APC a Adamawa Ta Rikice, Mai Neman Takarar Gwamna Ya Fice daga Jam'iyya

APC a Adamawa Ta Rikice, Mai Neman Takarar Gwamna Ya Fice daga Jam'iyya

  • Rikicin siyasr cikin gida a jam'iyya mai mulki ta APC da ke jihar Adamawa ya fara jawo asarar jiga-jigai da su ke ganin ba a yi masu adalci ba
  • Ɗan takarar gwamna a zaben da ya gabata, Cif Maurice Vonobolki, ya yi zargin cewa ba a yi masa adalci ba, saboda haka ba zai ci gaba da zama ba
  • Ya zargi rashin adalci da yunƙurin tilasta wa masu takara a jam’iyyar yayin da rikici ke kara tsananata tsakanin mabiya gwamna da Nuhu Ribadu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Adamawa – Rikicin cikin gida da ke addabar APC a jihar Adamawa ya kara tsananta bayan daya daga cikin fitattun masu neman takarar gwamna, Cif Maurice Vonobolki, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Jigon ADC ya 'gano' halin da APC ke ciki, ya fadi hadin da zai kai Tinubu ƙasa a 2027

Vonobolki ya bayyana murabus dinsa ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a Yola ranar Talata, 14 ga watan Afrilu, 2026.

Maurice Vonobolkii ya bar APC a Adamawa
Maurice Vonobolki a lokacin da ya ke gana wa da manema labarai kan barin APC Hoto: Majidadi Maurice Vonobolki
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa Cif Vonobolki ya yi zargin cewa jam’iyyar ta yi masa rashin adalci da kuma kokarin tilasta masu ‘yan takara ba tare da bin ka’idojin dimokuradiyya ba.

Rikicin APC a adamawa ya ta'azzara

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Cif Maurice Vonobolki ya ce duk da tabbacin da gwamnan jihar, Ahmadu Umaru Fintiri, da kuma kwamitin da aka kafa domin tsara yadda za a gudanar da zabukan cikin gida, har yanzu babu gaskiya da daidaito a tsarin zaben ‘yan takara.

Ya kara da cewa, matakin ficewar tasa ya biyo bayan shawarwari masu zurfi da ya yi da masu ruwa da tsaki da magoya bayansa, domin kare muradun al’ummar Adamawa.

Vonobolki ya tuna cewa irin wannan rashin adalci ne ya sa shi da magoya bayansa a kananan hukumomi 21 na jihar suka fice daga jam’iyyar PDP a ranar 23 ga Maris, 2026 domin komawa APC.

Kara karanta wannan

Buba Galadima: Ko gawa aka tsayar, za ta buga Tinubu da kasa a zaben 2027'

Cif Maurice Vonobolki ya kara da cewa amma yanzu abin takaicin shi ne sun sake cin karo da irin rashin adalcin da ya koro su daga PDP a APC.

Yadda rikicin APC ya samo asali

Rikicin cikin APC a Adamawa ya samo asali ne bayan sauyin sheƙa da gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya yi zuwa APC, wanda ya haifar da rabuwar kai tsakanin bangarori daban-daban.

Ana zargin tsagin Nuhu Ribadu na rikici da Gwamna Ahmadu Fintiri
Maurice a zantawarsa da manema labarai a ranar Talata Hoto: Majidadi Maurice Vonobolki
Source: Facebook

A yanzu haka, ana fafatawa tsakanin magoya bayan Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da kuma bangaren gwamnan jihar kan iko da tsarin jam’iyyar a jihar.

Vonobolki ya kuma zargi wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar da aikata magudi wajen rajistar mambobi, inda ya ce ana amfani da lambobin NIN na mutane ba tare da yardarsu ba domin kara yawan kuri’u musamman a yankin Yola ta Arewa.

Ya ce duk da alkawarin bai wa dukkannin ‘yan takara dama iri daya a zaben fitar da gwani kai tsaye kamar yadda dokar zabe ta tanada, halin da ake ciki yanzu ya nuna akasin haka.

Ya bukaci dukkan magoya bayansa a fadin kananan hukumomi 21 na jihar da su janye daga APC tare da jiran sabon umarni kan mataki na gaba da za su dauka.

Kara karanta wannan

Malamin addinin Musulunci ya shiga takarar gwamnan Zamfara, ya zabi jam'iyya

Gwamna ya fuskanci cikas kan shiga APC

A baya, mun wallafa cewa wasu daga cikin 'yan jam'iyyar APC na ci gaba da nuna adawarsu da shirin sauya shekar Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi na sauya sheka zuwa cikinta.

Wata kungiyar 'yan APC a jihar Bauchi ta tura wasikar koke ga shugaban jam'iyya na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, inda kungiyar ta bayyana dalilai 10 da ya sa ba ta goyon bayan sauya shekar gwamnan.

Yayin da take lissafa korafe-korafenta, kungiyar ta bayyana abin da ta kira yawan sukar da gwamnan ke yi wa jam'iyyar APC da kuma gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fili.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng