"Dole Mu Yi Nasara," APC Ta Dauki Babban Mataki kan Zaben Gwamnan Jihar Osun
- Jam'iyyar APC ta kaddamar da kwamitin yakin neman zabe mai mambobi 276 karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma
- Shugaban jam'iyyar na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana zaben na Osun a matsayin gwajin mizanin shirye-shiryensu na zaben 2027
- Jam'iyyar ta lashi takobin gudanar da yakin neman zabe na gida-gida domin tabbatar da nasarar dan takararta, Munirudeen Oyebamiji (AMBO)
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Abuja – Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta kaddamar da kwamitin yakin neman zaben gwamnan jihar Osun na ranar 15 ga Agustan 2026, tana mai bayyana zaben a matsayin wanda dole ne ta yi nasara domin auna shirin da take yi gabanin babban zaben shekarar 2027.
Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da kwamitin a Abuja ranar Talata.

Source: Twitter
Zaben Osun: APC ta kafa kwamiti
Ya ce jam'iyyar za ta yi amfani da dukkan tsarinta na siyasa, mambobinta da kuma hanyoyin yakin neman zabe domin tabbatar da nasarar dan takararta, Munirudeen Oyebamiji, wanda aka fi sani da AMBO, in ji rahoton Punch.
Kwamitin yakin neman zaben mai mutum 276 na karkashin jagorancin gwamnan jihar Imo kuma shugaban kungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodimma.
Yilwatda ya ce an zabo mambobin kwamitin ne domin hada dukkan karfin da ake bukata wajen tabbatar da nasarar APC a zaben.
Ya bayyana APC a matsayin jam'iyyar da ta fi kowacce karfi a Najeriya, yana mai cewa tana da gwamnoni, 'yan majalisun tarayya da na jihohi, shugabannin kananan hukumomi da sauran manyan jiga-jigai da za su taimaka wajen samun nasara.
'Zaben Osun gwajin APC ne kafin 2027'
Shugaban APC ya ce zaben gwamnan Osun shi ne babban zaben karshe da jam'iyyar za ta fuskanta kafin babban zaben kasa na 2027, saboda haka zai zama wata dama ta gwada shirinta.
Ya ce:
"Wannan shi ne gwajinmu. Zai nuna yadda muka shirya domin 2027. Zai zama atisayen da za mu yi kafin babban zaben kasa. Saboda haka dole ne APC ta yi nasara a Osun."

Source: Original
Jam'iyyar za ta yi yakin neman zabe gida-gida
Yilwatda ya ce APC za ta gudanar da yakin neman zabe ta hanyar ziyartar jama'a gida-gida da kuma tattaunawa kai tsaye da masu kada kuri'a domin neman goyon bayansu.
A cewarsa, gwamnoni daga dukkan shiyyoyin kasar nan, 'yan majalisun tarayya da na jihohi, shugabannin kananan hukumomi da kansiloli za su shiga wannan gangamin wayar da kan masu zabe.
Ya kuma bayyana cewa an tsara kwamitin ne ta yadda zai wakilci bangarori daban-daban na al'ummar Osun, tare da bai wa mata da sauran muhimman kungiyoyin masu kada kuri'a muhimmanci a yakin neman zaben.
An farmaki jigon APC a Osun
A wani labari, mun ruwaito cewa, wasu mahara da ake zargin 'yan daban siyasa ne sun harbi wani ’dan jam'iyyar APC, Taofeek Mustapha a jihar Osun.

Kara karanta wannan
"Ba kushe ba": Shugaban APC, Nentawe ya ba 'yan adawa shawara ana shirin zaben 2027
Rahotanni sun nuna cewa ana ci gaba da samun rigingimun siyasa gabanin zaben gwamnam jihar Osun da za a yi a watan Agusta, 2026.
Jigon APC da aka harba da bindiga, Taofeek Mustapha ya ce yana sanye da hular kamfen mai tambarin AMBO lokacin da aka kawo hari.
Asali: Legit.ng

