ADC: Ashiru Kudan Ya Zabi Abokin Takarar Gwamna domin Doke Uba Sani a Kaduna

ADC: Ashiru Kudan Ya Zabi Abokin Takarar Gwamna domin Doke Uba Sani a Kaduna

  • Dan takarar gwamnan jihar Kaduna na jam'iyyar ADC, Isa Ashiru, ya sanar da Barrista Irmiya Ishaku Kantiok a matsayin mataimakinsa a zaben 2027
  • Ashiru ya bayyana Kantiok a matsayin gogaggen lauya kuma tsohon dan majalisar jihar Kaduna da zai taimaka wajen cika burin jam'iyyar
  • Dan takarar ya ce tikitin nasu zai mayar da hankali kan hada kan al'ummar Kaduna, inganta shugabanci da bunkasa ci gaba a dukkan yankunan jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kaduna – Dan takarar gwamnan jihar Kaduna na jam'iyyar ADC, Isa Ashiru Kudan, ya sanar da Barrista Irmiya Ishaku Kantiok a matsayin wanda zai yi takarar mataimakin gwamna tare da shi a zaben 2027.

Isa Ashiru ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, inda ya ce zaben Kantiok ya biyo bayan la'akari da kwarewarsa a fannin shari'a da kuma gogewarsa a harkokin majalisa.

Kara karanta wannan

Yadda dan takarar gwamna ya kawo ƙarshen rikicin shugabancin ADC a Kaduna

Isa Ashiru Kudan da Irmiya Ishaku
Isa Ashiru Kudan a hagu da Irmiya Ishaku a dama. Hoto: Isa Ashiru Kudan
Source: Facebook

Bayanin da Ashiru Kudan ya wallafa a Facebook ya nuna cewa Kantiok ya wakilci mazabar Zonkwa a majalisar dokokin jihar Kaduna ya yi wa'adi uku a jere.

Dalilin zaben Irmiya Kantiok

Da yake bayyana dalilin zaben nasa, Isa Ashiru ya ce Kantiok mutum ne mai ilimi, nagarta da jajircewa, wanda ya dace da irin shugabancin da jihar Kaduna ke bukata a wannan lokaci.

Ya ce:

"Yau ina cikin farin ciki na sanar da Barrista Irmiya Ishaku Kantiok a matsayin mataimakina a takarar gwamnan jihar Kaduna karkashin babbar jam'iyyarmu ta ADC."

Ashiru ya kara da cewa Kantiok gogaggen lauya ne wanda ya yi fice wajen kare gaskiya da adalci, tare da nuna kwarewa a lokacin da yake aiki a majalisar dokokin jihar.

Tikitin Ashiru-Kantiok ya yi alkawari

Dan takarar gwamnan ya ce tikitin da suka kafa zai yi aiki domin hada kan al'ummar Kaduna, karfafa hukumomi da kuma samar da ci gaba mai dorewa a dukkan yankunan jihar.

Kara karanta wannan

Majalisar Kano ta matsa kan binciken yadda ake kashe N25m na tsaro bayan hare hare

A cewarsa, za su tabbatar da bin doka da oda, samar da damammaki ga matasa, fadada ayyukan more rayuwa da kuma inganta walwalar jama'a.

Punch ta wallafa cewa ya ce:

"Tare za mu gina Kaduna cikin hadin kai, inda doka za ta yi aiki, matasa za su samu damammaki, ayyukan raya kasa za su bunkasa, kuma kowane yanki zai samu ci gaba."

Ashiru ya bayyana tikitin nasu a matsayin wanda ya kunshi gogewa, kwarewa da hangen nesa domin samar da sabuwar Kaduna.

Dan takarar ADC a Kaduna
Ashiru Kudan da ke yi wa ADC takarar gwamna a Kaduna. Hoto: Isah Ashiru Kudan
Source: Facebook

Kudan ya nemi goyon baya

Isa Ashiru ya yi kira ga al'ummar jihar Kaduna da magoya bayan jam'iyyar ADC su mara wa tikitin nasu baya kafin zaben gwamna na shekarar 2027.

Ya ce jam'iyyar ta shirya kawo shugabanci nagari, ci gaba mai dorewa da kuma gwamnatin da za ta rungumi kowa ba tare da nuna bambanci ba.

Ashiru ya bayyana kwarin gwiwar cewa idan aka ba su dama, za su cika alkawuran da suka dauka tare da kawo sabon salo na shugabanci a jihar Kaduna.

Malami ya zabi abokin takara

A wani labarin, mun ruwaito cewa dan takarar gwamnan jihar Kebbi na jam'iyyar ADC, Abubakar Malami, ya zabi Musa Zagi a matsayin mataimakinsa a zaben gwamna na 2027.

Kara karanta wannan

Sokoto: Dan majalisar tarayya ya zama dan takarar mataimakin gwamna a ADC

Jam'iyyar ta bayyana cewa matakin ya samu amincewar dan takarar gwamna, tare da taya Musa Zagi da sauran 'yan takarar jam'iyyar murna.

A wani bayani da ta yi, ADC ta yi magana tana mai kira ga mambobinta su ci gaba da kasancewa cikin hadin kai kafin babban zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng