Yadda APC ke Fatan Samun Miliyoyin Kuri'u a Kano da Katsina a 2027
- Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya yi magana kan zaben 2027 da ke tafe da makomar jam'iyyarsu a wasu jihohin Arewa
- Farfesa Nentawe Yilwatda ya jaddada cewa APC na cigaba da samun karbuwa a jihohin Arewa musamman a yankunan Kano da Katsina
- Ya kuma sanar da cewa sauya shekar da 'yan siyasa ke yi zuwa jam'iyyarsu ba zai haifar da wata matsala ba, sabanin tunanin wasu mutane
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar APC, Farfesa Nentawe Yilwatda ya jaddada cewa sun hango alamun samun nasara a zaben 2027.
Ya bayyana haka ne yayin hira da manema labarai, inda ya yi magana kan yadda suke samun goyon baya a wasu jihohi, musamman Kano da Katsina.

Kara karanta wannan
"Duk na kere su": Atiku ya kwatanta farin jininsa da na Kwankwaso, Tambuwal a Arewa

Source: Facebook
Rahoton Vangurd ya nuna cewa Farfesa Nentawe Yilwatda ya yi tsokaci game da yadda 'yan siyasa daga jam'iyyu daban-daban ke shiga APC.
Jama'an APC a jihohin Kano da Kastina
Nentawe ya bayyana cewa manyan rukunan masu jefa ƙuri’a a jihohin Kano da Katsina sun riga sun tsaya tsayin daka tare da jam’iyya mai mulki gabanin zaɓen 2027.
“Zan iya tabbatar muku cewa Kano tuni ta zama tamu, kuma jiha ce mai akala a yankin Arewa maso Yamma,”
In ji shi, yana mai ƙarawa da cewa manyan rukunan masu zaɓe, ciki har da Katsina, suna goyon bayan jam’iyyar APC.
Maganar sauya sheka zuwa APC
Da yake magana kan fargabar cewa shigowar ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa na iya kawo tangarda a cikin APC, Yilwatda ya nuna tarukan jam’iyyar na baya-bayan nan a matsayin hujjar cewa tana nan daram.
“A’a. Idan kuka kalli tarukanmu, ‘yan adawa sun ce bayan su jam’iyyarmu za ta rushe saboda rikicin cikin gida.

Kara karanta wannan
Wutar rikici ta fara tashi a jam'iyyar APC, Yilwatda ya gargadi tsafaffin ƴan PDP
"Amma mun iya daidaita muradun kowa; gwamnonin jihohi, ‘yan majalisar dokoki da sauran mambobin jam’iyyar, kuma mun yi hakan cikin adalci,”
In ji shi.
Shugaban jam’iyyar ya danganta wannan kwanciyar hankali da tsarin warware rikicin cikin gida da ya ce APC ce kaɗai ke da irin sa a Najeriya.
The Sun ta rahoto ya ce:
“Ina ganin babu wata jam’iyya a Najeriya da ke da irin wannan tsarin warware rikicin cikin gida kamar namu,”

Source: Facebook
Maganar yi wa 'yan kasa adalci
Da yake mayar da martani ga masu sukar APC da ke zargin ta da fifita siyasa kan kawo cigaba ga 'yan kasa, Yilwatda ya jaddada cewa abubuwan biyu na tafiya tare.
Ya ce:
“Ba siyasa kawai muka saka gaba ba,”
A halin yanzu, APC na da iko da jihohi 31 cikin 36 na Najeriya, kuma ta fuskanci zarge-zargen yunƙurin mayar da ƙasar zuwa tsarin jam’iyya ɗaya.
An nemi a zabi jam'iyyar APC a 2027
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya nemi a zabi APC a 2027.

Kara karanta wannan
Jigon ADC ya 'gano' halin da APC ke ciki, ya fadi hadin da zai kai Tinubu ƙasa a 2027
Gwamnan ya yi kira ga masu zabe da su kada kuri'a ga shugaba Bola Tinubu, gwamnan APC a Gombe da 'yan majalisar tarayya da na jiha.
Inuwa Yahaya ya yi jawabin ne a lokacin da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC daga karamar hukumar Akko suka kai masa ziyara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng