Da Gaske an Sauya Dan Takarar Gwamna a Adamawa? ADC Ta Bayyana Gaskiya

Da Gaske an Sauya Dan Takarar Gwamna a Adamawa? ADC Ta Bayyana Gaskiya

  • Jam'iyyar ADC a Adamawa ta yi martani kan rahotannin da suke yawo game da maye gurbin ɗan takararta, Ambasada Injiniya Umar Suleiman
  • Jam'iyyar ta ce Umar Suleiman ne halastaccen ɗan takara, babu batun janye takara, maye gurbinsa ko wata tattaunawar sauya sunansa
  • ADC ta ce shugabannin ƙananan hukumomi 21 sun tabbatar da goyon bayansu gare shi, tare da roƙon al'umma su yi watsi da jita-jita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Yola, Adamawa - Jam'iyyar ADC reshen jihar Adamawa ta yi martani kan rahoton sauya dan takarta na gwamna da ake yadawa.

Jam'iyyar ADC ta musanta rahoton wata fitacciyar jarida da ta yi ikirarin cewa za a maye gurbin ɗan takararta na gwamna a zaɓen 2027, Injiniya Umar Suleiman.

ADC ta karyata sauya dan takarar gwamna a Adamawa
Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Hakan na cikin wata sanarwa da Darakta Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Injiniya Umar Suleiman, Dattijo Mark Wosi ya sanya wa hannu, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Iran ta titsiye jami'an Faransa 2 a Tehran, Faris ta yi gargadi

Adamawa: ADC ta ƙaryata sauya dan takarar gwamna

Jam'iyyar ta bayyana rahoton a matsayin ƙarya da masu adawa da ita suka ƙirƙira domin cimma manufar siyasa ta karan kansu.

ADC ta ce Ambasada Injiniya Umar Suleiman ne halastaccen kuma amintaccen ɗan takarar gwamna da aka zaɓa a Adamawa. Ta ce babu wani sauyi game da takararsa.

Sanarwar ta jaddada cewa babu batun maye gurbinsa, janye takara, sauka daga takara ko kuma wata tattaunawa da ake yi kan sauya ɗan takarar gwamna. Jam'iyyar ta buƙaci masu kaɗa ƙuri'a da su yi watsi da jita-jitar da aka ƙirƙira domin yaudarar jama'a.

ADC ta ba mutane shawara kan yada jita-jita
Atiku Abubakar da ɗan takarar gwamnan Adamawa na ADC, Injiniya Umar Sulaiman. Hoto: Atiku Abubakar, ADC Adamawa State.
Source: Facebook

Goyon baya da ɗan takarar gwamna ya samu

ADC ta kuma bayyana cewa goyon bayan da shugabannin ƙananan hukumomi 21 na jihar suka nuna wa Umar Suleiman ya ƙara tabbatar da haɗin kan jam'iyyar da kuma ingancin takararsa.

Jam'iyyar ta ce har yanzu ta mayar da hankali kan aiwatar da manufofinta na yaƙin neman zaɓe ƙarƙashin taken "Ingantacciyar Adamawa", tana mai kira ga magoya bayanta su ci gaba da tsayawa tsayin daka duk da abin da ta bayyana a matsayin yaɗa bayanan ƙarya.

Kara karanta wannan

ADC ta nemi gwamnati ta fito da bayanai kan yadda aka kashe N17.5tr a NNPCL

ADC ta kuma roƙi al'ummar jihar Adamawa da su yi watsi da jita-jitar da ake yaɗawa, tare da ci gaba da bai wa ɗan takararta na gwamna goyon baya yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027.

Tsagin ADC ta dakatar da Atiku, Babachir

An baya, kun ji cewa Wani tsagi na ADC a jihar Adamawa ƙarƙashin Raji Zumo ya yi taron sanar da dakatar da Atiku Abubakar da wasu mutane biyu daga jam'iyyar.

Raji Zumo ya zargi Atiku da sauran mutanen da hannu wajen ƙirƙirar rassan bogi a jam'iyyar, raunana tsarin shugabanci, da yin watsi da umarnin kotu.

Sai dai Babachir Lawal, wanda shi ma aka dakatar da shi, ya bayyana kwamitin Raji a matsayin "masu shan wiwi" wadanda ƙwaya ta bugar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.