Akwai Ci Gaba: Bankin Duniya Ya Fitar da Rahoto kan Tattalin Arzikin Najeriya
- Bankin Duniya ya ƙara hasashen ci gaban tattalin arzikin Najeriya a 2026 zuwa kashi 4.3, sakamakon daidaituwar tattalin arziki
- Bankin ya ce tattalin arzikin Najeriya zai bunƙasa da kashi 4.4 a kowace shekara tsakanin 2027 da 2028
- Bankin Duniya ya yi gargadin cewa tsadar rayuwa, rashin tsaro da matsin lambar zaɓe na iya rage saurin aiwatar da gyare-gyare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Bankin Duniya ya ƙara hasashen ci gaban tattalin arzikin Najeriya a shekarar 2026 zuwa kashi 4.3, saboda inganta tattalin arziki da ƙarin amincewar masu zuba jari.
Sai dai bankin ya yi gargadin cewa ƙarin kashe kuɗin gwamnati gabanin zaɓen 2027 na iya rage tasirin gyare-gyaren tattalin arzikin da ake aiwatarwa.

Source: Getty Images
Hasashen na cikin rahoton Bankin Duniya na Oktoban 2026 kan tattalin arzikin Afirka mai taken 'Gina Shirye-shiryen Amfani da Basirar Ƙwaƙwalwa ta Wucin Gadi', cewar Vanguard.
Hasashen Bankin Duniya kan tattalin arziki
Bankin ya kuma ƙara hasashen ci gaban tattalin arzikin Najeriya a shekarun 2027 da 2028 zuwa kashi 4.4 a kowace shekara.
Wannan ya kasance sama da kiyasin ci gaban tattalin arzikin Najeriya na shekarar 2025, wanda bankin ya bayyana cewa ya kai kashi 4.0.
Bankin Duniya ya ce ana sa ran ayyukan tattalin arziki a Najeriya za su ƙaru daga kashi 4.0 a 2025 zuwa kashi 4.3 a 2026.
Ya ce ana kuma sa ran ci gaban zai ƙaru zuwa kashi 4.4 a kowace shekara tsakanin 2027 da 2028, sakamakon daidaituwar tattalin arziki.
Bankin ya danganta wannan ci gaba da inganta yanayin tattalin arziki, ƙaruwa da amincewar masu zuba jari da kuma farfaɗowar zuba jari daga kamfanoni.
Duk da kyakkyawan hasashen, Bankin Duniya ya yi gargadin cewa ƙarin kashe kuɗin gwamnati gabanin babban zaɓen 2027 na iya kawo cikas.
Bankin ya ce hakan na iya raunana ƙoƙarin da ake yi na daidaita tattalin arziki da kuma rage saurin aiwatar da gyare-gyaren da aka fara.
Ya kuma bayyana cewa yanayin tattalin arzikin Najeriya na fuskantar barazana daga tsauraran yanayin kuɗin duniya da kuma tsawaitar rikicin Gabas ta Tsakiya.
Sauran barazanar sun haɗa da rashin tsaro, sauyin yanayi, matsalolin samar da mai da kuma ƙarin kashe kuɗin gwamnati gabanin zaɓen 2027.

Source: Twitter
Hasashen Bankin Duniya kan tsadar kayayyaki
Bankin Duniya ya kuma yi hasashen cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya za ta ci gaba da raguwa sakamakon tsauraran matakan kuɗi.
Bankin ya yi hasashen hauhawar farashin kayayyaki za ta ragu daga kashi 23.0 a 2025 zuwa kashi 15.7 a 2026.
Ya kuma yi hasashen cewa hauhawar farashin kayayyakin za ta ƙara raguwa zuwa kashi 12.2 nan da shekarar 2028.
Bankin ya ce raguwar hauhawar farashin kayayyaki za ta taimaka wajen ƙara ƙarfin sayen kayayyaki ga iyalai da kuma rage talauci a hankali.
Sai dai bankin ya yi gargadin cewa ƙarin ci gaban tattalin arziki shi kaɗai ba zai wadatar wajen inganta rayuwar jama’a sosai ba.
Ya ce raguwar talauci na tafiya a hankali saboda kuɗin shiga ga kowane mutum na ci gaba da kasancewa ƙasa da saurin bunƙasar tattalin arzikin.
Hakan na nufin cewa duk da ingantuwar wasu alamomin tattalin arziki, iyalai na ci gaba da fuskantar matsin lambar tsadar rayuwa.
Bankin ya kuma gargadi gwamnatoci kan yin almubazzaranci da kuɗaɗe yayin da siyasa ke ƙaruwa gabanin zaɓe.
Ya ce yawan kuɗin da ake kashewa wajen biyan basussuka na ci gaba da takaita damar gwamnati ta kashe kuɗi a wasu fannoni.
Bankin ya ce hauhawar farashin kayayyaki na iya fuskantar ƙarin barazana daga faɗuwar darajar naira, hauhawar farashin abinci da yawan kashe kuɗin gwamnati.
Tinubu zai ci bashi a Bankin Duniya
A baya, an ji cewa Gwamnatin Tarayya ta fara tattaunawa da Bankin Duniya kan neman sababbin rance uku da yawansu ya kai dala biliyan 1.5.
Sababbin rancen za su mayar da hankali kan jure sauyin yanayi, tallafa wa iyalai marasa galihu da kuma bunƙasa ilimin yara ƙanana.
Wannan na zuwa ne yayin da bashin Najeriya ya kai N166.79tn a ƙarshen watan Yunin 2026, lamarin da ke nuna ƙarin N14.39tn a shekara guda.
Asali: Legit.ng


