‘Yan takara 3 da Ake Hangen Za Su Kai Labari a Zaben Gwamnan Jihar Osun

‘Yan takara 3 da Ake Hangen Za Su Kai Labari a Zaben Gwamnan Jihar Osun

Osun - ‘Yan takara daga jam’iyyu har 15 ne ake fafatawa da su a zaben gwamnan jihar Osun da ake yi a ranar Asabar 15 ga Agusta 2026.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

A cikin jerin wadanda suka fito suna sha’awar zama gwamna a Osun a zaben nan, an fi hango nasara a wajen wasu ‘yan takara uku.

Osun.
Manyan 'yan takaran gwamna a Osun da suke takara a APC, ADC da Accord Hoto: Afolabi Henry Adedapo/Gov Ademola Adeleke/Rauf Aregbesola
Source: Facebook

'Yan takarar da ke neman kujerar gwamnan Osun

1. Ademola Adeleke - Accord Party (AP)

2. Bola Oyebamiji - All Progressives Peoples Congress (APC)

3. Najeem Salam - African Democratic Congress (ADC)

4. Farinloye Olarenwaju – Action Alliance (AA)

5. Esan Olajide – African Action Congress (AAC)

Kara karanta wannan

Osun 2026: Jerin manyan yan takarar gwamna 14, jam'iyyu, shekaru da matakin karatunsu

6. Adeagbo Opawoye – African Democratic Party (ADP)

7. Mustapha Adeniyi – Social Democratic Party (SDP)

8. Adesina Aseyemi-Doro – All Progressives Grand Alliance (APGA)

9. Adewale Adebayo – Allied People Movement (APM)

10. Clement Adesuyi – Action Peoples Party (AAP)

11. Masilo Adeleke – Boot Party (BP)

12. Taofeek Adeleke – New Nigeria Peoples Party (NNPP)

13. Saliu Oyelami – Peoples Redemption Party (PRP)

14. Ogunsakin Olalekan – Young Progressives Party (YPP)

Kara karanta wannan

Abubuwa 3 da za su iya sa gwamna Adeleke doke APC a zaben Osun

15. Adefemi Adesuyi – Zenith Labour Party (ZLP)

'Yan takara 3 da ke gaba a zaben Osun

Wani rahoto da tashar talabijin Channels ta fitar ya yi bayanin ‘yan takaran da ake ganin a cikin su gwamnan jihar Osun zai fito.

‘Yan takara su ne shi Gwamna Ademola Adeleke sai Bola Oyebamiji na jam’iyyar APC da Najeem Salam wanda ADC ta tsaida.

1. Ademola Adeleke

Ademola Adeleke zai yi bakin kokarinsa wajen ganin ya zarce a ofis, ya cigaba da mulki na wasu tsawon shekaru hudu a Osun.

Gwamnan ya tsaya takara ne a jam’iyyar Accord da ya shiga sakamakon sauya-sheka da ya yi daga PDP a shekarar da ta gabata.

Tsohon ‘dan kasuwan mutumin yankin Ede kuma ya fara yin takara ne a zaben 2018, sai a zaben 2022 ne ya dawo ya samu galaba.

Imole ya shigo siyasa ne lokacin da ya maye gurbin Adetunji Adeleke lokacin da sanatan ya rasu yana Majalisar dattawa a 2017.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin 'yan takara da jam'iyyunsu da ke fafatawa a zaben gwamnan Osun

2. Bola Oyebamiji

Bola Oyebamiji da yake rike da tutar APC a zaben 2026 ya san gwamnatin Osun domin ya yi aiki tun zamanin Rauf Aregbesola.

Tsohon kwamishinan kudin ya kuma yi aiki da gwamnatin Adegboyega Oyetola. Kafin yanzu shi ne shugaban hukmar NIWA.

Yadda ya sauka daga shugabancin NIWA a 2025, zai dage wajen ganin ya ci zaben yau.

Cikakken sunan shi Asiwaju Munirudeen Bola Oyebamiji, don haka ake yi masa lakabi da Ambo, mutumin Ikire ne a Irewole.

Osun.
Bola Oyebamiji da ke yi wa APC takarar gwamnan jihar Osun Hoto: Governor Ifedolapo Osun
Source: Facebook

3. Najeem Salam

Jam’iyyar hadaka ta ADC ta tsaida Najeem Salam wanda kwararren ‘dan siyasa ne kuma wanda a boko sai da ya samu digirin PhD.

Shi mutumin Ejigbo ne a karamar hukumar Ejigbo kuma tun 2007 ya shiga siyasa lokacin da ya tsaya takarar majalisar dokokin jiha.

Najeem ya samu matsala a kotu amma daga baya ya koma majalisa. Daga 2011 zuwa 2015, shi ne ya shugabanci Majalisar jihar Osun.

Kara karanta wannan

Kungiyar ASUU ta fito tana kumfar baki da 'yan sanda suka kama malaman jami’a

Abin da ‘dan takaran yake takama da shi ne karfin hadakar ADC da goyon bayan da Rauf Aregbesola wanda ya yi gwamna a baya.

Matakin karatun 'yan takaran gwamnan Osun

An ji cewa zaɓen gwamnan Osun na 2026 na da ‘yan takara daga jam’iyyu daban-daban, ciki har da maza 13 da mace ɗaya rak.

Shekarun ‘yan takarar sun kasance daga 37 zuwa 69, yayin da matakan karatunsu suka fara daga sakandare zuwa digirin MSc.

Daga cikin manyan ‘yan takarar akwai Gwamna Ademola Adeleke na Accord, Najeem Salam na ADC da Bola Oyebamiji na APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng