Masoyan Tinubu sun mayar wa Kwankwaso martani kan tikitin Musulmi Musulmi
- Magoya bayan Bola Ahmed Tinubu sun yi mamakin kalaman Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso game da tikitin takarar shugaban kasa da mataimakinsa a 2027
- Kwankwaso dai ya ce Tinubu bai yi wa kansa dabara ba da ya sake dauko Kashim Shettima, musamman bayan zazzafar muhawara da ake bugawa kan batun
- Amma masoya Tinubu sun bayyana cewa illar da Kwankwaso ya ce ya hango ba wani abu ba ne, kuma tikitin ba zai samu wata matsala a zabe mai zuwa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Magoya bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu sun yi watsi da sabon sukar da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi.
Daga cikin zafafan kalaman da Kwanwkaso ya yi wa gwamnatin APC game da zaben 2027, ya ce Tinubu ya yi gagarumin kuskure da ya hau tikitin Muslim-Muslim karo na biyu.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta wallafa cewa magoya bayan shugaban kasa sun ce batun ba shi da wani tasiri a siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027, domin 'yan Najeriya sun riga sun nuna matsayinsu a lokacin zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Magoya bayan Tinubu sun dauki zafi
The Guardian ta kawo labarin cewa Darakta Janar na Tinubu Support Group (TSG), Dakta Umar Tanko Yakasai, ya ce sakamakon zaɓen 2023 ya rufe wannan muhawara ta Muslim-Muslim.
Ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja yayin wani taron yini guda kan ci gaban tattalin arziki, gine-gine da ababen more rayuwa a yankin Arewa ta Tsakiya ƙarƙashin gwamnatin Tinubu
A cewarsa, mutane da dama sun yi hasashen cewa tikitin Musulmi da Musulmi zai hana Tinubu samun nasara, amma daga ƙarshe masu kaɗa ƙuri'a sun zaɓi ɗan takarar APC.
APC: Yakasai ya yi watsi da kalaman Kwankwaso

Kara karanta wannan
Ganduje ya caccaki Kwankwaso kan shirin tattaunawa da 'yan bindiga, ya fadi illarsa
Yakasai ya ce yankin Arewa ta Tsakiya, duk da kasancewar akwai Kiristoci da dama a cikinsa, ya amfana da muƙamai da kuma ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Tinubu ta aiwatar.
Ya jaddada cewa ya kamata a rika tantance gwamnati ne bisa irin ayyukan da ta yi wa al'umma, ba bisa addinin shugabanninta ba.

Source: Twitter
Haka kuma ya buƙaci 'yan siyasa su mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi ci gaban ƙasa maimakon sake tayar da muhawara kan tsarin tikitin shugaban ƙasa na APC.
Sai dai Kwankwaso ya nace cewa batun tikitin Musulmi da Musulmi zai kasance mai muhimmanci a zaɓen 2027. Ya ce abin mamaki ne yadda Shugaba Tinubu ya ci gaba da riƙe tsarin duk da ce-ce-ku-cen da ya haifar kafin zaɓen 2023.
Kuri'a ya ke nema - APC ta soki Kwankwaso
A baya, mun ruwaito cewa jam'iyya mai mulki a Najeriya, APC ta yi watsi da sukar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wa gwamnatin Bola Tinubu kan halin rashin tsaro da tattalin arziki a kasar nan.
Jam'iyyar ta ce kalaman Kwankwaso na neman goyon bayan siyasa ne kafin zaɓen 2027, amma babu kamshin gaskiya a dukkanin sukar da ya yi na cewa gwamnati ta gaza wajen sauke nauyin da ke wuyanta.
Sai dai kakakin Kwankwasiyya ya kara karfafa kalaman Kwankwaso, inda ya dage cewa gwamnati ta gaza kare rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya kuma jama'a za su dauki matakin da ya dace a babban zaben.
Asali: Legit.ng
