An Gano Abin da Manyan NDC na Arewa maso Yamma Su ka Tattauna a Abuja

An Gano Abin da Manyan NDC na Arewa maso Yamma Su ka Tattauna a Abuja

  • Shugabannin NDC na jihohin Arewa maso Yamma sun gana da jagoran jam'iyyar na kasa domin duba a gabar da siyasa ke kara zafi a Najeriya
  • Shugaban NDC na Kano ya ce jam'iyyar na samun karbuwa da ci gaba a jihohin shiyyar sakamakon fadada tsarinta.
  • Haka kuma tawkaransa na jihar Zamfara ya bukaci al'ummar jihar su mara wa Sanata Kabir Garba Marafa baya a zaben gwamnan 2027 mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugabannin jam'iyyar NDC na jihohin Arewa maso Yamma sun gudanar da zama da jagoran jam'iyyar na Kasa, Sanata Henry Seriake Dickson, domin tattauna hanyoyin karfafa ta a fadin shiyyar.

Taron ya hada shugabannin jam'iyyar daga jihohin Kano, Jigawa, Katsina, Kaduna, Kebbi, Sakkwato da Zamfara, inda suka yi nazari kan yadda jam'iyyar ke tafiya tare da duba dabarun kara fadada tasirinta.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya gana da na hannun daman Kwankwaso, Sanata Kabiru Gaya

Manyan NDC sun gana a Abuja
Shugabbanin NDC tare da Dikson a Abuja Hoto: Galadiman Gora
Source: Facebook

Wannan na kunshe a cikin sanarwar da Alhaji Surajo Garba Mai Katako, shugaban jam’iyyar NDC reshen Jihar Zamfara kuma Galadiman Gora ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Abin NDC ta tattauna a Abuja

Shugaban NDC na Jihar Kano, Hon. Husaini Isah Mai Riga, wanda kuma shi ne shugaban jam'iyyar a shiyyar Arewa maso Yamma, ya ce jam'iyyar na ci gaba da samun ci gaba mai yawa a jihohin yankin.

A cewarsa, karbuwar da jam'iyyar ke samu na da alaka da yadda ake fadada tsarinta da kuma abin da ya bayyana a matsayin shugabanci mai kishin jama'a.

Hon. Mai Riga ya kuma tabbatar da cewa shugabannin NDC na shiyyar za su ci gaba da hada kai, karfafa zumunci da fahimtar juna domin gina jam'iyya mai karfi wadda za ta fafata a zabukan da ke tafe.

NDC ta ce ta zage damtse don samun nasarar 2027
Jagoran NDC na kasa, Seriake Dickson Hoto: Henry Seriake Dickson
Source: Facebook

A karin bayanin da ya yi wa Legit, mai magana da yawun Mai Riga, Adam Said Adam ya ce:

Kara karanta wannan

Ricikin bayan zaben fitar da gwan ya raba kan APC a jihar Niger

"shugabannin NDC na Arewa maso Yamma sun tabbatar wa Shugaban Jam'iyyar na Ƙasa da Sakataren Jam'iyyar na Ƙasa cewa jam'iyyar NDC na ci gaba da samun karɓuwa tare da ƙara faɗaɗa tasirinta a dukkan jihohin shiyyar."
"Shugabannin sun kuma jaddada aniyarsu ta ci gaba da ƙarfafa haɗin kai, inganta tsarin jam'iyyar, da kuma aiki tare domin tabbatar da nasarar jam'iyyar NDC a zaɓuɓɓuka masu zuwa."

Bukatar NDC a Zamfara

Shi ma Shugaban NDC na Jihar Zamfara, Alhaji Surajo Garba Mai Katako, ya shaida wa jagoran jam'iyyar cewa reshen jihar ya shirya tsaf domin tabbatar da nasarar NDC a babban zaben shekarar 2027.

Ya ce fitowar Sanata Kabir Garba Marafa a matsayin dan takarar gwamnan jam'iyyar ta kara wa NDC karfi a jihar, yana mai cewa dan takarar ya na da gogewa da fahimtar siyasar Zamfara tare da tarihin hidimtawa al'umma.

A cewarsa, hakan ne ya sa yake ci gaba da samun goyon bayan fitattun 'yan siyasa da magoya baya daga jam'iyyu daban-daban tare da neman a mara masa baya.

'Dan takarar NDC ya yi magana

A wani labarin, mun wallafa cewa Peter Obi mai neman mulkin Najeriya ya bayyana cewa ya na da yakinin zai yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, inda zai kara da manyan 'yan adawa da Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

APC da PDP sun fara saka bayanan 'yan takarar gwamna a shafin INEC

Ɗan takarar shugaban kasar na jam'iyyar NDC ya ce zaɓen ba ya tsakaninsa da gwamnati, sai dai tsakanin al’umma da gwamnatin Najeriya musamman halin da ake ganin sun fada na wahalhalun rayuwa.

Tsohon gwamnan na Anambra ya ce shi wani makami ne kawai da ‘yan Najeriya ke amfani da shi wajen neman sauyi domin su samu ingantacciyar rayuwa da raguwar talauci da matsalolin rashin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng