Sanatan APC Ya Yi Barazana ga Tinubu, Zai Yi Murabus daga Jam'iyya Mai Mulki
- Sanata Orji Kalu daga jihar Abia ya bayyana abin da zai jawo ya fice daga jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya
- Kalu ya ce kalaman masu taimaka wa shugaban ba lallai su wakilci ra'ayin Tinubu ba, yana jaddada cewa shugaban na da kyakkyawar alaka da Cocin Katolika
- Ya kuma amince cewa tattalin arzikin talakawa na cikin ƙalubale duk da ci gaban da gwamnati ta samu a bangaren manyan tsare-tsaren tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Umuahia, Abia - Sanatan da ke wakiltar Abia ta Arewa, Orji Kalu, ya bayyana cewa zai iya yin murabus daga jam’iyyar APC.
Sanata Kalu ya ce zai yi haka ne idan har Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taba nuna rashin girmamawa ga Cocin Katolika.

Source: Twitter
Sanatan ya bayyana haka yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels a Abuja.

Kara karanta wannan
Atiku da Peter Obi sun tafka kuskure, an cire su daga barazanar da Tinubu zai fuskanta a 2027
Abin da ya jawo kalaman Sanata Kalu
Kalaman Kalu sun biyo bayan cece-kuce da suka taso bayan ganawar da Shugaba Tinubu ya yi da shugabannin taron fastoci na Cocin Katolika a Najeriya (CBCN), karkashin jagorancin Matthew Ndagoso.
A taron, bishop-bishop din sun bayyana damuwarsu kan tsadar rayuwa da matsalar rashin tsaro da ke addabar Najeriya.
Daga baya, John Onaiyekan, tsohon Archbishop na Abuja kuma Cardinal na Cocin Katolika, ya ce shugaban bai ji dadin sakon da bishop-bishop din suka gabatar ba.
Haka kuma, mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da manufofi, Daniel Bwala, ya zargi Cocin Katolika da goyon bayan ‘yan adawa.
Da yake mayar da martani, Kalu ya ce bishop-bishop din sun yi abin da ya dace domin su ne muryar lamirin kasa.
Ya ce da sun yi shiru kan halin da Najeriya ke ciki, da sun kasa cika nauyin da ke kansu na fadin gaskiya ga masu mulki.

Source: Twitter
Kalu ya yaba wa fastoci kan kokarinsu
A cewarsa, abin da ‘yan siyasa ba za su iya fadawa shugaban kasa ba, fastoci za su fada saboda ba su da wata bukatar siyasa da za su kare.
Game da bukatar a ba Cocin Katolika hakuri, Kalu ya ce bai ga abin da Shugaba Tinubu ya aikata da zai sa ya nemi afuwa ba.
Duk da haka, ya jaddada cewa idan shugaban ya taba nuna rashin girmamawa ga Cocin Katolika ko ‘yan adawa, zai yi murabus daga APC.
A bangaren tattalin arziki kuwa, Kalu ya kare sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa.
Ya ce manyan alamomin tattalin arziki suna samun daidaito, farashin musayar kudade da na fetur suna inganta, sannan masu zuba jari daga kasashen waje suna kara nuna kwarin gwiwa.
Sanata Kalu ya magantu kan mulkin Tinubu
An ji cewa tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Orji Kalu, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba shi da wata babbar barazana daga 'yan adawa kafin zaɓen 2027.
Sanata Kalu ya ce rashin haɗin kai tsakanin jam'iyyun adawa ya raunana ƙarfinsu wajen fuskantar APC.
Sanatan ya kuma bayyana cewa aikin gwamnatin Tinubu zai sa al'ummar Arewacin Najeriya su mara masa baya a zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng

