Kwankwaso Ya Hango Abin da zai Hana Tinubu Cin Zaɓe, Ya Ba Shi Mafita

Kwankwaso Ya Hango Abin da zai Hana Tinubu Cin Zaɓe, Ya Ba Shi Mafita

  • Rabi'u Musa Kwankwaso ya shaida wa shugaba Bola Tinubu da sauran yan Najeriya babban kalubalen da ke tunkaro tikitin takarar APC a 2027
  • Sanata Kwankwaso, wanda ke neman kujerar mataimakin shugaban kasa a NDC ya bayyana cewa tikitin Musulm-Musulm zai yi wa Tinubu cikas a zabe mai zuwa
  • Ya bayyana mamakinsa kan yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tsayar da Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa, amma ya ce akwai mafita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC a zaɓen 2027, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce akwai kalubale ga takarar Bola Tinubu.

Ya bayyana cewa tikitin Musulmi-Musulmi na Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai ci gaba da kasancewa babban kalubale a zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan

'Ko makiyana sun san ni ke da Kano,' Kwankwaso ya yi martani ga Ali Modu Sheriff

Kwankwaso ya ce Tinubu zai fuskanci gagarumar matsala a zaben 2027
Shugaan kasa Bola Tinubu, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso Hoto: Bayo Onanuga/Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Twitter

Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin wata hira da ya yi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels a ranar Litinin 20 ga watan Yuli, 2026.

Bola Tinubu ya ba Kwankwaso mamaki

Jaridar Punch ta kawo labarin cewa tsohon gwamnan jihar Kano ya ce ya yi mamakin yadda Shugaba Tinubu ya sake tsayar da Kashim Shettima takara duk muhawarar da ta biyo bayan wannan tsari a 2023.

A cewarsa:

"Abin ma ya ba ni mamaki cewa shugaban ƙasa ya sake gabatar da irin wannan tikiti. Na san shi mutum ne da yake son daidaito."
Kwankwaso ya yi mamaki da aka a Kashim takara
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Ya ƙara da cewa:

"Idan ka duba Legas, a koyaushe yana ƙoƙarin daidaitawa. Ko a gidansa akwai daidaito. Ban san dalilin da ya sa ba a samu wannan daidaito a Najeriya ba. Amma har yanzu yana da lokaci kafin wa'adin sauya sunayen 'yan takara ya cika domin ya gabatar da tikitin da ya fi daidaito."

Kara karanta wannan

'Ka hakura da neman takara a 2027': Atiku ya sake shawartar Shugaba Tinubu

Sanata Kwankwaso ya koda Peter Obi

Kwankwaso, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin NNPP a 2023, yanzu shi ne mataimakin Peter Obi a ƙarƙashin jam'iyyar NDC.

Ya ce lokaci ya ba shi damar fahimtar halayen Obi sosai. A cewarsa:

"Yanzu na san Peter ɗan siyasa ne mai matuƙar muhimmanci. Yana kishin ƙasar nan kuma mutum ne da za a iya dogaro da shi."

Kwankwaso ya ce shi da Obi suna da ra'ayi iri ɗaya kan yadda za a ceto Najeriya daga matsalolin tsaro, tattalin arziki, lalacewar ababen more rayuwa da kuma bunƙasa ilimi.

Ya yi watsi da ra'ayin cewa Obi ba shi da farin jini a Arewacin Najeriya, yana mai cewa ɗan takarar shugaban ƙasan na NDC yana da gagarumin karɓuwa a yankin kuma ya nuna ƙarfi a zaɓukan da suka gabata.

Yarjejeniyar da ke tsakanin Obi da Kwankwaso

A baya, mun kawo labarin cewa Rabiu Kwankwaso ya ce ya yi amanna cewa Peter Obi zai cika alkawarin yin wa’adi ɗaya na shekaru huɗu idan aka zaɓe shi a 2027 da ke kara kusantawa.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Lokacin da Tinubu ya mika wa Shettima fom din zama abokin takararsa a 2027

Ya bayyana cewa shi da Obi sun sanya hannu kan yarjejeniyar da ta tanadi komawar mulki Arewa bayan wa’adin shekaru huɗu, kuma ya yi imanin Peter Obi ba zai karya wannan alkawari ba.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce yarjejeniyar ta shafi jam’iyyar da kuma wata yarjejeniya ta daban tsakaninsa da Obi yayin da suka amince su hada hannu domin tunakarar jam'iyyar APC a 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng