Osun 2026: Jerin Manyan Yan Takarar Gwamna 14, Jam'iyyu, Shekaru da Matakin Karatunsu

Osun 2026: Jerin Manyan Yan Takarar Gwamna 14, Jam'iyyu, Shekaru da Matakin Karatunsu

Osun, Nigeria - Kamar yadda sanarwa ta gabata, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta shirya gudanar da zaben gwamnan jihar Osun a ranar Asabar, 15 ga watan Agusta, 2026.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zaɓen gwamnan Osun na 2026 na da jimillar ‘yan takara 14 da ke neman jagorantar jihar na tsawon shekaru hudu masu zuwa, inda suke wakiltar jam’iyyu daban-daban, matakan karatu da shekaru.

Adeleke.
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke yana jawabi a wurin taro a Osogbo Hoto: @Adeleke01
Source: Twitter

Yan takara 14 za su gwabza

Tashar Channels tv ta kawo duka 'yan takarar, inda daga cikin ‘yan takarar 14, akwai maza 13 yayin da mace daya ce kadai ta fito neman kujerar gwamna a jihar Osun.

Haka kuma, rahotannin lafiya sun tabbatar da cewa babu wani mai nakasa daga cikin ‘yan takarar da aka amince su shiga zaɓen.

Kara karanta wannan

Osun 2026: Muhimman abubuwa 8 da ya kamata kowane mai katin zabe ya sani

Jerin ‘yan takarar Osun

Ga jerin ‘yan takarar 14 da shekarunsu da kuma takardun karatunsu:

1. Gwamna Ademola Adeleke Jackson

Shekara 65 | Jam’iyya: Accord | Karatu: SSCE, digiri na farko BSc

2. Salaam Najeem Folasayo

Shekara 60 | Jam'iyya: ADC l Karatu: FSLC, SSCE, digirin M.Sc.

3. Oyebamiji Bola

Shekara 60 | Jam'iyya: APC | Karatu: FSLC, SSCE, HND

4. Esan Olajide

Shekara 39 | Jam'iyya: AAC | Karatu: FSLC, SSCE, digirin BSc

5. Olanrewaju Farinloye

Shekara 40 | Jam'iyya: AA | Karatu: GCSE, CCECS

6. Adeagbo Opawoye Yemisi

Shekara 64 | Jam'iyya: ADP | Karatu: B.Ed

7. Adeyemi Olusanya

Shekara 39 | Jam'iyya: APGA | Karatu: SSCE, BSc

8. Adebayo Adewale

Shekara 41 | Jam'iyya: APM | Karatu: FSLC, BSc, MBA

9. Adesuyi Clement

Shekara 69 | Jam'iyya: APP | Karatu: FSLC, SSCE, digirin BSc

Kara karanta wannan

Cikakken jerin 'yan takara da jam'iyyunsu da ke fafatawa a zaben gwamnan Osun

10. Adeleke Taofeek

Shekara 52 | Jam'iyya: NNPP | Karatu: FSLC, WAEC

11. Ogunsakin Enoch

Shekara 37 | Jam'iyya: YPP | Karatu: digirin BSc

12. Adeleke Masilo

Shekara 65 | Jam'iyya: BP | Karatu: FSLC, digirin BSc, AdvIP

13. Saliu Oyelami

Shekara 49 | Jam'iyya: PRP | Karatu: FSLC, SSCE, digirin BSc

14. Adesuyi Olufemi

Shekara 50 | Jam'iyya: ZLP | Karatu: FSLC, SSCE, PGD

Manyan yan takara.
Najeem Salam na ADC, Bola Oyebamiji na APC da Gwamna Ademola Adeleke na Accord Hoto: Najeem Salam, Bola Oyebamiji, @Adeleke01
Source: Facebook

Abin da masu zaɓe ya kamata su sani

Shekarun ‘yan takarar sun bambanta daga 37 zuwa 69, yayin da matakan karatunsu suka tashi daga takardun makarantar sakandare zuwa digirin MSc.

Yayin da ake tunkarar ranar zaɓe, ana sa ran jam’iyyun da ke takarar za su ci gaba da gabatar da manufofinsu ta hanyar kamfen, muhawara da sauran hanyoyin neman kuri’un jama’a.

Sanin ‘yan takarar na daga cikin muhimman abubuwan da masu zaɓe za su duba domin samun damar yin zaɓin da ya dace, kamar yadda Premium Times ta kawo.

Kara karanta wannan

Rana ba ta karya: Umarnin da Tinubu ya ba INEC da 'yan sanda kan zaben Osun

An jigbe jami'an tsaro a ofishin INEC

A wani rahoton, kun ji cewa jami’an tsaro da dama sun mamaye ofishin hukumar zabe, INEC da ke kan hanyar Gbongan-Ibadan a Osogbo a jihar Osun.

Wannan mataki na tsaurara matakan tsaro dai na zuwa ne yayin da ake shirye-shirye zaben gwamnan Osun a ranar Asabar, 15 ga Agusta, 2026

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262