Wata Sabuwa: Nafiu Bala da ADC za Su Koma Kotu, an Saka Rana
- Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dage sauraron wata shari’a da ke kalubalantar shugabancin jam’iyyar ADC zuwa ranar 5 ga Oktoba
- Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, Nafiu Bala Gombe, ne ya shigar da ƙarar yana neman kotu ta rushe shugabancin jam'iyyar
- Alƙali Peter Lifu ya kuma ce kotun za ta yanke hukunci kan bukatar dakatar da ci gaba da shari’ar har sai kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Mai shari’a Peter Lifu na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya dage sauraron wata babbar shari’a da wani jigo a jam’iyyar ADC, Nafiu Bala, ya shigar kan shugabancin jam’iyyar zuwa ranar 5 ga Oktoba.
Shari’ar ta ƙunshi kalubalen da ake yi wa shugabancin jam’iyyar karkashin Sanata David Mark da Rauf Aregbesola da sauran mambobin kwamitin gudanarwa na wucin gadi.

Source: Twitter
Kotu ta dage shari’ar ADC
Tribune ta wallafa cewa mai shari’a Lifu ya bayyana cewa kotun za ta kuma yanke hukunci a ranar da aka ɗage shari’ar kan wata bukatar dakatar da ci gaba da sauraron shari’ar har sai an kammala wata ƙarar ƙaramar hukuma da ke gaban kotun ɗaukaka ƙara.
Ya umarci bangarorin da su shigar da dukkan takardun da suka shafi shari’ar cikin sa’o’i 48 daga ƙarfe 11 na safe ranar 28 ga Satumba, 2026, lokacin da aka bayar da umarnin.
Alƙalin ya kuma umarci a aika sanarwar sauraron shari’ar ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa mai zaman kanta (INEC), wadda aka sanya a matsayin wadda ake ƙara ta huɗu.

Source: Facebook
Abin da Nafiu Bala ke nema
Nafiu Bala, wanda ya taɓa kasancewa mataimakin shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, ya nemi kotu ta hana David Mark, Rauf Aregbesola da mambobin kwamitin gudanarwa na wucin gadi na jam’iyyar bayyana kansu a matsayin shugabannin ADC.

Kara karanta wannan
Kotun musulunci ta ɗauki matakin farko kan wadanda ake zargi da kisan Dan Shagamu a Kano
Ya yi zargin cewa yadda Mark, Aregbesola da sauran mambobin kwamitin suka samu shugabancin jam’iyyar ya saɓa wa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin ADC da kuma dokar zaɓe.
An shigar da ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1819/2025, inda aka sanya ADC, David Mark, Rauf Aregbesola, INEC da Ralph Nwosu a matsayin waɗanda ake ƙara na ɗaya zuwa na biyar.
Atiku ya caccaki Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya goyi bayan buƙatar ƙungiyoyin ƙwadago na neman ƙarin mafi ƙarancin albashi.
Atiku ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da jefa ma’aikata cikin matsin tattalin arziki, yana mai cewa cire tallafin man fetur ya sa farashin kayayyaki da sufuri suka tashi kafin a samar da isasshen matakan saukaka rayuwa,.
A wata sanarwa da Daraktan Sadarwa na Kwamitin Yaƙin neman Zaɓen ADC, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce man fetur, sufuri, abinci da haya suna cinye kuɗin shigan ma’aikata.
Asali: Legit.ng
