Buba Galadima Ya Yi wa APC Tonon Asiri, Ya Ce Ta Kawo Sabuwar Dabara a 2027
- Jigon jam’iyyar NDC, Buba Galadima, ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da amfani da duk wata hanya wajen dakile ’yan adawa gabanin zaben 2027
- Galadima ya kuma yi zargin cewa ana bai wa wasu ’yan siyasa makudan kudi domin su janye daga takarar zaben 2027, tare da barin ’yan takarar APC ba hamayya
- Ya bayyana hakan ne a wata hira a ranar Talata, kwanaki 100 kafin babban zaben 2027, inda ya ce ’yan adawa na fuskantar matsaloli da dama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Jigon jam’iyyar NDC, Buba Galadima, ya zargi gwamnatin da jam’iyyar APC ke jagoranta da sanya cikas a kan hanyar ’yan adawa gabanin babban zaben 2027.
Dan siyasar ya ce duk da cewa saura kwana 100 a gudanar da zaben, har yanzu yanayin siyasar zaben bai yi kamari ba saboda, a cewarsa, ’yan siyasar adawa suna fuskantar matsaloli.

Kara karanta wannan
Duk da matsalar da ake ciki da Wike, APC ta bayyana shirin da ta yi saboda Tinubu

Source: Facebook
Buba Galadima ya bayyana haka ne yayin wata hira ta musamman da tashar Arise News yayin da ake shirin zaben Najeriya na 2027.
Buba Galadima ya zargi APC
A cewar Buba Galadima, APC na amfani da hanyoyi daban-daban wajen raunana jam’iyyun adawa da kuma hana ’yan takararsu gudanar da kamfe cikin ’yanci a sassan Najeriya.
Ya ce wasu ’yan siyasa a wajen APC ba su da tabbacin ko za su iya tsayawa takara a zaben, yana mai cewa akwai cikas da dama da aka sanya wa tsarin dimokuraɗiyya.
“Kwana 100 suka rage kacal kafin babban zaben, amma har yanzu zafin zaben bai kama kasar ba. Kowane dan siyasa, ban da wadanda ke kan mulki, yana dar-dar,”
In ji shi.
Ya kara da cewa APC da gwamnatin da ke karkashinta ba sa son jam’iyyun adawa su samu damar yin kamfe a kowane bangare na kasar.
Zargin ba 'yan adawa kudi
Buba Galadima ya kuma yi zargin cewa ana bai wa wasu ’yan takarar majalisun dokoki makudan kudi domin su janye daga takarar, tare da bai wa ’yan takarar APC damar tsayawa ba tare da hamayya ba.
Ya ce wasu ’yan majalisar dokokin jihohi da suka amince su janye wa ’yan takarar APC ana zargin ana ba su N50m, yayin da ya ce ana yi wa ’yan takarar Majalisar Wakilai alkawarin N200m da mota.
Buba Galadima ya yi zargin cewa wata mata daga Zamfara ce ke rarraba kudin a wani otal da ke Asokoro a Abuja, yana mai cewa wasu daga cikin ’yan takarar sun rubuta takardun murabus tare da karbar kudin.
An gayyaci 'yan NDC
Buba Galadima ya kuma yi ikirarin cewa wasu ’yan siyasar NDC sun halarci tarukan da ake zargin an yi musu tayin kudi domin su janye daga takarar 2027.
Ya ce wanda ke neman kujerar Sanata ana zargin ana masa tayin Naira miliyan 500 da mota, yayin da wanda ke neman kujerar gwamna kuma zai janye ake zargin ana masa tayin Naira biliyan 2 da mota.

Source: Facebook
Ga bayanin da Buba Galadima ya yi a kasa:

Kara karanta wannan
Doguwa ya fito da abubuwa 2 da za su ceci APC daga shan kaye a jihar Kano a zaben 2027
Ana kamfen din ADC a Gombe
A wani labarin, mun ruwaito cewa dan takarar gwamnan Gombe na jam’iyyar ADC, Bala Bello Tinka, ya yi alkawarin mayar da aikin achaba na tsawon sa’o’i 24 idan aka zabe shi a 2027.
Tinka ya ce zai sake duba dokar da gwamnatin Gombe ta sanya wadda ta takaita zirga-zirgar babura masu zaman kansu daga karfe 7:00 na dare zuwa 6:00 na safe.
Dan takarar ya kuma yi alkawarin samar da ilimi kyauta daga matakin firamare har zuwa jami’a, tare da daukar matakan yaki da satar wayoyi da jakunkuna idan ya samu nasarar lashe zaben.
Asali: Legit.ng
