Kungiyar ASUU Ta Fito Tana Kumfar Baki da 'Yan Sanda Suka Kama Malaman Jami’a
- Kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ta soki tsare shugabannin reshen Jami'ar Jihar Imo (IMSU) da jami'an 'yan sanda suka yi a Owerri
- ASUU ta jaddada cewa tsare shugabanninta na tsawon sa'o'i ba zai taba sa kungiyar ta cire hannu daga yajin aiki a jami’ar IMSU ba
- Shugabancin kungiyar ya bukaci gwamnatin Imo da mahukuntan jami'a da su koma teburin tattaunawa maimakon amfani da karfi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Imo - Kungiyar ASUU ta reshen Owerri a jihar Imo ta ce jami’an ‘yan sanda sun kama wasu ‘manyan ‘ya ‘yanta a makon nan.
Jagororin kungiyar akalla biyu suka shiga fada hannun jami’an tsaro a Owerri ranar Talata 11 ga watan Agusta 2026.

Source: Getty Images
ASUU ta shiga yajin-aiki a jami'ar IMSU
Premium Times ta rahoto cewa an kama wadannan malamai biyu ne bayan an sanar da shiga yajin aiki a fadin jami’ar IMSU.
Wani jawabi da shugaban ASUU na shiyyar, Dennis Aribodor, ya fitar ya ce an kama Chinedu Egbuchu da Nnamdi Chibo.
Chinedu Egbuchu shi ne mataimakin shugaban ASUU na reshen jami’ar jihar Imo, Nnamdi Chibo kuma sakataren juya kudi ne.
An dakatar da aiki har sai illa Ma sha Allahu a jami’ar ne saboda zargin gwamnatin Imo da gaza cika yarjejeniya da aka yi da ita.
ASUU tana ganin gazawar hukumomi wajen aiwatar da yarjejeniyar shekarar 2025 da aka cimma kan kyautata jin dadin malamai.
ASUU ta reshen na Owerri ce ke kula da jami’ar jihar Imo da jami’ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu da ke a jihar Anambra.
Jawabin kakakin kungiyar ASUU - IMSU
Jawabin ya ce ‘yan sanda sun cafke malaman ne a lokacin da suke kokarin tabbatar da yajin aikin a tsangayar aikin jarida da fannin sadarwa.
Dennis Aribodor ya ce:
"Bayanan da suka zo mana sun nuna shugabannin biyu sun gana da jami’in hulda da jama’a na IMSU a tsangayar, inda ake yin jarrabawa.
“Babu wani fito-na-fito ko fada tsakanin jami’an ASUU da jami’in hulda da jama’ar.

Source: Getty Images
Yadda aka kai shugabannin ASUU zuwa CID
Jaridar Blueprint ta ce ana haka sai lamarin ya canza da shugaban tsaron jami’ar ya iso wurin, ya dauke shugabannin na kungiyar ASUU.
A nan aka dauke Chinedu Egbuchu da abokin aikinsa zuwa sashen ‘yan sanda na CID, aka tsare su na fiye da awanni bakwai ana tambayoyi.
Sai bayan nan sannan aka yi nasarar bada belin kowanensu a kan a N1m da alkawarin za su koma CID a ranar Talata 18 ga Agusta 2026.
ASUU ta ce yajin-aikinsu bai saba doka ba kuma wannan kame ba zai ba ta tsoro ba tare da aika gargadi ga Farfesa Chukwumaeze Uchefula.
Kungiyar malaman ta ce idan wani abu ya faru da su ko iyalansu, za a daura nauyin kan wa shugaban jami’ar, Chukwumaeze Uchefula.
Za a rufe jami'o'i a Kano da Kaduna
Labarin nan cewa ya yi ASUU ta gargadi gwamnatocin jKano, Kaduna, da Jigawa kan jinkirta aiwatar da yarjejeniyar shekarar 2025 da aka rattaba wa hannu.
Ƙungiyar malaman jami'ar ta yi barazanar cewa ƙin cika yarjejeniyar na iya haifar da sabon tsaiko tare da dagula kalandar karatun jami'o'in jihohin.
Saboda haka, ASUU ta buƙaci jihohin da su gaggauta biyan haƙƙoƙin malaman jami'o'i kamar yadda sauran jihohi da gwamnatin tarayya suka fara.
Asali: Legit.ng


