Garabasa: Za a Raba Wa Dalibai Kyautar Hannun Jarin Matatar Dangote, An Fadi Yadda Tsarin Yake
- Gidauniyar Aliko Dangote ta kaddamar da shirin da zai bai wa daliban Najeriya karin hannayen jari 10 kyauta bayan sun sayi akalla guda 10
- Shirin na bai wa daliban manyan makarantun gwamnati da masu zaman kansu damar shiga harkar zuba jari da mallakar kadarori
- Gidauniyar ta ce shirin na da nufin bunkasa ilimin harkokin kudi, zuba jari cikin alhaki da kuma samar da arziki na dogon lokaci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos, Nigeria - Gidauniyar Aliko Dangote ta kaddamar da Shirin Tallafin Hannayen Jari na matatar Dangote ga Dalibai a Najeriya.
Shirin zai bai wa daliban Najeriya masu shekaru 18 zuwa sama karin hannayen jari 10 na matatar Dangote kyauta, bayan sun sayi akalla hannayen jari 10.

Source: Facebook
Tribune Nigeria ta ruwaito cewa shirin zai shafi daliban manyan makarantun gwamnati da masu zaman kansu da aka amince da su a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan
Gwamnati ta ɓullo da wani shiri, za a daina ɗauke wuta a Kano da wasu wurare a Najeriya
Haka zalika, wannan shiri yana da nufin bunkasa ilimin harkokin kudi, zuba jari da kuma samar da arziki na dogon lokaci tsakanin matasan Najeriya.
Hakan dai na kunshe ne a wata sanarwa da Shugaban Gidauniyar Aliko Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya fitar ranar Alhamis da ta gabata.
Dalibai za su samu hannu jari kyauta
Ya ce shirin zai bai wa dalibai damar samun kwarewa kai tsaye kan zuba jari da mallakar hannun jarin kamfani ta hanyar shiga cikin tayin sayar da hannayen jari na farko ga jama’a (IPO) a matatar Dangote.
Dangote ya ce:
“Tallafa wa matasa ya wuce samar musu da damar samun ilimi. Haka kuma dole ne ya kunshi ba su ilimi da damar shiga cikin harkokin bunkasa tattalin arziki da samar da arziki.
"Ta wannan shiri, muna son dalibai su fahimci muhimmancin adanawa, zuba jari da mallaka na dogon lokaci. Burinmu shi ne mu taimaka musu su fara samun tunanin zuba jari tun suna kanana.”

Kara karanta wannan
Akwai alheri: An buɗe shirin da ake buƙatar matasa 'yan shekaru 15 zuwa 35 su cike a Najeriya
Ya ce fara bai wa matasa damar fahimtar zuba jari tun da wuri na iya taimakawa wajen tsara yadda za su yanke shawarar kudi a nan gaba da kuma karfafa shiga cikin harkokin tattalin arziki na yau da kullum.
Ya kara da cewa,
“Idan matasa suka fahimci mallakar kadarori da zuba jari tun da wuri, za su fi samun damar yanke shawarar kudi bisa fahimta, gina arziki da kuma taka rawa sosai wajen bunkasar tattalin arziki.”
Yadda tsarin kyautar yake
A karkashin shirin, daliban da suka cancanta kuma suka kammala aikin tantancewa da ake bukata, sannan suka sayi akalla hannayen jari 10, za su cancanci Gidauniyar ta dauki nauyin sayen karin hannayen jari 10 da sunayensu ba tare da wani karin kudi ba.

Source: Facebook
Dole ne dalibai su kammala aikin tantancewa ta dandalin Gidauniyar da aka ware kafin a tura su sashen sayen hannayen jari, inda za su iya neman akalla hannayen jari 10 na matatar mai da sunayensu.
Gidauniyar ta ce ba za a iya amfani da shirin wajen sayen hannayen jari a madadin wani mutum, wani kamfanin Dangote ko kuma wani kamfani daban ba.
ACF ta fara taron wayar da kan jama'a

Kara karanta wannan
Shirin Bola Tinubu na tsaka mai wuya da APM ta aika saƙo na musamman Bankin Duniya
Kun ji cewa Ƙungiyar Arewa ta ACF ta ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a a Jihar Kano game da sayen hannun jarin Matatar Dangote.
Matakin da ACF ta ɗauka na wayar da kai an yi shi ne domin tabbatar da cewa ’yan Arewa sun samu isasshen bayani kan IPO ɗin, ta yadda za su iya yanke shawarar zuba jari.
Asali: Legit.ng