An Tura Dan Gwagwarmaya Gidan Gyaran Hali kan Sukar Gwamna
- An mayar da Abdulkarim Allanana, wanda aka fi sani da Oscar Keana, daga gidan gyaran hali na Lafia zuwa wani gidan yari mai matsakaicin tsaro
- SSS ta gurfanar da shugaban na IPNAS bisa zargin yaɗa bayanan ƙarya game da Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule.l
- Kotun Tarayya ta Lafia ta ɗage sauraron bukatar belinsa zuwa 26 ga Nuwamba, yayin da Allanana ke ci gaba da kasancewa a tsare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Nasarawa - An mayar da wani mai fafutukar kafafen yaɗa labarai, Abdulkarim Allanana, wanda aka fi sani da Oscar Keana, daga Gidan Gyaran Hali na Lafia zuwa Gidan Gyaran Hali mai Matsakaicin Tsaro da ke Jihar Nasarawa.
Allanana, wanda shi ne shugaban ƙungiyar Indigenous People of Nasarawa State (IPNAS), an mayar da shi ne ranar Talata bisa umarnin Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya.

Source: Facebook
SSS ta gurfanar da Allanana
Wata majiya da ke da masaniya kan lamarin ta sanar da Premium Times cewa an mayar da Allanana ne kwanaki kaɗan bayan Kotun Tarayya da ke Lafia ta bayar da umarnin ci gaba da tsare shi.
Hakan ya biyo bayan gurfanar da shi da Hukumar SSS ta yi a gaban kotu bisa zargin yaɗa bayanan ƙarya da suka shafi Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule.
Allanana na fuskantar tuhume-tuhume guda biyu da suka shafi zargin yaɗa bayanan ƙarya. Kotun ta ɗage shari’ar zuwa 26 ga Nuwamba domin sauraron bukatar belinsa.
Gwamna Sule ya kai ƙorafi
Lamarin ya samo asali ne daga wani ƙorafi da aka ce Gwamna Abdullahi Sule ya gabatar ta hannun wani kamfanin lauyoyi mai suna Legal Logic da ke Abuja.
An ce an rubuta ƙorafin ne a ranar 20 ga Satumba, inda gwamnan ya zargi Allanana da yin wasu kalamai da ya bayyana a matsayin “manyan zarge-zarge, ganganci da kuma marasa hujja” a wasu shirye-shiryen da ya gabatar a kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan
Ba ɓoye ɓoye, Gwamna Sule ya faɗi jihohi 3 da APC ke fuskantar babban ƙalubale gabanin 2027
Ɗaya daga cikin zarge-zargen da aka ambata a cikin ƙorafin shi ne cewa Allanana ya yi iƙirarin Gwamna Sule ya umarci magoya bayansa su goyi bayan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo, a zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na APC na 2022.
An kuma ce ƙorafin ya ambaci zargin da Allanana ya yi na danganta Gwamna Sule da rushewar kamfanin African Petroleum (AP) Group of Companies.
An kuma zarge shi da wasu kalamai kan Tinubu
A cewar ƙorafin, an kuma zargi Allanana da yin wasu ikirari game da matsayin Gwamna Sule wajen mara wa Shugaba Bola Tinubu baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
An ce gwamnan ya ɗauki zarge-zargen a matsayin ƙarya da kuma masu ɓata masa suna, yana mai cewa za su iya jefa shi da ofishinsa cikin ƙiyayya, izgili, raini da tozarta.
Ƙorafin ya kuma yi magana kan wasu bidiyoyi da aka wallafa a intanet, inda ake zargin Allanana da yin kalamai marasa daɗi game da wasu ’yan gidan gwamnan.
Daga cikin batutuwan da aka ambata har da kalaman da suka shafi wani gwajin DNA da aka ce ya shafi ’yar gwamnan. An ruwaito cewa Allanana ya janye wasu daga cikin kalaman da ya yi daga baya.
Ana nuna damuwa kan ’yancin faɗar albarkacin baki
Duk da hakan, SSS ta ci gaba da shari’ar tare da gurfanar da Allanana a gaban Kotun Tarayya.
Ci gaba da tsare shi da kuma mayar da shi wani gidan gyaran hali ya jawo damuwa daga wasu mutane, waɗanda ke cewa lamarin na iya haifar da tambayoyi kan ’yancin faɗar albarkacin baki da kuma kare ’yancin jama’a na gudanar da harkokinsu.
Wata majiya da ke da masaniya kan lamarin ta yi kira ga ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama da sauran masu fafutukar ’yancin jama’a da su sanya ido kan shari’ar.

Source: Original
An bayar da belin masu adawa da Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata kotun majistare da ke Maiduguri, Jihar Borno, ta bayar da belin mutane biyar da aka kama kan yin adawa da Bola Tinubu.
An tsare matasan ne bisa zargin sanya rigar siyasa mai ɗauke da rubutun 'Tinubu Must Go' a jihar Borno.
Asali: Legit.ng

