Davido Ya Kira Ruwa, Gwamnati Ta Yi Masa Tatas kan Mika Korafi gaban Trump

Davido Ya Kira Ruwa, Gwamnati Ta Yi Masa Tatas kan Mika Korafi gaban Trump

  • Gwamnatin Edo ta ba Davido shawara kan yunkurinsa na kai korafi ga Shugaba Donald Trump kan zaben gwamnan Osun
  • Kwamishinan yada labaran jihar Edo ya soki matakin Davido na neman Trump ya sa ido kan zaben gwamnan Osun
  • Kassim Afegbua ya ce sakamakon karatun Gwamna Okpebholo da ake yadawa a intanet na bogi ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Benin City, jihar Edo - Gwamnatin jihar Edo ta bukaci fitaccen mawakin Afrobeat, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, da ya mayar da hankali wajen yin wakokin da za su taimaka masa ya lashe kyautar Grammy.

Gwamnatin ta bukaci Davido ya mayar da hankalin ne maimakon barazanar neman Shugaban Amurka Donald Trump ya sa baki kan zaben gwamnan jihar Osun da za a gudanar ranar Asabar, 15 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: 'Hanyar da APC za ta bi don lashe zaben gwamnan Osun'

Gwamnatin Edo ta soki Davido
Mawakin Afrobeats, David Adeleke, da aka fi sani da Davido Hoto: Davido
Source: Instagram

Kwamishinan yada labarai da dabarun sadarwa na jihar Edo, Prince Kassim Afegbua, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a Benin City ranar Alhamis, 13 ga watan Agustan 2026, cewar rahoton jaridar The Punch.

Maganar Afegbua ta zo ne kwanaki bayan Davido ya roki Trump da ya sanya ido kan zaben gwamnan Osun mai zuwa, yana nuna damuwa kan yiwuwar tashin hankali da kuma kawo cikas ga tsarin zaben.

Davido ya kuma bukaci Amurka da kasashen duniya su sanya ido kan zaben tare da karfafa wa hukumomin Najeriya gwiwa su kare masu kada kuri’a da tabbatar da mutunta kuri’unsu.

Edo ta soki kalaman Davido

Da yake mayar da martani kan wannan kira, Afegbua ya bayyana barazanar a matsayin “maganar banza tsantsa”, inda ya ce ba daidai ba ne a soki Gwamna Monday Okpebholo kan shawarar da ya dauka ta yi wa dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) yakin neman zabe.

Kara karanta wannan

Davido ya tafka katobara, lauya ya nuna kuskuren babban mawakin

Afegbua ya ce Davido ya zabi shiga siyasa ne maimakon ya koma dakin daukar waka domin samar da wakokin da za su lashe kyaututtuka.

Ya kuma tunatar da Davido cewa ’yan Najeriya da suka tallafa wa sana’ar wakarsa ba ’yan jam’iyyar Accord Party ba ne.

Afegbua ya yi martani kan sakamakon Okpebholo

Kwamishinan yada labaran Edo ya ce sakamakon karatun Gwamna Okpebholo da ake yadawa a intanet na bogi ne.

“Sakamakon da aka wallafa a intanet na bogi ne. Na ga sahihin sakamakon Gwamnan wanda ya yi amfani da shi wajen samun digiri na biyu. Adeleke ya samu F9 a sakamakonsa. Babu laifi a samu dan rawa a matsayin gwamna. Shi ba dan rawa ba ne? Muna neman kuri’u daga Osun. Muna gaya musu su zabi mutane masu kishin aiki."
“Muna bukatar mu nuna goyon baya ga ’yan jam’iyya da ’yan takararta. Muna farin cikin ganin dan takarar APC ya yi nasara ranar Asabar. Davido, wanda ya kamata ya kasance a dakin daukar waka yana yin wakoki masu kyau, ya koma dan siyasa.” In ji shi

Kara karanta wannan

Babbar magana: Atiku ya yi gargadi mai zafi ga INEC, Tinubu kan zaben Osun

Gwamnatin Edo ta ragargaji Davido
Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo Hoto: Sen. Monday Okpebholo
Source: Facebook

Afegbua ya kara da cewa barazanar rubuta wa Trump korafi “sakarcin banza" ce, yana mai cewa lamarin ya nuna yadda wasu mutane ke kallon dimokuradiyya.

“Sakarcin banza ne a yi barazanar rubuta wa Trump. Ka yi tunanin abin da mutane za su yi idan aka zo batun dimokuradiyya. Gaskiyar magana ita ce Adeleke dan rawa ne. Mulki abu ne mai muhimmanci.” In ji shi

Lauya ya ba Davido shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani lauya kuma marubuci, Timothy Tugbiyele, ya bukaci mawaki Davido, ya ba Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, hakuri.

Lauyan ya bukaci Davido ya bayar da hakurin ne kan wani sakamakon jarabawar WAEC da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng