Babbar Magana: An Gano Jami'ar Bogi da Ta Tara Dalibai a Najeriya
- Hukumar NSCDC ta gano wata jami'ar bogi da ke aiki a cikin wani gida mai dakuna uku a jihar Legas tare da ceto matasa 106
- Jami'an tsaron sun kama wanda ake zargi da kafa cibiyar bayan an shafe kwanaki suna tattara bayanan sirri da sa ido
- Bincike ya nuna cewa an karɓi kuɗaɗen shiga makaranta da ya kai miliyoyin naira tare da amfani da tsarin da ya yi kama da na damfara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Legas – Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC), reshen Badagry, ta gano wata jami'ar bogi da ake zargin tana aiki daga wani gida mai dakuna uku a yankin Ilado da ke karamar hukumar Olorunda LCDA a jihar Legas.
Hukumar ta ce ta ceto matasa 106 da ake zargin an yaudare su da alkawarin samun gurbin karatu a wata jami'a ta ƙasashen waje.

Source: Facebook
Punch ta rahoto cewa jami'an NSCDC sun kuma kama wanda ake zargi da mallakar cibiyar, wanda ake zargin ya jawo matasa daga sassa daban-daban na Najeriya da wasu ƙasashen Yammacin Afirka.
Yadda aka gano jami'ar bogi
Kwamandan NSCDC na yankin Badagry, Gbenga Ekunola, ya ce an gudanar da samamen ne da safiyar ranar Litinin bayan kwanaki ana tattara bayanan sirri da kuma sa ido kan wurin.
A cewarsa, cibiyar ba ta da suna na hukuma, ba ta da rajista, kuma ba ta da harabar jami'a, sai dai tana gabatar da kanta a yanar gizo a matsayin cibiyar koyarwa daga nesa mai alaƙa da wata jami'ar ƙasashen waje.
The Cable ta rahoto ya ce:
"Mun samu sahihan bayanan sirri game da abubuwan da ke faruwa a wurin. Jami'anmu sun shafe kwanaki suna sa ido kafin su kai samame."
An karɓi miliyoyi daga ɗalibai
Binciken farko ya nuna cewa mafi yawan waɗanda aka ceto na tsakanin shekaru 19 zuwa 24 ne, kuma sun fito daga jihohin Kogi, Oyo da wasu jihohin Arewa.
Rahoton ya ƙara da cewa wasu sun fito daga ƙasashen Nijar, Kamaru da Togo bayan an yaudare su ta yanar gizo.
NSCDC ta ce waɗanda abin ya shafa sun biya kuɗin neman gurbin karatu da sauran kuɗin gudanarwa da suka kama daga N200,000 zuwa N1.5m, yayin da wasu 'yan ƙasashen waje suka biya tsakanin Dala 400 zuwa 500.
Tsarin ya yi kama da damfara
Binciken ya kuma gano cewa an tilasta wa waɗanda suka shiga shirin su nemo sababbin mutane domin su samu lada.
Masu bincike sun bayyana cewa tsarin ya yi kama da damfara, inda ake yi wa mahalarta alƙawarin samun ƙarin kuɗi idan suka jawo sababbin ɗalibai.
Ekunola ya ce wasu iyaye ma ba su san ainihin abin da 'ya'yansu ke yi a Badagry ba, domin wasu sun shaida musu cewa sun je koyon sana'a ne ba karatu ba.

Source: Original
An gano gawa a Uni Jos
A wani labarin, mun ruwaito cewa fargaba ta mamaye Jami'ar Jos (UNIJOS) bayan an gano gawar wani mutum ba tare da kai ba a wata gona da ke cikin harabar makarantar.
Rahotanni sun ce mamacin ba ɗalibi ba ne kuma ba ma'aikacin jami'ar ba ne, sai dai binciken farko ya nuna cewa manomi ne da aka saba gani yana noma a yankin.
Legit Hausa ta wallafa cewa jami'an tsaro sun fara bincike domin gano musabbabin mutuwar mutumin da kuma waɗanda ke da hannu a lamarin.
Asali: Legit.ng


