2027: Ganduje Ya Yi wa Obi da Kwankwaso Mummunan Hasashe, Ya Hango Faduwarsu a Kano
- Tsohon gwamnan Kano ya yi magana game da nasarar Peter Obi da Rabi'u Musa kwankwaso a jihar yayin da zaɓe ke kusantowa
- Ganduje, wanda tsohon shugaban APC ne a matakin kasa ya yi watsi da fariyar da Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi na cewa sun ci zaɓe a Kano
- Tsohon shugaban ya soki mulkin Obi da Kwankwaso a jihohinsu, inda ya ce ba su yi abin a zo a gani ba har zai da a zabe su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa tikitin takarar shugaban ƙasa da mataimakinsa na jam'iyyar NDC, wato Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba zai samu karɓuwa a jihar Kano ba a zaɓen shekarar 2027.
Ganduje, wanda tsohon gwamnan Kano ne, ya faɗi hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai ranar Talata 21 ga watan Yuli, 2026 awanni kadan bayan hira da aka yi da Kwankwaso.

Source: Twitter
The Cable ta ruwaito cewa Dr. Adullahi Umar Ganduje na ganin tikitin bai da ƙarfi ta fuskar siyasa da zai sa jama'ar jihar Kano su zaɓe su.
Ganduje ya yi watsi da tikitin Obi, Kwankwaso
A hira da ya yi da Channels TV, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Peter Obi ba su da tarihin shugabanci da zai sa al'ummar Kano su ba shi goyon baya.
Ya ce:
"Ban yi tunanin tikitin Peter Obi da Kwankwaso zai yi nasara a Kano ba. Ba zai yi nasara ba. Hasali ma, ya mutu tun kafin fara takara."
Ganduje ya kara da cewa: "Peter Obi ya taba zama gwamnan Anambra. Me ya yi a lokacin mulkinsa? Me ya bari?"
Ganduje ya daura kan Peter
Ya ƙara da cewa bai ga wani muhimmin matsayi da Obi ya riƙe bayan gwamna wanda ya nuna yana da ƙwarewar jagorantar Najeriya yadda ya kamata ba.
Da yake magana kan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Ganduje ya ce tsohon gwamnan Kano bai samu damar yin wa'adi biyu a jere ba, sabanin wasu gwamnoni da suka biyo baya.

Source: Twitter
Ya bayyana cewa Malam Ibrahim Shekarau ya yi shekara takwas a jere a matsayin gwamna, haka shi ma ya yi shekara takwas ba tare da katsewa ba.
A cewarsa, Kwankwaso ya rasa wa'adi na biyu bayan zangon farko, kafin daga bisani ya sake dawowa bayan shekaru takwas.
Ganduje ya ce wannan ya nuna cewa Kwankwaso bai bar irin tarihin shugabanci da zai sa jama'ar Kano ko 'yan Najeriya su yarda zai iya zama mataimakin shugaban ƙasa mai nasara ba.
Ya ce:
"Wane irin tarihi Kwankwaso ya bari a Kano da zai gamsar da mutanen Kano da ma 'yan Najeriya cewa zai iya zama mataimakin shugaban ƙasa mai nasara?"
APC za ta zaaro na kusa da Kwankwaso
A baya, mun kawo labarin cewa tsohon gwamnan Kano, Sanata Kabiru Gaya, ya amince da cewa zai koma jam'iyya mai mulkin Najeriya, wato APC bayan ganawa ta sirri da manyan ta a Abuja.
Rahotanni sun ce matakin ya biyo bayan rashin samun tikitin Sanatan Kano ta Kudu na jam'iyyar NDC duk da sauya shekarsa zuwa jam'iyyar gabanin zaben 2027, inda ya bi Rabiu Musa Kwankwaso.
Kabiru Gaya wanda ya taba mulkin Kano tsakanin 1992 da 1993, sannan ya wakilci Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa kafin ya rasa zaben 2023 ga Kawu Sumaila ya shiga wadanda APC ke nema.
Asali: Legit.ng


