Kurunƙus: Tinubu Ya Mika Fam ga APC, Ya Zabi Wanda Zai Masa Mataimaki a Zaben 2027

Kurunƙus: Tinubu Ya Mika Fam ga APC, Ya Zabi Wanda Zai Masa Mataimaki a Zaben 2027

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kawo karshen duk wata jita-jita da jama'a ke yaɗa wa kan wanda zai dauka a matsayin abokin takara a zaben 2027
  • Rahotanni sun nuna cewa APC ta karbi takardun tsayawa takarar Tinubu da Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa
  • Gwamnan Imo, Hope Uzodinma da Abba Kabir Yusufa na Kano na cikin gwamnonin d suka halarci taron da APC ta shirya a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya dauki Sanata Kashim Shettima a matsayin wanda zai yi masa takarar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar APC.

Wannan mataki na nufin Shugaba Tinubu da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima za su nemi tazarcen kujerunsu a zaben 2027.

Tinubu Shettima.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wurin taro Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

DW Hausa ta tabbatar da hakan a wani rahoto da ta wallafa a shafinta na Facebook yau Juma'a, 10 ga watan Yuli, 2026.

Kara karanta wannan

Albarkacin Shettima, matasan Arewa sun yi wa Tinubu alkawarin ruwan kuri'u a 2027

A cikin watannin baya, an yi ta hasashen cewa matsayin Shettima na fuskantar barazana, musamman bayan wasu jiga-jigan APC, har da wasu daga yankin Arewa maso Gabas, ba su fito fili sun bayyana goyon bayansu gare shi ba.

Har ila yau, masu neman sauyin mataimakin shugaban kasa sun rika cewa Tinubu na iya maye gurbin Shettima da wani dan Arewa Kirista domin tikitin zaben 2027.

Tinubu ya mika sunan Shettima ga APC

Sai dai a ranar Juma'a, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Masari, ya mika takardun tsayawa takarar Tinubu ga shugabannin APC a taron da ya gudana a otal din Continental da ke Abuja.

A takardun, Shugaba Tinubu ya sanya sunan Sanata Kashim Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC a zaben 2027.

Mika takardun ya tabbatar da matakin da Tinubu ya dauka na ci gaba da tafiya tare da Shettima a matsayin mataimakinsa a babban zaben shekarar 2027, cewar rahoton Daily Trust.

Taron APC.
Babban mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin siyasa, Ibrahim Masari yana mika fam ga shugabannin APC Hoto: Prof. Nentawe Yilwatda
Source: Facebook

Gwamnoni sun halarci taron APC

Taron ya samu halartr gwamnoni da suka hada da Hope Uzodimma na Imo, Mai Mala Buni na Yobe, Abba Kabir Yusuf na Kano, Nasir Idris na Kebbi, Uba Sani na Kaduna, Ahmadu Fintiri na Adamawa da Babagana Zulum na Borno.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kwantar wa 'yan Najeriya hankali, ya yi alkawarin romon dimukradiyya

Gwamnan jihar Imo kuma shugaban kungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodimma, ne ya jagoranci gwamnonin jam'iyyar zuwa wajen taron.

Mambobin Kwamitin Gudanarwa na APC (NWC), 'yan majalisar dokoki ta kasa, mambobin majalisar zartarwa ta tarayya (FEC), da sauran manyan shugabanni da masu ruwa da tsaki na APC sun halarci taron.

APC ta hango nasarar Tinubu a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta bayyana cewa manyan ayyukan ci gaba da gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa su na yi wa jama'a dadi.

Jam'iyyar ta ce tana da yakinin wadannan ayyuka za su taimaka masa samun gagarumar nasara a babban zaben shekarar 2027.

APC ta ce ayyukan raya kasa da gwamnatin tarayya ke gudanarwa a sassan Arewa cin Najeriya sun nuna kudurin gwamnatin Tinubu na bunkasa yankin, kuma sun karyata zargin cewa an yi watsi da Arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262