Abin da Ya Shuka a Mulki ne Yake Girba, Sanata Shehu Sani Ya Jero Zunuban El Rufai
- Shehu Sani ya ce abin da ke samun Nasir El-Rufai sakamakon amfani da mulki ta hanyar da ba ta dace ba ne da ya yi
- Ya zarge shi da halin ko-in-kula ga umarnin kotu, tare da tunatar da duniya yadda aka tsare ‘yan jarida da manya a Kaduna
- Kwamred ya yi wadannan maganganu ne lokacin da ake cewa mutanen tsohon gwamnan sun yi watsi da shi da aka cafke shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Tsohon sanata a Kaduna, Shehu Sani, ya yi tsokaci dangane da lamarin Nasir El-Rufai da aka garkame tun tuni.
Sanata Shehu Sani yana ganin cewa miyagun ayyukan da Malam ya aikata ne suke bibiyarsa a yau.

Source: Facebook
Shehu Sani ya tabo batun Nasir El-Rufai
A zantawarsa da tashar Channels a ranar Juma’a, Shehu Sani ya nuna akwai alhakin jama’a a lamarin tsohon gwamnan.
An bijiro da zancen ne ganin Malam El-Rufai ya yi magana game da abokansa da suka yi watsi da shi da yake mawuyacin hali.
Sharrin barin kujerar mulki a Najeriya
‘Dan siyasar ya ce idan mutum ya bar mulki, dama zai rasa abokan tafiyarsa kuma zai rika kallon abubuwa ta wata fuska dabam.
Kwamred Shehu Sani wanda bai shiri da tsohon gwamnan na Kaduna ya yi magana a kan halin da shi ya shiga a baya.
Ya ce ya dade a gidan kaso, kuma ya san yadda abokai suke janye wa daga jikin mutum idan har ya dade yana a daure.
“El-Rufai yana fuskantar sakamakon yadda ya tafiyar da mulki da kuma rashin daukar nauyi a lokacin da yake kan mukamin gwamnati.
"Na ji mutane da dama suna nuna tausayinsu gare shi, amma ni abin da zan ce shi ne: Idan kana kan mulki, ka rika tuna cewa dama ce da aka ba ka, kuma dama ce ta dan wani lokaci da za ta kare.”

Kara karanta wannan
"Allah ne ya cece ni," Gwamna ya ba da labarin yadda aka yi yunkurin kashe shi a gidansa
- Shehu Sani
Zargin da ake yi wa Nasir El-Rufai
Premium Times ta rahoto shi yana cewa El-Rufai ya yi watsi da doka, ya rika saba wa hukuncin kotu lokacin yana karagar mulki.
Shehu Sani ya ce:
"Ya rike mukami; bai yi wa doka biyayya. Bai bin hukuncin kotu. Ya kamata mutane da yawa ya aika su gidan kaso, a yau kuma ya samu kan shi a irin wurin da ya kai mutane da-dama."
Daga 2015 zuwa 2023, kwamred din ya ce gwamnatin Kaduna ta daure Luka Binyat na kusan shekara saboda wani rahoto.
Ya bada misali da cafke malaman Musulunci da aka yi a Zaria saboda sun soki korar ma’aikatan gwamnati da aka yi a jihar.
Akwai wasu shugabannin al’umma a Katchia su 89 da aka daure a gidan gyaran hali na watanni tara saboda sun yi zanga-zanga.
Ya kawo labarin John Danfulani da aka sallama daga jami’ar KASU da wani ‘dan jarida Maida Joseph saboda sukar gwamnati.
‘Dan siyasar ya tuno da abin da ya faru da ‘yan kungiyar IMN a Zariya a gwamnatin baya kuma ya ce ba a kula da sha'anin tsaro ba.

Source: Facebook
Mutanen El-Rufai sun ce ba su kyale shi ba
An ji tsohon mataimakin shugaban Majalisar Kaduna, Muktar Isa-Hazo, ya ce har yanzu shi abokin Nasir El-Rufai ne, duk da bambancin ra’ayin siyasa.
Hon. Hazo ya musanta cewa makusantan tsohon gwamnan sun yi watsi da shi, yana cewa sauyin siyasa ne ya raba wasu daga cikinsu a jihar Kaduna.
Ana ganin cewa wasu abokan aiki, aminai har da ‘yan danginsa sun yi watsi da Malam El-Rufai da hukumomi suka kama shi a farkon bana.
Asali: Legit.ng

