Zaben Osun: Gwamna Adeleke Ya Fadi Yadda zai Kifar da APC
- Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bayyana kwarin gwiwar samun nasara a zaben gwamnan jihar da ake gudanarwa a yau Asabar
- Adeleke ya ce yana da yakinin zaben zai gudana cikin lumana, gaskiya da bin ka'idoji, tare da bayyana cewa zai sake samun damar jagorantar jihar na tsawon shekaru hudu
- Gwamnan ya yi wannan magana ne jim kadan bayan da ya kada kuri'arsa a mazabarsa da ke Sagba Agbogunde a karamar hukumar Ede ya Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Ede, Osun – Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bayyana kwarin gwiwar cewa zai yi nasara a zaben gwamnan jihar da ake gudanarwa a yau Asabar.
Rahoto ya nuna cewa Adeleke ya yi wannan magana ne bayan ya kada kuri'arsa a Sagba Agbogunde da ke karamar hukumar Ede ta Arewa.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa gwamnan ya isa rumfar zaben da misalin karfe 8:32 na safe, tare da dimbin magoya bayansa.

Source: Facebook
Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa an tantance shi a matsayin mai kada kuri'a da misalin karfe 8:35 na safe, kafin ya kada kuri'arsa.
Maganar Adeleke kan zaben Osun
Vanguar ta wallafa cewa bayan kada kuri'arsa, Gwamna Ademola Adeleke ya bayyana kwarin gwiwar cewa zai samu nasarar lashe zaben.
Ya kuma bukaci al'ummar jihar da su fito da yawa domin kada kuri'a tare da kare kuri'unsu har zuwa lokacin kammala aikin zaben.
A cewarsa, zaben ya ba al'ummar Osun damar zabar wanda za su ba amanar shugabancin jihar na tsawon shekaru hudu masu zuwa.
Ya bukaci zaman lafiya a Osun
Adeleke ya bukaci masu kada kuri'a da su kasance masu bin doka da oda yayin kada kuri'a da kuma tattara sakamakon zaben.
Ya kuma shawarci masu kada kuri'a da su zauna a rumfunan zabensu domin sanya ido kan yadda ake gudanar da aikin, bisa ka'idojin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).
Gwamnan ya ce yana da yakinin cewa zaben zai kasance cikin lumana, sahihi kuma ya ba al'ummar Jihar Osun abin da suka zaba.

Source: Facebook
Zuwa yanzu dai zaben na tafiya lami lafiya sai dai 'yan kananan matsaloli da suka hada da kama wasu mutane da 'yan sanda suka yi.
Zargin sayen kuri'u a Osun
A wani labarin, mun kawo muku cewa an zargi jam'iyyun APC da Accord da gudanar da wani gagarumin yunkurin sayen kuri'u a sassan Jihar Osun, inda ake zargin wakilan jam'iyyun da bai wa masu kada kuri'a tsakanin N10,000 zuwa N20,000.
An kuma ruwaito cewa wasu masu kada kuri'ar sun ce jam'iyyun sun tattara lambobin asusun bankin dubban masu zabe mako guda kafin zaben, da nufin tura musu kudi bayan sun kada kuri'a.
A zaben, Adeleke na jam'iyyar Accord na fuskantar kalubale daga Bola Oyebamiji na APC, Najeem Salaam na ADC da wasu 'yan takara tara.
Asali: Legit.ng

