An kai Hari Wajen da Ya Shafi Masallacin Annabi SAW a Madina
- Ƙungiyar haɗin gwiwar da Saudiyya ke jagoranta ta zargi mayakan Houthi da kai hari kan wata tashar rarraba wutar lantarki a Madina
- An ce harin ya lalata ɗaya daga cikin na’urorin sauya wutar lantarkin tashar da ke samar da wuta ga Masallacin Annabi SAW
- Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta ta yi Allah-wadai da harin, tana mai cewa kai hari kan wurin da ke samar da wutar Masallacin Madina tsokana ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Saudi Arabia – Ƙungiyar haɗin gwiwar da Saudiyya ke jagoranta ta zargi mayakan Houthi da kai hari kan wata tashar rarraba wutar lantarki a birnin Madina da ke Saudiyya.
A cewar sanarwar kakakin rundunar haɗin gwiwar, harin ya shafi tashar Taibah da ke samar da wutar lantarki ga Masallacin Annabi SAW, inda ɗaya daga cikin na’urorin sauya wuta ya fita daga aiki ba tare da katse tsarin wutar lantarki ba.

Kara karanta wannan
Gwamnati ta ɓullo da wani shiri, za a daina ɗauke wuta a Kano da wasu wurare a Najeriya

Source: Facebook
An zargi Houthi da kai hari Madina
Sanarwar da Saudi ta wallafa a X ta ce harin ya kasance kan wata cibiyar samar da wutar lantarki ga Masallacin Annabi SAW.
Sai dai ikirarin alhakin harin na Houthi ya fito ne daga ɓangaren Saudiyya da ƙungiyar haɗin gwiwar da take jagoranta, yayin da Houthi ta musanta zargin.
Lamarin ya ƙara dagula rikicin da ake fama da shi tsakanin Saudiyya da ƙungiyar Houthi da ke Yemen.
Ƙungiyar Musulmi ta yi Allah-wadai
Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya ta yi Allah-wadai da harin da ta danganta ga Houthi kan tashar wutar lantarki ta Taibah da ke Madina.
Babban Sakataren ƙungiyar, Mohammed bin Abdulkarim Al-Issa, ya yi tir da hare-haren da ake kai wa kayayyakin more rayuwar fararen hula da wuraren ibada.
Ƙungiyar ta ce kai hari kan cibiyar da ke samar da wutar lantarki ga ɗaya daga cikin wuraren ibada mafi tsarki a Musulunci babban tsokana ne ga Musulmi a duniya.
An kai hari kan Houthi a Taiz
A wani ɓangare na rikicin, Al Jazeera ta wallafa cewa rundunar sojin Yemen ta kai hare-haren sama 13 kan wuraren da mayakan Houthi ke amfani da su a lardin Taiz.
Kakakin rundunar, Kanal Majid Al-Nuzaili, ya ce hare-haren sun shafi dakaru da motocin yaƙi na Houthi a wasu yankuna na lardin.

Source: Facebook
Ya ce wuraren da aka kai hare-haren sun haɗa da Al-Ridha, Al-Aqrud, Bani Bakar, Al-Kadha, Jabal Numan, Al-Ajarm da Al-Marazim.
Batun kai hari dakin Ka'aba
A wani labarin, mun ruwaito cewa Saudiyya ta musanta rahotannin da ke cewa an kama wani ɗan kunar bakin wake a Masallacin Harami da ke Makka.
Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ta ce jami’an tsaro sun kama mutumin ne saboda tsangwamar masu wucewa da kuma jawo firgici da tsoro a tsakanin jama’a.
Wasu bidiyoyi da aka yaɗa a kafafen sada zumunta sun yi ikirarin cewa mutumin ya yi yunkurin kai hari kan Ka’aba, amma hukumomin Saudiyya sun ce babu gaskiya a cikin wannan ikirari.
Asali: Legit.ng
