Lokuta 10 da Aka Samu Jirgin Sojoji Ya Yi hadari a Najeriya daga 2021 har 2026

Lokuta 10 da Aka Samu Jirgin Sojoji Ya Yi hadari a Najeriya daga 2021 har 2026

Abuja - An samu jiragen sojojin Najeriya sun fadi a sakamakon hadari akalla sau 10 daga 2021 zuwa shekarar bana ta 2026.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Wadannan hadura sun shafi jiragen yaki, jirage masu saukar ungulu da kananan jiragen sama zuwa jiragen koyon aikin sojoji.

Jaridar Punch da ta yi kokarin bibiyar manyan haduran da aka yi ta ce ana samun matsalar ne a kokarin koyon aiki ko yaki.

Wasu matsalolin kuma sun faru ne a sanadiyyar rangadi, aikin kai ceto ko gyaran jiragen ko kuwa hari daga 'yan ta'adda.

Jirgin sama
Wani sojan kasar Kamaru a cikin jirgin yaki Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hadarin jirgin da aka yi a Oktoban 2026

Idan ba a manta ba, na karshen nan shi ne jirgin sojojin sama na ATR-42 mai lamba NAF 931 da ya fadi a Igbokoda, jihar Ondo.

Jirgin ya taho kamar yadda ya saba daga Benin zuwa Legas sai aka samu matsala da shi da safe, ba a kara jin duriyar shi ba.

Kara karanta wannan

Lauya ya shiga neman beli da aka maka shugabannin jam’iyyar ADC a kotu

Rahoton ya ce babu lokacin da haduran suka fi muni kamar a shekarar 2021 da aka rasa jiragen sojojin Najeriya da-dama.

Sauran haduran jirgin da aka yi a shekaru 6

1. Hadarin Beechcraft King Air 350i

A shekarar ta 2021, jirgin NAF Beechcraft King Air 350i ya fadi jim kadan bayan ya taso daga Abuja yana kan hanyar Minna.

An rahoto cewa duka mutane bakwai da jirgin ya dauko sun mutu nan take a Fubrairun 2021.

2. Alpha Jet a Borno

Cikin karshen Maris a shekarar ta 2021 ne dai kuma wani jirgin yaki na Alpha Jet ya bace a lokacin da yake aiki a jihar Borno.

Bayan watanni 11, Daily Trust ta rahoto cewa an ga bangaren jirgin saman a jejin Sambisa, har yau babu labarin matukansa biyu.

3. Jirgin Hafsun sojoji da manyan jami’ai

Mafi munin hadarin shi ne wanda jirgin NAF King Air 350 ya yi a kusa da filin jirgin sama da yake garin Kaduna a Mayun 2021.

Duka mutane 11 da suke cikin jirgin, har da shugaban sojojin kasa, Laftanan Janar Ibrahim Attahiru sun mutu nan take hadarin.

Kara karanta wannan

An saki sunayen sojoji da mutum 25 da suka rasu a hadarin jirgin soji a Ondo

4. Harbe jirgin NAF Alpha Jet

Sojojin saman Najeriya sun rasa wani jirgin yaki kirar NAF Alpha Jet a Yulin 2021 lokacin da aka harbo shi a jihar Zamfara.

BBC ta rahoto yadda matukin jirgin saman, Flight Lieutenant Abayomi Dairo ya yi rai bayan ya fice kafin ya fadi ya tarwatse.

5. Super Mushshak

Abin bai tsaya a shekarar ba, ko a 2022 akwai jirgin Super Mushshak da ya fadi a Kaduna, wannan ya sa aka rasa matuka biyu.

TVC ta rahoto hafsun sojoji na lokacin ya bada umarnin a binciki abin da ya jawo hadarin.

6. Hadarin NAF FT-7NI a Benuwai

Wani jirgin koyon aiki da sojoji suka rasa shi ne NAF FT-7NI wanda ya fado a garin Makurdi, jihar Benuwai a watan Yulin 2023.

Jaridar The Nation ta kawo labarin a lokacin, an kuma ji cewa matukansa biyu sun tsira.

7. NAF Mi-171

Bayan wata daya da abin da ya faru a Makurdi sai jirgin NAF Mi-171 mai saukar ungulu ya kife a wani kauye a Shiroro.

Kara karanta wannan

Gwamna ya shiga aikin da ba nasa ba, ya fadi abubuwa 3 da suka jawo hatsarin jirgin sojoji

Bayanai sun ce jirgin ya taso daga Zungeru ne zai nufi Kaduna. A sanadiyyar hadarin aka rasa mutane 11 kuma an samu rauni.

8. NAF Mi-35P

Jirgin NAF Mi-35P mai saukar ungulu ya gamu da matsala a karshen 2023, a sanadiyyar haka ya fadi kasa a sansanin sojoji.

Rahoton da Arise ta fitar ya ce duka mutanen da ke cikin jirgin a Fatakwal sun kubuta, sai dai sun samu kananan rauni a jikinsu.

9. Alpha jet a Neja

A shekarar bara wato 2025, wani jirgin Alpha Jet ya gamu da matsala don haka ya yi saukar gaggawa a Kainji, jihar Neja.

An yi dace, direbobinsa sun iya fita daga cikin jirgin yakin ba tare da an samu asarar rai ba.

10. NAF CH-4B

Na karshe kafin abin da ya faru a Ondo shi ne jirgin NAF CH-4B da aka rasa lokacin yana sintiri a wasu kauyukan jihar Neja.

Babu wanda aka samu ya mutu a sanadiyyar hadarin wanda shi ne na farko a shekarar bana.

Jirgin yaki
Jiragen yakin Najeriya da Nijar lokacin ana tsakiyar rikicin Boko Haram Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Makokin sojojin da suka mutu a jirgin sama

Kara karanta wannan

Iyalan sojoji da dukkan dakarun da ke cikin jirgin sojin da ya yi hadari sun mutu

An ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana kwanaki uku na zaman makoki a fadin Najeriya domin karrama dakarun da aka rasa a jirgi.

Umarnin ya hada da sauke tutocin Najeriya zuwa kasa a fadin kasar yayin da ake gudanar da zaman makokin sojojin saman da suka mutu.

Hadarin jirgin saman na ATR-42 ya faru ne a yankin Igbokoda da ke jihar Ondo yayin da yake hanyarsa ta tashi daga Edo zuwa Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng