Yadda Ƴan Takarar Mataimakan Shugaban Kasa Za Su Lalubo Kuri'u ga Tinubu, Atiku da Obi

Yadda Ƴan Takarar Mataimakan Shugaban Kasa Za Su Lalubo Kuri'u ga Tinubu, Atiku da Obi

  • Manyan jam'iyyu uku sun bayyana 'yan takarar mataimakan shugaban kasa, lamarin da ya mayar da hankali kan tasirinsu
  • APC ta ci gaba da Kashim Shettima, ADC ta zabi Rotimi Amaechi, yayin da NDC ta hada Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso domin neman karin kuri'u
  • Masana sun ce mataimakan takara na iya kara karfin yakin neman zabe, amma tattalin arziki, tsaro, tsarin jam'iyya da fitowar masu kada kuri'a ne za su fi yanke hukunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Yayin da Hukumar INEC ta rufe karɓar sunayen 'yan takara, hankalin 'yan siyasa ya koma kan rawar da mataimakan 'yan takarar shugaban kasa za su taka a zaben 2027.

Shugaba Bola Tinubu zai sake takara tare da mataimakinsa Kashim Shettima a karkashin APC.

Kara karanta wannan

'Dan Afrika zai fafata da turawa 5 a zaben shugaban Majalisar Dinkin Duniya

Kallo ya koma kan ƴan takarar mataimakan shugaban kasa a Najeriya
Rabi'u Kwankwaso, Rotimi Amaechi da Kashim Shettima. Hoto: Kashim Shettima, Rabi'u Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Wadanda aka zaba yan takarar mataimakan shugaban kasa

A bangaren ADC, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya zabi tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi, a matsayin abokin takararsa, cewar Leadership.

Haka kuma dan takarar NDC Peter Obi ya zabi tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin mataimakinsa.

Fitowar wadannan tikiti uku ta jawo tattaunawa kan irin gogewa, tasirin yanki da kuma goyon bayan jama'a da kowanne mataimakin dan takara zai kawo wa yakin neman zaben jam'iyyarsa.

Babban aikin da ke gaban Kashim Shettima

Kashim Shettima ya ci gaba da kasancewa mataimakin Tinubu bayan ya yi wannan aiki tun shekarar 2023.

Tsohon gwamnan Borno ne kuma tsohon sanatan Borno ta Tsakiya, wanda ake sa ran zai taimaka wajen karfafa APC a Arewa maso Gabas.

Ana kallon Arewa maso Gabas a matsayin muhimmin yanki saboda Atiku, wanda ya fito daga yankin, na kokarin karfafa tasirinsa.

Kara karanta wannan

ADC: Ashiru Kudan ya zabi abokin takarar gwamna domin doke Uba Sani a Kaduna

Duk da haka, ya ce dole mataimakin shugaban kasar ya kara kokari domin tinkarar tasirin Atiku a Arewa maso Gabas.

A zaben 2023, Atiku ya lashe Adamawa, Bauchi, Gombe, Taraba da Yobe, yayin da Tinubu ya yi nasara a Borno kawai, cewar Punch.

Wasu masu sharhi sun ce ci gaba da Shettima a matsayin mataimakin Tinubu zai rage cece-kuce cikin APC, sun ce sauya shi da wani dan takara Kirista na iya haddasa karn rikici a jam'iyyar.

Tinubu ya ɗauki Shettima a matsayin mataimaki
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da mai gidansa, Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Tasirin da Amaechi ke da shi a yankinsa

Masu lura da al'amura sun ce zaben Amaechi na iya karfafa ADC a Kudu maso Kudu tare da fadada tasirinta zuwa Kudu maso Gabas.

Tsohon kakakin majalisar Rivers ne, gwamna sau biyu, kuma tsohon ministan sufuri, ya kasance cikin manyan masu neman tikitin shugaban kasa na APC kafin zaben 2023, inda Tinubu ya doke shi.

Duk da Tinubu ya lashe Rivers a 2023, Peter Obi ya mamaye yawancin jihohin Kudu maso Gabas.

Amaechi ya zama mataimakin Atiku
Rotimi Amaechi da ɗan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar. Hoto: ADC Nigeria.
Source: Facebook

Hasashen da ake kan tasirin Kwankwaso

A bangaren NDC kuwa, ana ganin zaben Rabiu Kwankwaso zai kara wa jam'iyyar karfi a Arewacin Najeriya, musamman Kano da wasu jihohin Arewa maso Yamma saboda tasirin tafiyar Kwankwasiyya.

Kara karanta wannan

Masoyan Tinubu sun mayar wa Kwankwaso martani kan tikitin Musulmi Musulmi

Kwankwaso ya lashe Kano a zaben shugaban kasa na 2023 karkashin NNPP, inda ya kayar da APC, PDP da LP da gagarumin rinjaye, ya samu kusan kashi 58.4 cikin 100 na kuri'un jihar.

Sai dai wasu na ganin tasirin Kwankwaso ya fuskanci kalubale bayan sabanin da ya shiga da tsohon amintaccensa, Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda daga baya ya koma APC.

Ana ganin cewa Kwankwaso na da farin jini a tsakanin matasan Arewa da Musulmai, wanda hakan ka iya fadada karbuwar Obi a yankin kafin zaben shugaban kasa na 2027.

Peter Obi ya zaɓi Kwankwaso a matsayin mataimaki
Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi da mataimakinsa, Rabi'u Kwankwaso. Hoto: Mr. Peter Obi.
Source: Facebook

Hasashen da masana siyasa ke yi

Masanin siyasa Suleiman Hassan Gimba ya ce ba a lashe zaben shugaban kasa saboda sunayen 'yan takara kadai ba.

Ya ce tattalin arziki, tsaro, tsarin yakin neman zabe da fitowar masu kada kuri'a su ma suna da muhimmanci.

Gimba ya bayyana cewa Kwankwaso na da karfin tafiyar jama'a mai zaman kanta, Shettima na da gogewar shugabanci a Arewa maso Gabas, yayin da Amaechi ke da kwarewar siyasa da mulki.

Malamin kimiyyar siyasa na Jami'ar Nnamdi Azikiwe, Dakta Christian Okeke, ya ce Kwankwaso ne ke da mafi karfin magoya bayan kasa kai tsaye saboda tasirin tafiyar Kwankwasiyya.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya hango abin da zai hana Tinubu cin zaɓe, ya ba shi mafita

Masoyan Tinunu sun dura kan Kwankwaso

An ji cewa magoya bayan Bola Ahmed Tinubu sun yi mamakin kalaman Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso game da tikitin takarar shugaban kasa da mataimakinsa a 2027.

Kwankwaso dai ya ce Tinubu bai yi wa kansa dabara ba da ya sake dauko Kashim Shettima, musamman bayan zazzafar muhawara da ake bugawa kan batun.

Amma masoya Tinubu sun bayyana cewa illar da Kwankwaso ya ce ya hango ba wani abu ba ne, kuma tikitin ba zai samu wata matsala a zabe mai zuwa ba.

Wanda ya tantance Abdullahi Abubakar, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.