Gwamnatin Tarayya Ta Yi Gargaɗin Ɓarkewar Ambaliya a Kano, Kaduna da Jihohi 22
- Gwamnatin Tarayya ta yi sabon gargadi kan yiwuwar ambaliyar ruwa a jihohi 24 da Abuja tsakanin Satumba zuwa Oktoba
- Cibiyar hasashen ambaliyar ruwa ta ce yankunan na iya fuskantar ruwan sama mai yawa, cunkoson magudanan ruwa da ɓarkewar koguna
- An shawarci mazauna yankunan da ke cikin hadari su tanadi hanyoyin kwashewa, tsaftace magudanan ruwa da kare kadarori
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Gwamnatin Tarayya ta fitar da sabon gargadi kan ambaliyar ruwa, inda ta sanar da al’ummomin jihohi 24 da Abuja cewa ambaliya na iya faruwa tsakanin watan Satumba zuwa Oktobar 2026.
Ma'aikatar ta ce yankunan da abin ya shafa na iya fuskantar ruwan sama, kwararar ruwa a saman kasa, cunkoson magudanan ruwa wadanda za su iya haddasa ambaliya.

Source: Getty Images
Gargadin na kunshe ne cikin hasashen ambaliyar ruwa da Cibiyar Tsarin Gargadin Ambaliyar Ruwa ta Kasa, karkashin Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, ta fitar, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: An ɗauko batun da zai tsoratar da 'yan Arewa kan shirin dawo da tallafin fetur
Yankunan da ambaliyar ruwa ka iya shafa
Ta kasafta yankunan da abin ya shafa zuwa rukuni uku, wato Matsanancin Hadari, Babban Hadari da Jerin Sa-ido na Matsakaicin Hadari, bisa matakin yiwuwar fuskantar ambaliya.
Jihohin da ke da al’ummomin da aka sanya cikin rukunin Matsanancin Hadari sun hada da Benue, Kogi, Kwara, Niger, Adamawa, Bauchi, Taraba, Rivers, Edo, Delta, Cross River, Bayelsa, Akwa Ibom, Abia, Anambra, Ebonyi, Enugu, Imo, Ekiti, Lagos, Ogun, Ondo, Osun da Oyo.
A Ekiti, yankunan da abin ya shafa sun hada da Ado-Ekiti, Ijero, Ikere, Ekiti ta Kudu maso Yamma, Ekiti ta Gabas, Ise/Orun da Ekiti ta Yamma.
A Lagos kuwa, yankunan sun hada da Apapa, Badagry, Epe, Eti-Osa, Ikeja, Ikorodu, Ikoyi, Lagos Island, Lekki, Ojo, Orile Agege, Surulere, Agege, Alimosho da Kosofe.

Source: Original
Yankunan Abuja da ka iya shiga matsala
An sanya Abuja cikin rukunin Babban Hadari, inda Abuja Municipal, Abaji, Asokoro, Bwari, Garki, Gwarinpa, Gwagwalada, Kuje, Kubwa, Maitama, Nyanya da Wuse ke cikin wuraren da aka lissafa.

Kara karanta wannan
Gwamnati za ta samar wa matasan Najeriya ayyuka a ƙasashen waje, an ji yadda tsarin yake
Sauran jihohin da ke da al’ummomin cikin rukunin Babban Hadari sun hada da Nasarawa, Plateau, Bauchi, Taraba, Adamawa da Kebbi, cewar Punch.
Cibiyar ta kuma sanya wasu al’ummomin Bauchi, Borno, Gombe, Yobe, Zamfara, Sokoto, Katsina, Kano, Kaduna da Jigawa cikin wadanda ka iya shiga matsala.
Ta shawarci mazauna yankunan su kasance cikin shirin lura da ambaliya nan take, su tabbatar da hanyoyin kwashe jama’a tare da kare iyalai masu rauni da muhimman kadarori.
An kuma gargadi mazauna yankunan da kada su zauna, ajiye motoci, yin kasuwanci ko adana kayayyaki a wuraren da ambaliyar ruwa ke yawan faruwa, dausayi, gefen koguna da hanyoyin magudanan ruwa.
Ta kuma bukaci mazauna dukkan yankunan da abin ya shafa su bi umarnin kwashe jama’a, su nisantar da yara daga ambaliyar ruwa, sannan su guji tafiya ko tuki cikin ruwa mai gudu.
Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 633
A baya, an ji cewa masu aikin ceto a Nepal da China na ci gaba da neman kusan mutane 3,000 da suka ɓace bayan ambaliyar ruwa da ta mamaye wasu yankunan Himalaya.

Kara karanta wannan
2027: Bayan hukuncin kotu, PDP ta ɗauki matsaya kan takarar Sheikh Pantami a jihar Gombe
Rahotanni sun ce an gano gawarwaki 633 a kasashen biyu, yayin da ake fargabar wasu daga cikin mutanen da suka mutu za su iya gangarawa zuwa India.
Hukumomin Nepal sun ce dubban mutane da suka hada da ma’aikatan tashoshin samar da wutar lantarki, masu yawon bude ido na cikin wadanda ba a gani ba.
Asali: Legit.ng