Bidiyon Aisha Buhari, Dino Melaye, Seyi Tinubu da Wasu Suna Liyafa a Spain
- Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa Aisha Buhari ta halarci wata liyafar maraba mai kayatarwa gabanin bikin auren Saraya da Bawa a Marbella
- An gudanar da taron ne a La Cabane, wani wurin taro na Dolce & Gabbana da ke Málaga, Spain, inda fitattun ’yan Najeriya da dama suka halarta.
- Dino Melaye, Ben Bruce da Terry Waya na daga cikin fitattun mutanen da aka gani a taron tare da Folake Oyemade ida aka ce har da Seyi Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Spain - An hango tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya, Aisha Buhari, a wata liyafar maraba da aka shirya gabanin bikin aure a Marbella, Spain, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta a ƙarshen mako.
Bidiyon da ya bayyana a yanar gizo ranar Asabar, 19 ga Satumba, 2026, ya nuna liyafar da Saraya da Bawa suka shirya domin tarbar baƙinsu gabanin bikin aurensu.

Source: Instagram
An gudanar da taron ne a La Cabane, wani wurin taro na Dolce & Gabbana da ke Málaga, Spain yayin da Kabiru Salisu ya wallafa bidiyon a X.
Folake Oyemade ma na daga cikin baƙin da suka halarci liyafar mai kayatarwa, lamarin da ya jawo farin ciki daga wasu masoyanta da suka ji daɗin ganinta a wajen taron.
Sauran fitattun ’yan Najeriya da aka gani a wajen taron sun haɗa da ɗan siyasa Dino Melaye, fitaccen mai harkar kafafen yaɗa labarai Ben Bruce, Seyi Tinubu da ɗan kasuwa Terry Waya, da sauransu.
An wallafa hotuna da bidiyon taron ne a shafin Instagram mai suna @mediaroomhubb, inda lamarin ja hankalin mutane a yanar gizo.
Martanin mutane kan liyafar
Lamarin jawo martani da dama daga ’yan Najeriya a Instagram, inda mutane da yawa suka bayyana ra’ayoyinsu kan irin mutanen da suka halarci taron.
@ogeokwesa ya ce:
“Da kun gayyaci Cubana Chief Priest ya kasance tare da ku. Irin wannan yanayin ne yake so. Yin cuɗanya da mutane da kuma zaman tare.”
@jannyposh ta ce:
“Mace ce kyakkyawa sosai 😍”

Source: Facebook
@otunba_agba_akin ya ce:
“Aiki: Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa… Hmm 🤔 Waɗanda ke ihu Sai Baba har yanzu suna cikin talauci da yunwa… ɗan talaka.”
Ga bidiyon su Dino Melaye a kasa:
@opearemo ya rubuta:
“Na ji daɗin ganin Mrs Folake Oyemade ❤️❤️❤️ Kyakkyawa ce. Cc @0rearemo”
@sensationalmonica ya ƙara da cewa:
“Amma mutane za su zaɓi su caccaki jakar matar Obi. Wurin masu…”
Ga bidiyon Aisha Buhari a kasa:
Aisha Buhari ta ziyarci Atiku
A wani labarin, kun ji cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya hadu da Aisha Buhari, inda ya yi amfani da damar wajen magana kai tsaye kan matsalar tsadar rayuwa da ke ƙara ta’azzara a Najeriya.
Idan za a tuna dai dama tun a watan Fabrairu 2026, Atiku da Aisha, matar marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, sun gana a Saudi Arabia.
A wannan karon kuma, Atiku Abubakar ya karbi Aisha Buhari ’yarta Hanan da wasu ’yan gidan Buhari a lokacin da suka kai masa ziyara a gidansa da ke FCT Abuja.
Asali: Legit.ng

