"Ka ba Mutane Hakuri," Atiku Ya Sake Tono Abin da Bola Tinubu ya Aikata a Najeriya
- Dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Tinubu da jefa ’yan Najeriya cikin tsananin wahalar rayuwa
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya tambayi dalilin ci gaba da karɓar bashi duk da ƙarin kuɗin shigar gwamnati
- Atiku ya buƙaci Tinubu ya fito ya nemi afuwar ’yan Najeriya, sannan ya nesanta kansa daga harkokin mulkin kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a matsayin ɗaya daga cikin gwamnatocin da suka fi jefa Najeriya cikin wahala.
Ya zargi gwamnatin Tinubu da sanya rayuwar yau da kullum ta yi tsada matuƙa, yayin da gwamnati ke ci gaba da karɓar bashi da abin da ya kira “tsananin sha’awar karɓar bashi”.

Source: Facebook
Atiku ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da Phrank Shaibu, Daraktan Sadarwa na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen ADC, ya fitar a madadinsa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Gwamna ya hango abin da ba zai wa 'yan Najeriya daɗi ba kan dawo da tallafin fetur
Atiku ya dauko batun ciyo bashin Tinubu
A cewarsa, idan gwamnati na cewa kuɗin shiga yana ƙaruwa, ya kamata ta bayyana dalilin da ya sa take ci gaba da karɓar bashi da kuma dalilin da ya sa ’yan Najeriya ba sa ganin amfanin da aka yi musu alkawari.
Atiku ya ce bayan sama da shekaru uku da aka nemi ’yan Najeriya su yi sadaukarwa, mutane na fuskantar ƙarin kuɗin abinci, sufuri da makamashi, tare da matsin lamba kan ayyukan gwamnati.
Ya kuma yi nuni da bayanan Ofishin Kula da Bashi na Ƙasa (DMO), wanda ya nuna cewa bashin gwamnati ya kai Naira tiriliyan 166.79 zuwa 30 ga Yuni, 2026.
A cewarsa, bashin gwamnati ya kasance Naira tiriliyan 49.85 a watan Maris na 2023, kafin ya kai N166.79 tiriliyan a watan Yuni na 2026.
Ya nemi Tinubu ya yi bayani
Atiku ya ce yana sa ran Shugaba Tinubu zai gabatar wa ’yan Najeriya cikakken bayani kan bashin, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Ya ce batun bashi ba zai iya rabuwa da abin da ya bayyana a matsayin tazara tsakanin ikirarin gwamnati na farfaɗowar tattalin arziki da halin da talakawan Najeriya ke ciki.
Ya ce ya kamata Tinubu ya ba da haƙuri ga iyalan da ba sa iya samun abinci, ma’aikatan da albashinsu ke ƙarewa a kuɗin sufuri tun kafin ƙarshen wata, iyayen da ke fama da biyan kuɗin makaranta da ’yan fansho da tsada ta lalata wa kuɗinsu daraja.
"Ya kamata Tinubu ya nemi yafiyar mutane"
Atiku ya ce:
“An nemi ’yan Najeriya su yi sadaukarwa, an cire tallafin man fetur, an bar darajar naira ta faɗi sosai kuɗin wutar lantarki da sufuri sun ƙaru. Kuɗin shiga gwamnati ya ƙaru, amma karɓar bashi ya ci gaba.
“Bayan duk wannan, ’yan Najeriya na da damar yin tambaya guda ɗaya mai sauƙi: mene ne ainihin abin da sadaukarwarmu ta saya mana?”

Source: Twitter
Tsohon mataimakin shugaban kasa ya ce ba abu ne mai wahala ba idan gwamnatin Tinubu ta nemi afuwar ’yan Najeriya bisa wahalar da suka shiga.
Atiku ya ƙara da cewa:

Kara karanta wannan
Kwankwaso ya gano abin da ya sa 'yan Najeriya ke shan wahala bayan cire tallafin fetur
“Ku daidaita bayanan bashin, ku nuna wa ’yan Najeriya abin da sadaukarwarsu ta saya musu. Ku nemi afuwar wahalar da aka jefa su ciki, sannan ku sauka ku bar mulki ga waɗanda suka shirya samar dal rayuwa mai sauƙi da araha.”
Atiku ya nemi a canza Tinubu
Kun ji cewa Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, bukaci ’yan Najeriya su canza Shugaba Bola Ahmed Tinubu, su zaɓi sabuwar gwamnati a 2027.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC ya yi alkawarin cewa idan aka zaɓe shi, zai dawo da tallafin fetur tare da ɗaukar matakan ƙarfafa tsaro a ƙasar.
Asali: Legit.ng
