba su gamsu ba suna duba wasu hanyoyi, ciki har da yiwuwar ƙulla alaƙa da Atiku,”
In ji shi.
Premium Times ta wallafa cewa wata majiya daga Arewa mai alaƙa da Arewa Mandate Alliance ita ma ta tabbatar da cewa wasu gwamnonin APC na duba wasu hanyoyin siyasa a wajen jam’iyyar domin kare muradunsu gabanin 2027.
APC ta yi gargagi
Daraktan Yada Labarai na Ƙasa na APC, Alhaji Bala Ibrahim, ya yi gargaɗi kan kulla ƙawance tsakanin gwamnonin APC da jam’iyyun adawa gabanin zaben 2027.
Bala ya ceya kamata biyayya ga APC ta kasance cikakkiya, yana mai cewa bai kamata ɗan jam’iyya ya zaɓi lokacin da zai goyi bayan jam’iyyar da lokacin da zai yi mata adawa ba.

Source: Facebook
“Idan kana biyayya ga wani mutum ko wani abu, dole ne biyayyarka ta kasance cikakkiya. Ba za ka iya zama mai biyayya a wani mataki sannan ka zama marar biyayya a wani matakin ba,”
In ji shi.
Ya ce idan wani gwamna na APC ya nemi ƙawance da wata jam’iyya ko ɗan takara domin kare muradunsa a wasu matakan zaɓe, hakan na iya jawo tambayoyi kan amincinsa ga APC.
Ya ƙara da cewa:
“Muna son jam’iyyarmu ta yi nasara a zaɓe na gaskiya da adalci, ba ta hanyar ƙulla wata yarjejeniya da wasu mutanen da ba ’yan jam’iyyarmu ba.”
APC ta je kotu kan Atiku
A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar APC ta kalubalanci umarnin Babbar Kotun Tarayya da ya ba Atiku Abubakar da ADC damar kai wa Shugaba Bola Tinubu takardun shari’a ta hedkwatar jam’iyyar.
APC ta ce ba a bukatar umarnin, domin lauyoyin Tinubu sun riga sun karɓi takardun shari’ar tare da neman ba shi kariya kafin kotun ta bayar da umarnin kai masa takardun.
Shari’ar da Atiku da ADC suka shigar tana neman a hana Tinubu da APC shiga zaben shugaban ƙasa na 2027, bisa zargin da suka gabatar kan bambancin sunan da ke kan takardar NYSC.
Asali: Legit.ng

