Babban Malamin Jami'a Ya Mutu a Otel bayan Lalata da Karuwa

Babban Malamin Jami'a Ya Mutu a Otel bayan Lalata da Karuwa

  • Dr. Matthew Uwuigbe, babban malami a Jami’ar Ambrose Alli, ya mutu a wani otel da ke Ekpoma bayan ya je wurin tare da wata karuwa
  • ’Yan sanda sun kama mutane uku da suka haɗa da matar, mai otel da manajansa, yayin da ake ci gaba da bincike kan musabbabin mutuwar
  • Jami’ar ta tabbatar da cewa Uwuigbe ma’aikacinta ne, amma ta ce lamarin ya faru ne a wajen harabar jami’ar kuma ya shafi rayuwarsa ne ta kashin kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Edo - Wani babban malami a Jami’ar Ambrose Alli da ke Ekpoma, Jihar Edo, Dr. Matthew Uwuigbe, ya faɗi ya mutu a wani ɗakin otel bayan wata ganawa da wata karuwa mai shekaru 21.

Lamarin ya faru ne ranar Lahadi, 4 ga watan Oktoban 2026 a wani otel da ke yankin Mosco, Ekpoma, cikin Ƙaramar Hukumar Esan West ta Jihar Edo.

Kara karanta wannan

Ana jimamin hatsarin sojoji, fasinja ya mutu a jirgin da ke kan hanyar zuwa Legas

Malamin jami'a ya ce ga garinku nan
Malamin jami'an da ya rasu a otel a Edo, Dr. Matthew Uwuigbe Hoto: Lina's Home
Source: Facebook

An ce malamin ya je otel tare da matar

Rahotan jaridar The Punch ya ce Uwuigbe ya shiga otel ɗin tare da matar mai suna Angela Defa Jacob, inda daga baya ya faɗi ya mutu a cikin ɗakin.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo, Eno Ikoedem, ta tabbatar da faruwar lamarin ranar Talata, 6 ga watan Oktoban 2026.

Ta ce rundunar ta samu rahoton lamarin da misalin ƙarfe 8:00 na dare ranar 5 ga Oktoba 2026.

A cewarta, an samu rahoton cewa Uwuigbe, wanda malami ne a Jami’ar Ambrose Alli, ya sauka a wani otel da ke Ekpoma tare da matar mai shekaru 21.

’Yan sanda sun kama mutane uku

Ikoedem ta ce Uwuigbe daga baya ya aika matar domin ta je ta saya masa ruwa. Ta ce lokacin da matar ta dawo, ta tarar da malamin kwance a cikin ɗakin ba tare da rai ba.

Bayan samun rahoton, ’yan sanda sun fara bincike tare da kama mutane uku da ake dangantawa da lamarin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace mahaifin dan takarar jam'iyyar ADC

Wadanda aka tsare sun haɗa da mamallakin otel ɗin, manajan otel ɗin da kuma Angela Defa Jacob.

Kakakin ’yan sandan ta ce an kai gawar malamin ɗakin ajiyar gawa na Asibitin Oriaifo Memorial, yayin da ake ci gaba da bincike.

Jami’a ta tabbatar da cewa malamin ma’aikacinta ne

Jami’ar Ambrose Alli ta tabbatar da cewa Uwuigbe ma’aikacinta ne. Jami’in Hulɗa da Jama’a na jami’ar, Otunba Mike Ade Aladenika, ya tabbatar da hakan a wata tattaunawa da PM News.

Sai dai ya jaddada cewa lamarin bai faru a cikin harabar jami’ar ba. Ya ce matar da aka ambata ba ɗalibar jami’ar ba ce, yana mai cewa abin da ya faru ya shafi rayuwar malamin ne ta kashin kansa.

Malamin jami'a ya mutu a otel
Taswirar jihar Edo, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Soja ya yi lalata da matar abokin aikinsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojan ruwa ta Najeriya (NN) ta kori wani jami’i mai mukamin Laftanal daga aiki tare da yanke masa hukuncin shekaru uku a gidan yari.

An yanke wa sojan wannan hukuncin ne bayan da aka same shi da laifin kulla alaƙar soyayya da matar wani soja, har ta kai su ga lalata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng