Wata Mata Ta Fito Fili Ta Bayyana Cewa Tana Taimaka wa Yan Ta'adda a Arewacin Najeriya

Wata Mata Ta Fito Fili Ta Bayyana Cewa Tana Taimaka wa Yan Ta'adda a Arewacin Najeriya

  • Wata mata mai suna, Sumaiya Abubakar ta amsa laifin taimaka wa ’yan ta'addan ISWAP ta hanyar ajiye musu makamai da alburusai a jihar Nasarawa
  • An gurfanar da matar ne a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan tuhume-tuhume biyu da suka shafi ta’addanci
  • Kotu ta dage sauraron karar zuwa 14 ga Oktoba, yayin da aka bayar da umarnin ci gaba da tsare ta a hannun DSS

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja Nigeria - Wata mata, Sumaiya Abubakar ta amsa laifin taimaka wa ’yan kungiyar ta'addanci ta ISWAP ta hanyar ajiye musu makamai da alburusai a jihar Nasarawa.

Sumaiya ta amsa laifin ne ranar Talata a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, bayan gwamnatin tarayya ta gurfanar da ita kan tuhume-tuhume biyu da suka shafi ta’addanci.

Kara karanta wannan

Duk da matsalar da ake ciki da Wike, APC ta bayyana shirin da ta yi saboda Tinubu

Kotu.
Gudumar da ake amfani da ita a wurin shari'a a kotunan Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An tuhumi Sumaiya da ta’addanci

Leadership ta ruwaito cewa a daraktan sashen gabatar da kara na tarayya, Rotimi Oyedepo SAN ne ya jagoranci shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CR/418/2026.

Lauyan gwamnati ya zargi Sumaiya Abubakar da aikata laifin a shekarar 2024 a yankin Shinge da ke ƙaramar hukumar Lafia ta jihar Nasarawa.

Masu gabatar da ƙara sun yi zargin cewa matar, wadda ta fito daga ƙauyen Shuwari da ke ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar Borno, ta ba da taimako ga ’yan ISWAP da gangan ta hanyar taimaka musu wajen ajiye makamai da alburusai.

An ce laifin ya saɓa wa doka kuma yana da hukuncin da aka tanada a ƙarƙashin Sashe na 13 na Dokar Hanaws da Dakatar da Ta’addanci ta shekarar 2022.

Ta amsa 1 daga cikin tuhume-tuhumen

Lokacin da aka karanta mata tuhume-tuhumen, Sumaiya Abubakar ta musanta laifin da ke cikin tuhuma ta farko, amma ta amsa laifin da ke cikin tuhuma ta biyu.

Kara karanta wannan

NSCIA: An faɗaɗa majalisar kula da harkokin addinin musulunci ta Najeriya

Lauyan masu gabatar da ƙara, M.A. Oladunjoye, daga bisani ya roƙi kotun da ta yanke mata hukunci kan tuhumar da ta amsa, tare da neman janye tuhuma ta farko.

Lauyan wacce ake zargi, Itodo, bai yi adawa da buƙatar ba, lamarin da ya sa Mai Shari’a Salim Ibrahim ya soke tuhuma ta farko.

Sai dai alkali ya ce masu gabatar da ƙara na buƙatar sake duba bayanan shari’ar kafin kotu ta yanke hukunci kan tuhuma ta biyu da wacce ake zargi ta amsa.

Nasarawa.
Taswirar jihar Nasarawa da ke Arewa ta Taskiya a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Alkali ya dage sauraron karar

Mai Shari’a Ibrahim ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 14 ga Oktoba domin a sake duba bayanan shari’ar.

Ya kuma bayar da umarnin ci gaba da tsare Sumaiya Abubakar a hannun Hukumar Tsaro ta Ƙasa (DSS) har zuwa ranar da za a ci gaba da sauraron karar.

Kotu ta kama masu garkuwa a Edo

Kun ji cewa Wata Babbar Kotu ta Musamman ta Jihar Edo ta gamsu da hujjojin da aka gabatar mata, ta kama wasu mutum hudu da hannu a garkuwa da mutane.

Sakamakom haka, babbar kotun ta yanke wa mutanen huɗu da aka samu da laifi hukuncin kisa ta hanyar rataya ranar Talata, 29 ga watan Satumba, 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262