2027: Ndume Ya Gargadi Tinubu da APC, Ya Ce Suna da Babban Kalubale

2027: Ndume Ya Gargadi Tinubu da APC, Ya Ce Suna da Babban Kalubale

  • Sanata Ali Ndume ya amince cewa jam’iyyar APC mai mulki za ta fuskanci ƙalubale mai tsanani a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027
  • Ya ce fitowar takarar Atiku Abubakar, Peter Obi da Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde za ta iya haifar da kalubale ga jam'iyya mai mulki
  • Ndume ya ce mutanen da ke kewaye da shugaba Bola Ahmed Tinubu ba sa gaya masa gaskiyar halin da gwamnatin ke ciki ta fuskar siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sanata Ali Ndume ya yi gargaɗin cewa babban zaɓen 2027 zai kasance cikin fafatawar siyasa mai matukar zafi a Najeriya.

Ya kwatanta zaben gasar dambe ta WWE, tare da kira ga shugaba Bola Tinubu da ya fuskanci gaskiyar halin da gwamnatinsa ke ciki.

Kara karanta wannan

Babachir ya fadi wanda ya yi kulle kulle aka kore shi a gwamnatin Buhari

Sanata Ali Ndume da Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a hagu da Ali Ndume a gefen dama. Hoto: Bayo Onanuga|Ali Muhammad Ndume
Source: Facebook

Da yake magana a shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels TV, Ndume ya ce ‘yan adawa suna samun ƙarfi, inda ya ce bai kamata APC ta yi sakaci ba.

Dalilin gargadin Ndume ga APC

Kalaman Ndume sun biyo bayan hasashen cewa fitattun ‘yan siyasar adawa, ciki har da Atiku Abubakar, Peter Obi da Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, za su iya kafa ƙawance mai ƙarfi domin kalubalantar APC a 2027.

Da yake mayar da martani kan yiwuwar irin wannan haɗaka, Ndume ya ce bai damu sosai ba, amma ya jaddada cewa raina abokan adawa kuskure ne babba.

“Guguwar tana tafe, amma ban damu sosai da ita ba. A lokaci guda kuma, ba na raina abokan hamayya,”

In ji shi.

Ndume ya gargadi Bola Tinubu

Sanatan ya yi gargaɗin cewa wasu daga cikin mutanen da ke kewaye da shugaba Tinubu ba sa ba shi sahihin bayani game da halin da ƙasar ke ciki.

Kara karanta wannan

Birtaniya za ta sa ido kan zaben Najeriya domin tabbatar da adalci

Ya yi magana yana mai cewa shugabanni na buƙatar samun cikakken bayani kan halin da ake ciki domin su iya magance matsalolin jama’a yadda ya kamata.

“Na faɗi wannan sau da dama a talabijin. Wannan shi ne kuskuren da yawancinmu muke yi, musamman waɗanda ke kewaye da shugaban kasa. Suna da matsala wajen gaya masa gaskiya,”

In ji Ndume.

The Sun ta wallafa cewa Ndume Ya yi hasashen cewa zaɓen 2027 zai kasance mai matuƙar zafi, inda kowane ɓangare zai shirya tsaf domin fafatawa.

“Za mu yi gwagwarmaya tare. Zai iya zama mai tsauri kamar WWE; zai zama fafatawa mai wahala,”

In ji shi.

Ndume ya kuma amince da cewa jama’a da dama suna cikin takaici sakamakon matsalolin tattalin arziki da zamantakewa, amma ya nuna kwarin gwiwa cewa har yanzu akwai damar gyara lamarin idan gwamnati ta ɗauki matakan da suka dace.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Lokacin da Bola Tinubu ya karbi shaidar lashe zaben fitar da gwani na APC. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ga bayanin da Ndume ya yi a bidiyo:

Tinubu ya gargadi 'yan ta'adda

A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa ba za ta miƙa wuya ga ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ba.

Kara karanta wannan

Bayan sukar kalamansa a 2023, Peter Obi ya shawarci matasa kan siyasar addini, kabilanci

Sakon shugaban ƙasar ya zo ne ta bakin sakataren gwamnatin tarayya, George Akume a daidai lokacin da ake alhinin sace dalibai a Borno da Oyo.

Akume ya yi maganar ne a wajen taron addu’a a coci da aka gudanar a Abuja a matsayin wani ɓangare na bukukuwan ranar dimokuraɗiyya ta 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng