Zaben 2027: Gwamnoni, Malamai da Manyan Arewa Sun Yi Taro, Sun Yiwa Tinubu Mubaya'a

Zaben 2027: Gwamnoni, Malamai da Manyan Arewa Sun Yi Taro, Sun Yiwa Tinubu Mubaya'a

  • Gwamnoni da manyan Arewa sun gana da wakilan mata malaman addini Islama daga jihohin Arewa 19 da Abuja
  • Uba Sani ya ce matan malamai sun nuna goyon bayansu ga sake zaɓen Tinubu a 2027 da ke tafe nan kusa
  • Gwamnan ya ce Arewa ta samu kaso mai yawa daga shirye-shiryen NELFUND da TVET da gwamnatin ke gudanarwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Kaduna - An gudanar da taron nemawa Tinubu kuri'u a zaben 2027 a Cibiyar Taro ta Umaru Musa Yar’Adua da ke Kaduna, inda manyan ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki daga jihohin Arewa suka halarta.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya; Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni; Gwamnan Borno, Babagana Zulum da Gwamnan Kaduna, Uba Sani.

Haka kuma, Ministan Tsaro, Bello Matawalle; Ministan Gidaje, Mustapha Rabe Darma da wasu manyan jami’an gwamnati sun halarci taron.

Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa kan Harkokin Siyasa, Ibrahim Masari ne ya shirya taron, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Wasu malaman musulunci sun faɗa tarkon yan bindiga a hanyar dawowa daga taron APC

Yadda gwamnoni suka taru don nuna goyon baya ga Tinubu
Lokacin da ake taron gwamnoni da malamai a Kaduna | Hoto: @Abdool85
Source: Twitter

An gudanar da shi ne domin ganawa da wakilan kungiyar malaman mata na addinin Islama wato Northern Nigerian Women Ulama daga jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya Abuja.

Dalilin goyon bayan Tinubu

Da yake magana a taron, Uba Sani ya ce haduwar shugabannin siyasa da masu ruwa da tsaki na nuna yadda goyon bayan gwamnatin Tinubu ke ƙara samun karɓuwa a Arewa.

Ya ce matan Ulama da ke wakiltar miliyoyin mata a yankin sun nuna goyon bayansu ga sake zaɓen Tinubu saboda ayyukan da gwamnatinsa ta gudanar.

Sani ya ce ayyukan sun haɗa da habaka ilimi, ababen more rayuwa, kiwon lafiya, noma da koyar da sana’o’i.

A cewarsa:

“Ba wai suna goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne saboda son zuciya ko wata maslaha ta kansu ba. Hakan ya samo asali ne daga abin da ya yi wa Najeriya da musamman Arewa."

Matan Ulama sun yabawa aikin Tinubu a Arewa

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi alhini da aka tabbatar da rasuwar tsohon gwamma a Najeriya

Gwamnan ya ce matan sun kuma yaba da yadda gwamnatin Tinubu ke gudanar da mulki ba tare da nuna bambanci ba.

Ya ce suna ganin gwamnati na rarraba ayyukan ci gaba da damarmaki a sassa daban-daban na ƙasar.

Sani ya ce ilimi na daga cikin manyan abubuwan da ke bukatar kulawa a Arewa saboda gibin da ke tsakanin yankin da sauran sassan ƙasar.

Yadda 'yan Arewa suka mori shirin TVET da NELFUND

Ya ce gwamnatin Tinubu ta zuba jari wajen ilimin boko da kuma koyar da sana’o’i ta hanyar shirin TVET da kuma NELFUND.

A cewarsa, bayanan NELFUND da TVET sun nuna cewa Arewa ta samu gagarumar fa’ida daga shirye-shiryen.

Ya kalamansa:

“Idan kuka duba bayanan NELFUND da TVET, za ku ga cewa Arewa ta samu sama da 60% cikin 100% na tallafin.”

Ya ce hakan na nuna cewa Tinubu ba ya nuna bambanci tsakanin kabilu ko yankuna.

Sani ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki da su kai sakon tallata Tinubu zuwa al’ummomi, mazabu da kananan hukumomi a jihohin Arewa.

Kara karanta wannan

2027: Pantami ka iya goyon bayan Tinubu a kaikaice saboda tasirin Wike a sama

Arewa ta fi amfana da Tinubu, in ji Sani

Gwamnan ya yi ikirarin cewa Arewa ta samu ƙarin moriya a karkashin gwamnatin Tinubu fiye da kowace gwamnati da ta gabata a Najeriya.

Ya ce gwamnati na da bayanai da alkaluma da za su iya tabbatar da wannan ikirari, rahoton jaridar Vanguard.

Sani ya kuma yi watsi da kokarin wasu ‘yan siyasa na mayar da zaɓen 2027 tamkar takarar yakin Arewa da Kudu.

Ya ce irin wannan salon siyasa ya tsufa kuma ba zai taimaka wajen kawo ci gaba ba.

Gwamnan ya bukaci masu ruwa da tsaki su mayar da hankali kan ci gaba, haɗin kai da kyakkyawan shugabanci, maimakon barin batun bangaranci ya mamaye siyasar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng