Atiku Ya Yi Alkawarin Warware Matsalar da Ta Fi Damun Yan Najeriya kan INEC da Tsarin Zabe

Atiku Ya Yi Alkawarin Warware Matsalar da Ta Fi Damun Yan Najeriya kan INEC da Tsarin Zabe

  • Atiku Abubakar ya yi alkawarin kawo karshen magudin zabe da karfafa ‘yancin INEC idan aka zabe shi shugaban kasa a 2027
  • Ya ce masu laifin zabe, ba tare da la’akari da jam’iyyarsu ba, za su fuskanci hukunci mai tsauri
  • Atiku ya bukaci masu kada kuri’a su kare kuri’unsu tare da neman tsare-tsaren manufofi masu gamsarwa daga ’yan takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin kawo karshen magudin zabe da karfafa ‘yancin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC).

Atiku ya sha alwashin gyara kura-kuran da ake yi a harkokin gudanar da zaben Najeriya da tabbatar da yancin INEC mai zaman kanta idan aka zabe shi shugaban kasa a 2027.

Atiku.
Dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar lokacin da ya karbi bakuncin Aisha Buhari Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a hedikwatar ADC da ke Abuja yayin jawabin ranad cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai.

Kara karanta wannan

An kama shugaban ƙungiyar magoya bayan Peter Obi da Kwankwaso

Atiku ya yi alkawarin gyara tsarin zabe

Wazirin Adamawa ya bayyana wasu muhimman sauye-sauyen zabe da zai aiwatar domin dawo da kwarin gwiwar masu kada kuri’a ga tsarin dimokuradiyya.

Atiku ya yi alkawarin tallafa wa fitar da sakamakon rumfunan zabe ga jama’a cikin gaggawa, tare da yin alkawarin cewa za a gurfanar da masu duk wanda aka kama da aikata laifin zabe a gwamnatinsa, ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasar da suke goyon baya ba.

Atiku ya ce:

“Duk wanda aka kama yana sayen kuri’u ko sauya sakamakon zabe zai fuskanci gurfanarwa a gaban kotu ba tare da duba jam'iyyarsa ba."

Dan takarar na ADC ya kuma jaddada cewa kuri’ar kowane dan Najeriya dole a kirga ta daidai yadda ya kada ta.

Atiku ya ja hankalin masu kada kuri'a

Da yake magana kan masu kada kuri’a gabanin babban zaben 2027, Atiku ya bukaci ’yan kasa su kare kuri’unsu, su tsaya tsayin daka kan duk wani yunkurin tsoratar da su, sannan su rika neman ’yan takara su yi bayani kan abin da suka yi alkawari.

Kara karanta wannan

Atiku ya buƙaci Tinubu ya saki El Rufai, Sheikh Zaria, ya taɓo batun Nnamdi Kanu

Ya shawarci masu kada kuri’a su nemi tsare-tsaren manufofi bayyanannu kuma masu iya auna sakamakonsu, maimakon alkawura marasa tushe da cikakken bayani.

“Zaben da ke tafe ya ba mu hanya ta lumana wajen zabar alkiblar da za mu bi. Wannan kasa taku ce," in ji Atiku.
INEC.
Tambarin hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Dan takarar shugaban kasar ya kara da cewa idan aka zabe shi, gwamnatinsa za ta mayar da kare lafiyar jama’a da saukaka rayuwa a matsayin ginshikan muhimmai na tafiyar da mulkin kasa.

Atiku ya kalubalanci gwamnatin Tinubu

Kun ji cewa Atiku Abubakar ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta yi wa yan najeriya bayanain yadda shirin tallafin N75,000 ya isa ga talakawa.

Atiku ya tambayi ko an ba wadanda suka amfana kudin ne da hannu ko kuma ta hannun cibiyoyin hada-hadar kudi, yana mai bukatar a gabatar da takardun da ke tabbatar da kowace hanya da aka bi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262