Yadda Matashi Ya Rasa Ransa bayan Caka Masa Wuka a Jigawa kan N500 Kacal
- Rundunar ’yan sandan Jigawa ta kama matashi mai shekaru 20 bisa zargin kashe wani bayan takaddama kan bashin N500
- An ce wanda ake zargin ya daba wa matashin wuƙa bayan ya kasa biyan N500 da ya rage daga kuɗin wayar hannu da ya saya
- A wani lamari, ’yan sanda sun kama Abbas Ibrahim bisa zargin ƙona ɗakin ɗan uwansa, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Dutse, Jigawa - Rundunar ’yan sanda a jihar Jigawa ta kama wani matashi da ake zargin ya yi ajalin Mohammed Abba kan basin N500.
Matashin da aka cafke mai shekaru 20, Lawisi Safiyanu ya caka wa Muhammad Abba wuƙa har ya mutu saboda bashin da ke tsakaninsu.

Source: Facebook
Mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Facebook a ranar 6 ga Oktoba.
Yadda matashi ya yi kisa a Jigawa
Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 12:30 na dare ranar 1 ga Oktoba a ƙauyen Chamo, ƙaramar hukumar Dutse.
’Yan sanda sun ce binciken farko ya nuna cewa Abba ya sayi wayar hannu daga hannun wanda ake zargin kan N1,500.
An ce Abba ya biya N1,000, amma ya rage yana bin Safiyanu bashin N500, wanda ya haifar da rashin jituwa tsakaninsu.
A yayin takaddamar, wanda ake zargin ya yi amfani da wuƙa wajen caka wa Abba, lamarin da ya jikkata shi sosai.
An garzaya da Abba zuwa Asibitin Koyarwa na Rashid Shekoni da ke Dutse domin samun magani, amma ya rasu yayin jinya.
Rundunar ta ce an kama Safiyanu tare da kwato wuƙar da ake zargin ya yi amfani da ita wajen aikata laifin.
’Yan sanda sun kuma ce an kammala binciken lamarin, sannan an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar shari’a.

Kara karanta wannan
A karshe, kotu ta ba da belin matasa da ke tsare kan sanya rigar 'Tinubu Must Go'

Source: Original
An kama wani da ya kona dan uwansa
A wani lamari na daban, rundunar ta ce ta kama Abbas Ibrahim mai shekaru 27 bisa zargin shiga ɗakin babban ɗan uwansa, Basiru Shuaibu.
An ce Abbas ya zuba fetur a cikin ɗakin Basiru mai shekaru 25, sannan ya cinna masa wuta, lamarin da ya jikkata shi da matarsa.
’Yan sandan sun ce Basiru da matarsa sun samu munanan raunuka sakamakon gobarar da ta tashi a ɗakin.
’Yan uwansu sun kai su wajen wani mai maganin gargajiya domin neman magani, amma Basiru ya rasu daga baya sakamakon raunukan da ya samu.
Rundunar ta ce jami’anta sun fara bincike tare da kama Abbas a garin Sara da ke ƙaramar hukumar Gwaram.
Kwamishinan ’yan sandan Jigawa, CP Tijjani Murtala, ya bukaci mazauna jihar su kwantar da hankalinsu tare da guje wa ɗaukar doka a hannunsu.
Mata sun mutu a hatsarin jirgin ruwa

Kara karanta wannan
Ministan Tinubu bai ji daɗin abin da ya faru da mutane 32 a jirgin saman sojojin Najeriya ba
A wani labarin, an ji cewa matafiya mata huɗu sun mutu bayan wani jirgin ruwa da ke ɗauke da mutane takwas ya kife a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.
Rahotanni sun nuna cewa an samu nasarar ceto sauran mutane huɗu a raye bayan hatsarin da ya faru a tafkin Dudduru.
Hukumar NSCDC ta yi kira ga masu amfani da hanyoyin ruwa su yi taka-tsantsan a lokacin iska mai ƙarfi.
Asali: Legit.ng
